✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda matasa suka kone barawon kaza a Kalaba

Gungun matasan da suka fusata a Layin Abitu da ke Karamar Hukumar Kalaba ta Kudu  Jihar Korus Riba sun kone wani matashi mai suna Victor,…

Gungun matasan da suka fusata a Layin Abitu da ke Karamar Hukumar Kalaba ta Kudu  Jihar Korus Riba sun kone wani matashi mai suna Victor, sakamakon zarginsa da satar kaza.

Mutanen unguwa sun shaida wa Aminiya, lokacin da ta je bin diddigin labarin cewa, wanda ake zargin  ya saba yi musu ’yan dauke-dauke ana kama shi a ja masa kunne, amma duk da haka idan ya yi kamar ya bari bay an kwana biyu sai ya sake komawa halinsa.

Asirin wanda ake zargi Victor ya tonu ne, kamar yadda mai kiwon kajin da aka sata mai suna Akpan Asukuo, ya shaida wa wakilinmu “Ya saba zuwa yana yi mana sata iri-iri tun ba mu san wake yi mana sata ba, har sai da kungiyar sintiri ta wannan unguwa ta kama shi ’yan sintirin suka gargade shi kada ya sake sakewa a kama shi, ya kuma amince da gargadin da aka yi masa.

Ranar Talata da asuba, sai muka ji kajin suna kara a kejinsu kamar akwai wani abu da ba su gane ba ya shigo musu. Sai ni da matata muka leko ta tagar daki muka gan shi ya kama kaza yana kokarin boye ta a cikin buhu shi ne muka yi ihu muka nemi daukin jama’a aka kama shi,” inji shi.

Wani da ke makwabtaka da wanda aka yi wa satar kazar ya ce, ba tun yanzu ba ake ta fakon barawon a ga ko wane ne ashe ma sananne ne, abin ya ba su mamaki ganin haka ya faru sai matasan unguwa da suka harzuka suka kwace barawon kazar daga hannun jama’ar da suka kama shi, kafin a mika shi ga ’yan sintiri fusatattun matasa sun make shi da gora suka daddaure masa hannuwa da kafafuwa suka watsa masa man fetur ne suka kyasta masa ashana ya kama da wuta da ransa yana ihu yana ci da wutar, har sai da ta cinye shi ya mutu.

Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kuros Ribas, DSP Irene Ugbo game da lamarin inda ta ce “Tabbas hakan ya faru an kone shi ya mutu kamar yadda ka samu labari.”

An tambaye ta ko an kama wadansu da ake zargi su ne suka kone wanda ake zargi da satar kazar zuwa yanzu sai ta ce, “A’a amma rundunar ba ta yarda idan irin wannan ya faru, mutane su rika daukar doka a hannu suna yin yadda suka so alhali ’yan sanda ya kamata su rika sanar wa ko kira.”

Zuwa yanzu babu wanda aka samu labarin an kama shi game da batun kone wanda ake zargi da satar kaza.