✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda matasan Badarawa suka kawar da mashayar Colombiya a Kaduna

Ga duk wanda ya san makarantar firamare ta Badarawa da ke gundumar Malali a garin Kaduna, shekara sama da 12 da suka gabata ya san…

Ga duk wanda ya san makarantar firamare ta Badarawa da ke gundumar Malali a garin Kaduna, shekara sama da 12 da suka gabata ya san ta zama wata cibiya ce ta tu’ammali da miyagun kwayoyi, musamman tabar aljanu da ake kira wiwi, wadda aka rika baje ta a kasa ana auna ta mudu-mudu ido na ganin ido ba kunya ba tsoron Allah.
A baya hukumomin tsaro, musamman ’yan sanda da sojoji sun rika kai wa masu harkar miyagun kwayoyin hari a wurin domin tarwatsa su, amma hakan bai hana su ci gaba da bajen kolin kayayyakinsu ba, musamman tabar wiwi da ake sayar da ita kamar yadda ake sayar da gyada ko auna masara tun daga wayewar gari har zuwa dare.
Akwai lokacin da wani babban jami’in ’yan sanda na Malali ya turo ’yan sanda suka shafe wata uku suna kwana a makarantara wajejen shekarun 2004, amma sai masu harkar saya ko sayar da wiwi da sauran miyagun kwayoyin suka rika zuwa suna lekawa su ko sun tafi, domin su dawo su ci gaba da baje kolinsu.
Haka lamarin ya ci gaba da ci wa iyayen yara da makwabtan makarantar tuwo a kwarya ta yadda masu tu’ammali da wiwi da miyagun kwayoyin suka ci gaba da rawar hantsi a harabar makarantar wani lokaci ma yara suna cikin ajujuwa.
kokarin da gwamnatin Jihar Kaduna ta yi don inganta makarantar da kokarin da wasu masu kishi suka yi don yi mata Katanga, don dakile wannan harka sun ci tura. Domin masu wannan harka sun rusa katangar da aka yi a tsakanin makarantar da makabartar Kiristoci da ke unguwar.
To, amma kimanin wata daya da ta gabata da wakilinmu ya ziyarci makarantar sai ya ga kamar an yi ruwa an dauke, babu masu wannan harka ta mu’amala da wiwi ko miyagun kwayoyi a makarantar da ake kira Colombiya.
Ko me ya kawo wannan sauyi, Salisu Isa Abba wanda aka fi sani da Malam Babangida wanda shi ne Sakataren Kwamitin Tsaro na kungiyar Masu Kishin Badarawa da Malali da ake kira ‘Badarawa Malali Concerned Forum’ ya shaida wa Aminiya cewa, “Saboda tabarbarewar zamantakewa musamman tsaro da tarbiyya a tsakanin matasa, musamman yadda yara suke shaye-shayen kayan maye, suka sanya matasan yankin suka yanke shawarar nemo wa kansu mafita. “An kafa kungiyar ce don magance abubuwan da suke faruwa na rashin tsaro da nemo hanyar da za a tabbatar da zaman lafiya a yankunan biyu, ta hanyar kawar da shaye-shayen miyagun kwayoyi da wiwi da sauransu,” inji shi.
Ya ce wajen kokarin yin haka sun hada kai da masu sayar da kayan maye da masu kemis-kemis da suke sayar da wasu magungunan tari da matasan ke amfani da su wajen sha don bugarwa.
Ya ce, “Lokacin da muka kafa kungiyar babban kalubalen da muka fuskanta shi ne yadda za a fuskanci matasan da suke tu’ammali da miyagun kwayoyi da wiwi a harabar makarantar, wadda saboda kaurin sunan da ta yi aka sanya mata sunan Colombiya, inda masu fataucin miyagun kwayoyi suke neman fin karfin hukuma.”
Ya ce daga farko wasu sun bayar da shawarar a auka wa masu tu’ammali da miyagun kwayoyin, to, amma sai suka tuna a baya idan ’yan sanda suka kai musu farmaki, jefe-jefe ke gudana a tsakaninsu da ’yan sandan, wanda hakan ya sa suka tsaya suka yi nazari sosai kan yadda za su bullo wa batun.
Malam Babangida ya ce shawarwarin da suka samu daga jama’a musamman babban jami’in ’yan sanda na Malali, DPO danbala da Hakimin Malali kuma Dokan Zazzau Alhaji Shehu Ja’e da dagatansa tara da hadin kan sarakunan matasan yankin sun taimaka wajen hada karfi don cimma nasarar kawar da wannan harka a unguwar cikin sauki.
Game da yadda suka fara tunkarar masu tu’ammali da miyagun kwayoyin a harabar makarantar, Malam Babangida ya ce, “Lokacin da muka tattauna an yanke shawarar a tuntubi dillalan wiwi da miyagun kwayoyin, wacce a baya ake kawo ta buhu-buhu ana aunawa kamar yadda mutum zai je kasuwa ya auni masara. To sai muka gayyato dillalan muka nuna musu cewa idan a da mu ’ya’ya ne a unguwar yanzu mun zama iyaye. Don haka akwai bukatar su fahimci matsalar da suka jefa matasa a ciki da kuma hadarin da suka sanya tsaro a ciki, su daina wannan harka ko kuma mu da kanmu mu dauki mataki a kansu.”
Malam Babangida ya ce, dillalan wiwi din sun yi musu alkawarin daina gudanar da wannan harka a makarantar ko unguwannin biyu gaba daya. Kuma hakan ne ya sa aka kira kananan masu sayar da wiwi da sauran miyagun kwayoyin aka shaida musu matakin da ake son dauka, don haka su daina a cikin girma da arziki ko kuma duk abin da ya faru da su kada su zargim kowa sai kawunansu.
“Da wannan ne muka samu nasarar kawar da wannan bakar sana’a a harabar makarantar firamare ta Badarawa LEA wadda saboda kaurin sunan da ta yi a baya ake yi mata kirari da Colombiya. Yanzu da makarantar ta samu lafiya muna roko ga gwamnatin Jiharb Kaduna, musamman Hukumar Ilimi Ba-daya (UBE) ta taimaka wajen gyara ajujuwan da masu harkar shan wiwi da sauran kwayoyin suka lalata tare da samar da kayan aiki a ajujuwan,” inji Sakataren.