✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda malaman jami’a suka yi sabani da ASUU

Wasu malaman jami’a a Najeriya sun bayyana rashin gamsuwa da matakin da kungiyarsu ta dauka na yin watsi da bukatar su ba da lambobin tantance…

Wasu malaman jami’a a Najeriya sun bayyana rashin gamsuwa da matakin da kungiyarsu ta dauka na yin watsi da bukatar su ba da lambobin tantance sahihancin asusun banki (BVN) don a biya su albashin da suke bin gwamnatin tarayya.

Daya daga cikin malaman, Dokta Aliyu Kankara. ya ce shi bai ga dalilin kungiyar na yi watsi da bukatar ta gwamnati ba.

Kungiyar Malaman Jami’ar (ASUU) ta yi watsi da bukatar bayar da BVN din ne ta bakin shugabanta, Farfesa Biodun Ogunyemi, wanda ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya cewa abin bai yi wa malaman dadi ba.

Sai dai Dokta Kankara, wanda shi ne shugaban Sashen Ilimin Binciken Kasa na Jami’ar Tarayya ta Dutsanma a jihar Katsina, ya ce, “Ba na goyon bayan abin da shugaban ASUU ya fada.

“Mu mun fi sauran ma’aikatan Najeriya ne.? Da lambar BVN ake biyan albashi, ba yadda za a yi a ba ka albashi sai da lambar BVN,  ban ga laifi ba idan an ce a ba da lambar BVN saboda abu ne wanda ya shafi banki.”

Dakta Kankara ya kara da cewa ”A yanzu a ce mutum mai iyali ya yi wata uku ba albashi ga azumi ya zo kuma an ce za a biya wannan kudin, to ko me aka ce a bayar me zai hana a bayar?

“Ba wai cewa aka yi dole za a saka mu cikin sabon tsari na bai-daya na biyan albashi dauke da bayanan ma’aikaci ta na’ura (IPPIS) ba, mu masu ilimi ne. a cikin mu akwai wadanda suka kai matsayin farfesa, akwai daktoci da sauran su.

“Kawai don ka ba da lambar BVN sai a saka ka cikin tsarin IPPIS ko da ba ka so ba? Don haka ba na goyon bayan wannan matakin da shugabanmu ya dauka”, inji malamin.

A ranar Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umarni a biya malaman da ke karantarwa a jami’o’in gwamnatin tarayya albashinsu na watannin Fabrairu da Maris da aka rike saboda ba su yi rajista da sabon tsarin na IPPIS ba.

A ranar 23 ga watan Maris ne dai kungiyar ASUU ta tsunduma yajin aikin gama gari, sakamakon gazawar gwamnati wajen biyan bukatunsu da suka tsara na FGN-ASUU 2019 da kuma kin amincewa su shiga tsarin IPPIS.