✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda matsafa suka jawo rudu bayan tsawa ta kashe mutum uku a Shagamu

A ranar Juma’ar da ta gabata ce lokacin da ake tsakiyar ruwan sama, tsawa ta fada a kasuwar Koso da ke wajen garin Shagamu a…

A ranar Juma’ar da ta gabata ce lokacin da ake tsakiyar ruwan sama, tsawa ta fada a kasuwar Koso da ke wajen garin Shagamu a Jihar Ogun lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku, biyu daga ciki leburori Hausawa da suka fake wa ruwan sama a wani daki a cikin kasuwar, yayin da na ukun matashi ne da tsawar ta sama a nesa da kasuwar.

Wani lamari da ya so ya tayar da hankalin al’ummar yankin shi ne yadda wadansu matsafa suka so janyo hargitsi bayan faruwar lamarin inda suka hana a dauki gawarwakin domin yi musu suttura suka ce, sai sun yi tsibbace-tsibbaccensu.

Aminiya ta ziyarci kasuwar ta garin Shagamu,  domin jin yadda lamarin ya faru inda ta zanta da Sakataren Majalisar Sarakunan Jihar Ogun Alhaji Inuwa Sarki da mahaifin daya daga cikin wadanda tsawar ta kashe da kuma daya daga cikin wadanda ke cikin dakin da lamarin ya afku ta kuma bi diddigin al’adun Yarbawa game da tsawa.

Sakataren Majalisar Sarakunan Hausawan Jihar Ogun, Alhaji Inuwa Sarki ya shaida wa Aminiya cewa da misalin karfe 11 na ranar Juma’ar da ta gabata, lokacin da ake ruwan sama aka sanar masa cewa tsawa ta gifta ta kuma kashe wadansu matasa leburori da ke aiki a Kasuwar Katako ta Koso, “Sai muka nemi a je a dauko gawarwakinsu domin mu yi musu sutura kamar yadda yake a Musulunce. Ka san mu Musulmi mun yarda da kaddara ba mu yarda da wani camfi ba, ko da muka je dauko gawarwakin sai muka tarar da mutanen yankin sun sanar wa wadansu matsafa har sun isa wajen da kayayyakin surkullensu suka hana kowa taba gawarwakin lamarin da ya kusa janyo tashin tashina sai muka fada musu kada su yarda su taba mana gawarwakinmu domin muddin muka ga wani abu ya same su ba za mu yarda ba,” inji shi. Ya ce nan ya sanar da DPO din ’yan sandan yankin halin da ake ciki wanda ya ce, su yi hakuri zai shigo lamarin. “Haka muka koma muka saurare shi bayan wani lokacin ya debi ’yan sanda suka isa wajen bayan ya tattauna da shugaban kasuwar sai ya sanya jami’ansa suka shiga dakin suka debo gawarwakin suka sa su a mota suka kawo mana su muka yi musu sutura aka yi jana’izarsu bayan Sallar Isha’i a ranar Juma’ar,” inji shi.

Ya ce, matsafan sun yi ikirarin cewa su ne suka aiko tsawar ta kashe masu yin sata a kasuwar, “Amma mun san wannan zancen banza ne, camfe-camfensu ne kawai, shi Musulmi ya yarda da kaddara ko wace iri ce,” inji shi.

Daya daga cikin leburorin da ke dakin da tsawar ta fada mai suna Yusha’u wanda ya ce su shida ne a dakin lokacin da lamarin ya faru, “Ranar Juma’a da safe ana tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya a garin Shagamu, muna cikin daki a wajen da muke aiki a Kasuwar Koso, da ake sayar da itacen da ake kaiwa kasar China da ke yankin Ologede a wajan garin Shagamu, ni da Sagiru da Iliya da Jibrin da Rilwanu da Muhammadu Sani, sai muka ji tsawa mai karfin gaske. Ni dai kawai sai ji na yi an wurgo ni waje cikin sauran abokaina na cikin dakin, ko da mutane suka zo aka leka cikin dakin mutum biyu sun rasu, Rilwanu da Muhammadu Sani,” inji shi.

Ya ce, Hausawan da ke kasuwar suna shirin shiga dakin domin fito da gawarwakin, sai Yarbawan da ke yankin suka ce atafau ba za a shiga dakin ba. “Da isar shugabar matsafan yankin, sai ta ce wai dama an taba sata a kasuwar aka yi tsafi, to wai tsafin ne ya kama wadanda suka yi satar, kuma idan irin haka ta faru sai an yi wasu al’adu kafin a dauki gawar. Ana cikin wannan cece-kuce tsakanin Hausawa da Yarbawan ne, shugabar matsafar ta zo, ta ce kowa ya kauce daga kusa da dakin, ta zagaye kofar dakin da assabari da wani bakin kyalle, can sai ga wadansu matsafan da yawa, sun zo dauke da bakin dan akuya da farin rago da kaji uku da  manja mai yawa, nan suka yanka dan akuyar nan kuma suka zagaye dakin da manja,” inji shi,

Ya ce, “Ana cikin haka ne bayan Sallar La’asar, sai ga motar ’yan sanda, “Ko da suka tsaya sai muka ga DPO ya fito daga cikin motar tare da yaransa, bayan ya gana da mai filin sai DPO ya ce, a shiga a dauko gawarwakin a sa a mota.”

Mahaifin Rilwanu daya daga cikin leburorin da suka rasu mai suna Malam Yunusa ya shaida wa Aminiya cewa, su asalin mutanen Karamar Hukumar Kankara ce a Jihar Kastina. “Ina kwance ina barci kusan karfe 12:00  na rana, sai aka aiko wani daga cikin abokan aikinsu ya shaida min tsawa ta fada a Kasuwar Koso har wadansu sun rasu, kuma  Rilwanu na cikin wadanda suka rasu. Nan take na je na fada wa liman cewa za mu dauki makara mu dauko gawar Rilwanu a Kasuwar Koso, muna shirin daukar makara, sai ga labari ya zo cewa matsafa sun hana a taba gawar, sai na tafi gidan Sarkin Hausawa na shaida masa abin da ke faruwa, a gabana ya kira waya ya ce mu bari sai an sauko daga Sallar Juma’a,” inji shi.

Ya ce, da suka koma bayan Juma’a, sai ya ce su tafi wajen DPO,  “Lokacin da muka je wajen DPO baya nan, sai da muka dade a zaune sannan ya zo, bayan sun tattauna da Sarkin sai na ji DPO ya ce, mu jira shi zai je wajen da kansa, can sai ga DPO ya dawo dauke da gawarwakin a mota. Shekarun Rilwanu 25, kuma bai jima da dawowa daga gida a Arewa ba, da ma ya je ne saukar karatun kanensa da aka yi. Daya mamacin Muhammadu Sani, mutumin Argungu ne akwai ’yan garinsu a nan Shagamu, lokacin da lamarin ya faru sun kira mahaifinsa sun shaida masa, ya ba da umarnin a yi jana’izarsa a nan Shagamu haka kuma aka yi, fatanmu Allah Ya jikansu Ya yi musu gafara,” inji shi.

  Mutum hudu da suka tsira a lokacin da tsawar ta fada a dakin da suke
Mutum hudu da suka tsira a lokacin da tsawar ta fada a dakin da suke

Tsawa a al’adar Yarbawa

Wakilinmu ya tattauna da Alhaji Rufa’i Wazirin Hausawan Shagamu wanda haifaffen garin ne da ya tashi cikin Yarbawa, iyaye da kakanni suka yi mu’amaloli da su har da auratayya wanda hakan ya sa suka san da yawa daga cikin al’adun Yarbawan, kuma ya shaida wa Aminiya cewa: “Tsawa a al’adar Yarbawa wacce suke kira Shango sun dauke ta ne a matsayin wani laifin da aka aikata a wajen da ke jawo yin ta. Idan aka yi wani laifi kamar sata ko cin amana ko neman matar wani da makamantansu, to idan wanda aka yi wa laifin bai hakura ba, ya je wajen wadansu mutane da ake ce da su SHANGO wato masu bautar tsawa,  idan aka fada musu suka yi wasu tsibbace-tsibbacensu, sai su ce tsawa za ta fada wa wanda ya yi laifin in hadari ya taso. Duk inda tsawar ta fada to Yarbawa na guje wa wajen, har sai an sanar da matsafan da ake ce da su Shango, sun zo sun yi wasu tsibbace-tsibbace tukun kafin a taba wani abu a wajen da tsawar ta auku.”

Ya ce, a wani lokacin ma Shango ne ke daukar gawar su je su binne ta, kuma ko ’yan uwan mamacin za su dauki gawar to sai bayan an gama al’adun tukunna Musulmi ne ko Kirista. “Haka na faruwa ne saboda Yarbawa suna tafiya ne da addini da al’adunsu, kuma a da idan aka yi tsawa a wata unguwa, to in aka ga hadari ya taso barin unguwar ake, wadansu ma sun kaurace wa unguwar ke nan har abada,”. inji shi.

Al’ummar garin Shagamu sun yi murnar ganin yadda aka warware matsalar cikin ruwan sanyi da taimakon sanya Sarkin Hausawa da jami’an ’yan sandan yankin saboda tarihi ba zai manta da rikicin garin Shagamu ba wanda asalinsa ke da alaka da wadansu matsafa ko tsibbace-tsibbace.

Kakakin Rundunar ’Yan sandar Jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa wakilinmu cewa bai samu rahoton lamarin ba,  inda ya ce zai yi bincike kuma zai kira wakilinmu domin karin haske, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai kira ba.