✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda masu garkuwa da mutane ke kai wa ’yan Arewa mazauna Ogun farmaki

Al’ummar garin Sabo Abeokuta, sun sake samun kansu cikin alhinin rashin daya daga cikin dattawansu inda masu garkuwa da mutane suka sace kuma suka kashe…

Al’ummar garin Sabo Abeokuta, sun sake samun kansu cikin alhinin rashin daya daga cikin dattawansu inda masu garkuwa da mutane suka sace kuma suka kashe shi bayan sun karbi kudin fansa, wata guda da masu garkuwar suka kashe yaro dan shekara bakwai, bayan sun karbi kudin fansa daga mahaifinsa wanda dan uwa ne na kud-da-kud gare su.

A makon jiya ne masu garkuwar suka sace mutum uku mazauna garin Sabo Abeokuta, inda bayan an biya kudin fansa suka saki mutum biyu yayin da suka kashe na ukun mai suna Alhaji Umaru Danmaruda, daya daga cikin shugabanin Fulanin yankin da ya shafe sama da shekara 40 kuma yake  sahun gaba na wadanda ake ganin za su jagoranci Fulanin Jihar Ogun a karkashin Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyyati Allah. Bayanan da Aminiya ta tattaro sun tabbatar da cewa, an kammala shirye-shiryen ba shi jan ragamar kungiyar a jihar nan bada jimawa ba, sai masu garkuwar suka sace shi.

Aminiya ta zanta da wadansu daga cikin shugabannin al’ummar Arewa mazauna Jihar Ogun, wadanda suka bayyana rashin jin dadinsu da lamarin inda suka ce a baya ba kasafai ake ganin irin haka ba.

Alhaji Kabir Labar Sarkin Fulanin Randa, kuma Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya na jihohin Yamma ya shaida wa Aminiya cewa, garkuwar da aka yi da Alhaji Umaru Danmaruda abin takaici ne, kasancewarsa jigo mai fada-a-ji kuma mutum wanda ba ya gajiyawa domin ci gaban al’ummar Fulanin yankin, “Hakika mun tafka babbar asara ta rashin jajirtaccen mutum mai himma da za a dade ba a cike gurbinsa ba,” inji shi.

Ya ce, ’yan bindigar sun yi sace Alhaji Umar Danmaruda ne suka yi awon gaba da shi bayan sun karbi kudin fansa suka kuma hallaka shi, ya ce abin bakin ciki ne kuma suna fata Allah Ya yi masa rahama Ya bi masa hakkinsa. “Saboda  duk wanda ya hallaka rai ya san makomarsa, ina yi wa al’ummarmu gaba daya ta’aziyya da iyalansa da danginsa, Allah Ya ba mu wanda zai maye gurbinsa domin mutum ne mai kwazo mai kokari, ya kawo wa Fulani makiyaya ci gaba a wannan yanki, kuma daya ne daga cikin ’yan takarar Shugaban  Kungiyar Miyyati Allah wanda ake yi wa zaton nasara kuma ake sa ran zai yi abin kirki in an ba shi. Muna fata can ya fi masa nan, mutum ne da ya dace a wannan yanki domin ya fi shekara 40 a nan. Ya zo ne daga Jihar Kebbi daga yankin Maruda, babu wani taro da za a yi ba ka gan shi a wajen ba, wannan mutum da muka rasa babban jigo ne, mutumin kwarai nagari na kowa,” inji shi.

Sarkin Fulanin, ya ce matsalar ’yan bindiga ta zamo gama-gari a Najeriya sai dai a yi ta addu’a kuma a hada kai da jami’an tsaro domin tunkarar lamarin don a samu saukin wannan ta’addaci.  “Wannan ba shi ne na farko ko na biyu ba, an yi da dama wasu ba a ji su ba ne ko ba a sansu ba, ko ba su da karfi. Don haka wannan matsala ce da muke neman taimakon Allah a kanta,” inji shi.

Sarkin Fulanin Sabo Abeokuta Alhaji Bashir Musa, ya shaida wa Aminiya cewa, abin da za su ce shi ne Allah Ya jikan Alhaji Umaru Damaruda. “Domin lokaci ne ya yi, mu ma in namu lokacin ya yi Ya sa mu cika da imani, sun dauke shi ne a can mashayar shanu ta Iguwa inda ake zuwa yin rani a nan jihar Ogun.  A ranar Talatar makon jiya, bayani ya zo mana, inda aka ce ya ce lallai a nemi kudi a kai musu domin a ceci ransa kuma haka aka yi. Bayan an kai musu kudin da goshin Magariba aka ce suka kashe shi a ranar Alhamis. Mutumin kirki ne yaron mahaifinmu ne, mu ba mu taba samunsa da wata matsala ba, sun yi masa kisan gilla, don haka muna yi wa iyalansa ta’aziyya,” inji shi.

Ya ce, a baya sun rabu da jin irin wannan matsala amma yanzu ta yi kamari, “Abin da ya kamata shi ne hukuma da mu shugbanin da al’ummar gari a kula da tsaro a sa ido kowa kuma ya san wanda yake mu’amala da shi. Idan an ga abu ba daidai ba a sanar da shugabannin a kuma sanar da hukuma, domin ba komai idon muke gani ba,” Inji shi.

A  bangaren sarkin Hausawan Abeokuta Alhaji Ibrahim Hassan, cewa ya yi hakika abubuwa da dama suna faruwa, “Wannan jarrabawa ce da Allah ya kawo mana mu mazauna garin Sabo Abeokuta. A baya irin wadannan abubuwa ba sa faruwa, sai ga shi yanzu mun samu kanmu a ciki, sai mu koma ga Allah da tuba da addu’o’i, bai kamata mu manta da Allah ba.Wannan abin ana danganta shi da kabilun Arewa musamman Fulani, amma idan muka duba za mu ga ba Fulani kadai suke wannan abu ba, wani lokacin ma za ka ga ba Fulani ba ne wasu kabilu ne na daban suke yin shigar burtu kai ka dauka Fulani ne. Akwai kabilu da dama da suke wannan ta’asa amma Fulani ne suka yi kaurin suna, kuma hakika muna fada wa shugabanninsu abin da ya kamata su yi. Su rika bin rugage suna fadakar da jama’arsu, suna fada masu abin da ya kamata su yi, a fadakar da mata, a sanya yara a makarantu su yi ilimi, domin yaran da suka yi ilimi ba za ka same su a wannan mummunan abu ba. Jahilci shi ke kawo wannan, yara su shiga shaye-shaye, daga nan su fara neman kudi ta kowane hali, don haka iyaye su ba ’ya’yansu ilimin addini da na zamani mu kuma mu koma ga Allah mu ci gaba da addu’,” inji shi.

Ya ce, ma’aikata na kokari bakin gwargwado don haka gwamnati ta rika dafa musu da kayan aiki domin su samu yin aiki yadda ya kamata.

Aminiya ta zanta da Malam Mu’azu, wanda aka sako shi bayan ya shafe kwana biyar a hannun masu garkuwa da mutanen, inda ya ce, an yi garkuwa da shi a hanyarsa da ya saba bi domin neman abincinsa, “Ni kasuwancin sayar da kifi nake yi, ina zuwa daji in saro kifi in kai cikin gari in sayar. Hanyar tamu daji ne sosai a baya da mota nake zuwa, amma yanzu babu harka sosai ina daukar dan acaba ne. A ranar da lamarin ya faru mun yi nisa sosai a dajin sai aka tare mana gaba mutum hudu, a gefe ma haka kuma baya, mutum 17 ne suka sanya mu a tsakiya kowanensu da bindiga AK47, ina ganin haka na cire ’yan kudin aljihuna na mika musu. Suka karba suka kuma daka min tsawa in sauko daga kan babur din, haka na sauka na bi su,” inji shi.

Ya ce,  a baya an sha tare shi irin haka amma da zarar ya bada abin da ke wurinsa sai a sake shi amma a wannan karo sai aka tafi da shi. “Allah ne Ya tserar da ni, domin an yi ta shirya addu’a a haka muka yi ta zama da su daga wannan waje a sauya mu a koma waccan kullum cikin tafiya muke ana sauya mana wajen zama, har Allah Ya sa suka shirya da ’yan uwana aka ba su abin da ya sawwaka suka sallamo ni. Ina godiya ga Allah da kuma jama’ar da suka yi ta nuna damuwarsu, wannan abu daga Allah ne kuma Shi ne zai yi mana maganinsa,” inji shi.

Ya ce, yana tsare a hannunsu ya ji labarin cewa wadanda suka dauki Alhaji Umar Danmaruda, sun kashe shi inda ya yi fata Allah Ya jikansa Ya yi masa rahama.

Tuni dai aka yi jana’izar Alhaji Umaru Danmaruda a garin Maruda da ke Jihar Kebbi, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, bayan da aka tafi da gawarsa daga Jihar Ogun zuwa Kebbi kamar yadda mahaifiyarsa ta bukata.

Aminiya ta zanta da Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi, wanda ya  ce rundunar ba ta da masaniyar cewa masu garkuwa da mutane sun kashe marigayin, kuma ba a sanar musu da labarin garkuwa da karin mutum biyu da aka ce an yi garkuwa da su ba. Ya ce a wannan mako sun yi ba-ta-kashi da masu garkuwa da mutane a dazukan Shagamu, “A wannan karo da masu garkuwar suka yi garkuwa da wani mutum da matarsa da jami’anmu suka yi ta ba su wuta suka kewaye dajin sai suka saki matar da mijinta. Yanzu haka muna kokarin kama wadanda ake zargi, mako biyu da suka gabata mun kama wadansu mutum hudu da ake zargi da garkuwa da Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Remo ta Arewa , Mista  Soniyi Taiwo, inda jami’anmu suka kubutar da shi daga masu garkuwar wadanda suka hada da Muhammad Abdullah, dan shekara 25 da Ibrahim Dikko mai shekara 20 sai Gambo Abdullah mai shekara 25 da Mohammed Sulaiman mai shekara 23 kuma zuwa yanzu ana bincike a kansu,” inji shi.

Ya ce, matsalar garkuwa da mutane aba ce da ta zamo ruwan dare a kasar nan kuma jami’an tsaro na aikinsu yadda ya kamata. “Ban yarda cewa wannan matsala na kara yawaita a Jihar Ogun ba, kuma shi al’amari irin wannan ba a danganta shi da wata kabila, ba za ka ce Fulani ne ko Hausawa ko Yarbawa ba ko wata kabilar, shi mai laifi mai laifi ne ko daga ina yake, ba ma kallon kabilar mai laifi, a’a laifin ne abIn lura, kuma ba za mu saurara masu ba ko su wane ne ko daga ina suke,” inji shi.

Ya ce yana da tabbacin mutanen da suka sace Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar zaunannun yankin ne ba baki ba, lura da irin surkukin daji da hanyoyin da suka bi da shi.