Da Dumi Dumi

Yadda masu garkuwa da mutane suka rike ni bayan na kai musu kudin fansa – Yusuf Rigasa

Yusuf Is’hak Rigasa matashi ne da masu garkuwa da mutane suka rikeshi bayan ya kai musu kudin fansar abokin aikinsa da suka yi garkuwa da shi. A tattaunawa da Aminiya ya ce sai da suka karbi karin kudin fansa kafin suka sallame su:

Yaushe ka kai musu kudin fansa domin karbo abokinka?

Ranar Alhamis din makon jiya ne na kai musu a wani wuri da suka yi min kwatance a cikin daji da ke gaban wani wuri da ake kira Doguwa a gaban Rigasa, bayan an sasanta da su a kan Naira dubu 350 aka ba nI in kai musu. Bayan na ba su kudin sai suka rike ni na kuma sha duka a hannunsu.

Laifin me ka yi musu?

Wai kudin da aka ba su bai isa ba. Ni kuma na san cewa yadda aka yi ke nan na kai musu.

ADVERTISEMENT

Wadanne irin mutane ne?

Ni dai idona a rufe yake a lokacin, don haka sai dai kurum in ji suna yare kamar Fulani amma ban san wadanne iri ne su ba. Sun rufe min ido sannan sun daure min hannu ta baya. Ban ma san yadda aka yi suka daure ni ba. Domin lokacin da na kai masu kudin suka ce in wuce gaba, daga nan ko da na bude ido sai na gan ni a daure ido da kafa.

Daga nan sai me ya faru?

Suka fada min wai kudin da aka bayar ba su isa ba, don haka za su rike ni sai an karo kudi.

Nawa suka bukaci a kara musu?

Naira miliyan shida suka bukata da aka ci gaba da ciniki sai suka dawo Naira dubu  650, mu duka biyun.

Ko ka ga abokin naka lokacin da kake tsare?

Ai shi cewa ma ya yi ya zaci na mutu ne da ya ga irin dukan da suka yi min na fadi.

Wa ya kai musu karin kudin da suka bukata?

Wan abokin nawa ne ya yi shahada ya kai musu tunda kowa na tsoron zuwa.

Amma shi ba a yi masa komai ba?

A’a, amma dai sun rika nuna masa bindiga domin tsorata shi. Bayan sun karbi kudin ne suka sake mu wajen karfe  1:00 na ranar Litinin din nan.

Akwai nisa daga inda aka sake ku zuwa Rigasa?

Gaskiya akwai domin tun Asuba da muka rika tafiya sai da rana muka isa wajen kai musu kudin. Ni ban san dajin ba amma fa sai da aka kwashe sama da awa biyu ana tafiya a kan babur.

Suna ba ku abinci?

Eh irin wanda suke dafawa a daji kamar shinkafa, kuma muna ci suna dukkanmu.

A kwana hudu da ka yi a hannunsu idanunka a rufe suke?

Ai shi ya sa na ce maka ban san inda nake ba, domin komai za ka yi sai dai su dan kwance maka hannu ka rika dan tsalle zuwa inda za ka je biyan bukata, idan fitsari ne in ka kammala sai ka gyara ka dawo inda kake ido a rufe.

Share