✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda matasa suka rungumi kasuwancin rake a Jos

Wadansu matasa shida da shekarunsu ba su wuce 16 zuwa 23 ba suna tura baro dauke da rake a yayyanke. Suna tura baron ne a…

Wadansu matasa shida da shekarunsu ba su wuce 16 zuwa 23 ba suna tura baro dauke da rake a yayyanke. Suna tura baron ne a daidai kusurwar Katako Junction da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato.

Kusuwar Katako Junction ce yawancin hanyar da suke bi a kullum idan sun taso daga kasuwar da suke sayen rake a Farin Gada, kafin sun bazama titunan birnin Jos don sayar da rakensu.

Aminiya ta fahimci cewa matasan sun jera yankakkun raken da suke sayarwa kan farashin Naira 20 zuwa N100 a kan baronsu.

Yankakkun raken jere suke a kan wani katako bayan sun daure su da wata roba don idan suna tafiya robar ta hana raken watsewa ko zubewa.

Sun bayyana wa Aminiya cewa sukan sayar da rakensu a kan hanyoyin birnin Jos, ko wuraren kallon kwallo ko filayen kwallo ko wuraren nishadi ko kuma wuraren da ake gudanar tarurruka.

Aminiya ta sake fahimci wadannan matasan da suke kasuwancin raken sun zo ci-rani Jos ne daga kauyukan da ke jihohin Bauchi da Kaduna da Jigawa da Kano da sauransu.

A lokacin da Aminiya ta tattauna da su sun ce duk mai sha’awa zai iya fara kasuwancin sayar da rake idan yana da Naira 1,400, amma wannan sai idan ya samu baro da katakon da ake dorawa a kan baron da sauran abubuwan da ake bukata.

Yawancin masu sayar da raken manoma ne, inda suke amfani da kudin da suka samu dalilin sayar da raken wajen sayen takin zamani ko iri, sannan sukan yi amfani da kudin wajen daukar nauyin bukatunsu na yau da kullum.

Sun ce yawanci sukan zo ci-rani Jos ne bayan sun kammala girbi, inda a yanzu kasuwancin rake ke ci gaba da habaka a Jos.

A lokacin da wakilinmu ya ziyarci kasuwar rake da ke Farin Gada da ta Kwanar Shagari da suke cikin birnin Jos ya fahimci dimbin matasa ne suke gudanar da kasuwancin sayar da raken.

Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Rake a Farin Gada, Zaharaddin Sani ya ce, kasuwancin rake ya samar wa daruruwan matasa aikin yi, inda ta hanyar kasuwancin suke iya biya wa kansu bukata har su taimaka wadansu.

Ya ce, “Duk da cewa kakar rake shekara-shekara ce, amma kasuwancin rake akwai riba, domin a yanzu da ita na dogara wajen samun kudin kashewa.”

Ya ce, yakan sayar da damin rake 10 zuwa 20 a kowace rana, inda yake sayar da kowane dami a kan Naira dubu 1, 700.

Yusuf Ado, dan kimanin shekara 17 dan Karamar Hukumar Wudil da ke Jihar Kano ya ce, ya fara  sayar da rake ne kimanin shekara biyu da ta wuce.

Ya ce dalilin kasuwancin rake yake iya biya wa kansa bukata, inda a bara ya koma kauyensa da ribar Naira dubu 100.

Ya ce, “Ina son kasuwancin rake, domin akwai riba. A yau na sayi damin rake a kan Naira dubu 1, 500, amma zan iya samun ribar Naira N1, 600, kamar a bara na tafi da ribar Naira dubu 100 gida, wannan ba a sanya kudin mota da kuma na abinci a ciki ba. Tsallar ribar da na je gida da ita ne.”

Wani mai sayar da raken, Rilwanu Danyaya, dan kimanin shekara 18 dan asalin Jihar Jigawa ya ce, ya fara kasuwancin rake ne bayan ya fahimci ribar da ke ciki.

“Kasuwancin rake akwai riba, idan mutum ba ya da lalaci zai samu kudi sosai da rake, kamar ni a kowace rana nakan iya samun ribar Naira 1, 300,” inji shi.

Ya ce, “Iyayena masu karamin karfi ne, ba za su iya daukar nauyin karatuna ba, sai na fada wa kaina cewa ba zan yi bara ba, a yanzu ta dalilin kasuwancin rake nakan dauki nauyin kaina har ma na taimaki mahaifana.”

“Da zan samu wanda zai daukin nauyin karatuna da zan ci gaba, inda nake da burin son zama likita,” inji shi.

Magaji Hassan, dan kimanin shekara 22 daga Jihar Kaduna ya ce, ya fara kasuwancin rake ne shekara uku da ta gabata, kuma ya koyi kasuwancin ne a wurin yayansa da a yanzu ya bar kasuwancin rake ya koma yin tasi da mota kirar Bectra da ya saya dalilin kasuwancin rake.

“Na fara kasuwancin rake bayan na kammala makarantar sakandare, kuma yayana ne ya koya mini kasuwancin, shi ne ya ba ni kyautar baro da sauran kayayyakin da ya yi kasuwancin rake da su, inda a yanzu ga shi ina cin moriyar abin,” inji Hassan.