✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda masu zanga-zanga suka sace kayan abinci

‘Yan daba dauke da makamai sun sa wawa a rumbun Gwamnatin Jihar Legas suka kwashe kayan abinci da aka ajiye na miliyoyin Naira. Kayan abincin…

‘Yan daba dauke da makamai sun sa wawa a rumbun Gwamnatin Jihar Legas suka kwashe kayan abinci da aka ajiye na miliyoyin Naira.

Kayan abincin da suka sace sun hada da na tallafin COVID-19 da ba a kai ga rabawa ba.

Mutanen sun far wa wajen ne bayan samun labarin an ajiye kayan tallafin COVID-19 a wurin inda suka yi ta jidar buhunan shinkafa, wake, masara da garin rogo.

Cikin dan lokaci labarin ya bazu a yankin Mile 2 inda daga nan ‘yan daba suka karaso suna dibar kayan abincin.

‘Yan daban sun kuma yi yunkurin kai wa karamin caji ofis da ke layin Old Ojo hari, amma ‘yan sanda da matasan unguwar suka kora su.