✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda matsalar satar shanu ta canza rayuwar Fulani

Matsalar satar shanu matsala ce da ta dade tana ci wa Fulani makiyaya tuwo a kwarya. kauyen Chaza da ke garin Suleja, daya ne daga…

Matsalar satar shanu matsala ce da ta dade tana ci wa Fulani makiyaya tuwo a kwarya. kauyen Chaza da ke garin Suleja, daya ne daga cikin dimbin wuraren da wannan matsalar ta yi karamari. A zantawarsa da Aminiya, Sarkin Fulanin kauyen, Malam Idris Abdulkadir ya bayyana irin mawuyacin halin da suka samu kansu a yankunan da suke rayuwa tun fil’azal sakamakon hare-hare da kuma yadda, a wasu lokuta, bata gari ke raba su da dabbobinsu.
Sarkin ya ce: “Na kasance a wannan wurin fiye da shekara 60 ke nan, tun lokacin da iyayena suka dawo nan daga wani yanki kusa da garin Izom. A lokacin al’ummar Fulani na rayuwa ne ta hanyar tafiye-tafiye daga yankin Arewacin kasar nan zuwa Kudanci, su karade duk wani lungu da sako na fadin kasar nan tare da dabbobinsu cikin zaman lafiya da fahimtar juna da dukkannin kabilun da suka tarar a kan hanyarsu.”
Ya ci gaba da cewa lokacin da mahaifinsa ya tare a kauyen, bukkoki kadan ne a garin da wasu gonaki kalilan mallakin wasu jama’a da ya samu a wajen.
Ya ce an samu karin yawan jama’a a kauyen, ga kuma yadda al’umma ke kara dawowa garin a fatansu na gudanar da ayyukan gona da kasuwanci.
Jagoran Fulanin kauyen ya ce tarihin rikicin Fulani da Manoma ya fara ne a shekarun 1960, a lokacin da burtalin kiwon da Fulani ke amfani da shi ya fara bacewa, lamarin da ya tilasta musu bin wasu hanyoyi na daban wadanda kuma gonakin wasu jama’a ne. Amma ya ce a wancan lokacin,   cikin hanzari ake samu nasarar shawo kan takaddamar, saboda yadda shugabanni suka kasance masu gaskiya  da aiki tukuru, sabanin yanzu da suke karbar cin-hanci don goyon bayan wani bangare a yawancin rikice-rikicen da ke faruwa.
 Sarkin ya ce  matsalar satar shanu ta zama wani lamari mai ban tsoro kuma mahukunta sun zura idanu duk lokacin da wannan matsalar ta bijiro wa al’umma. Ya ce a da, barayin shanun suna amfani ne da makami kamar kwari da baka don kai farmaki, wanda ba wuya suke dakilewa kuma su karbo dabbobinsu, amma a yanzu suna zuwa ne da muggan makamai, wannan ne ya sa suke cin karensu babu babbaka.
Girman asarar da suke tafkawa
Sarkin ya ce babban abin da ke daure musu kai shi ne yadda da zarar an yi awon gaba da dabbobin nasu, to shi ke nan sun yi batan-dabo, ba a kara jin duriyarsu. “Sabanin lokacin iyayenmu, wanda idan mutum ya bi sawu, akwai yiwuwar gano inda suke. Amma a yanzu idan barayi suka sace shanu, to daga nan ba za a kara jin amonsu ba, ballantana labarisu.” Inji shi.
Ya ce kimanin wata biyu da suka wuce, an sace wasu shanu daga wani kauye da ke makwabtaka da su, mai suna Bamburu. A lokacin maharan sun umarci makiyayin da ya kwance musu dukannin shanunsa, bayan sun dora masa bindiga a ka. Bai yi wata-wata ba ya bi umarninsu, suka tasa keyar shanun, wanda har zuwa yanzu babu labari.
“Sun tafi da shanu kimanin 150, wadanda mallakin mutum uku ne, wato  Alhaji Tanko da Alhaji Agage da kuma Muri, wanda yake Bayarabe ne. Saboda faruwar wannan al’amarin, kowane lokaci muka ji wani motsi, ko muka hangi wani haske daga nesa, mukan kaurace wa dakunanmu don neman wajen buya a daji. Hakazalika ba ma iya gudu da shanunmu, muna barinsu ne a hannun Allah. Yawancin Fulanin da suka rasa shanunsu karo daya zuwa biyu, sun yi kaura zuwa jihohin Kogi da Kwara a yankunan da ke kusa da Saki da Offa, saboda a can da wahala ake samun matsalar satar shanu.” Inji shi.
Basaraken ya bayyana wani al’amari da ya faru a wani gari mai suna Fadaman Abuchi, inda wani mutum ya samu shanu guda uku da sanyin safiya daure a jikin wata bishiya bayan barayi sun sace su da daddare.
Ya kara da cewa ana yawan samun rahoton sace-sacen dabbobi a wannan wurin, amma ko da sau guda ba a taba samun asarar rai ba. Daga nan ya yi nuni da wata hanya wadda ya ce daga nan ne barayin shanun ke shigowa kauyen.
A doke ka, a hana ka kuka
A cewarsa, Ardo Suleja Malam Salisu Muhammad, wanda gidansa ke tsakanin wasu tsaunuka biyu, ya ce hatta ’ya’yansa kanana sun san abubuwan da suke faruwa dangane da matsalar satar shanu.  Ardon yana da iyali sosai da ke zaune a wasu bukkokin Fulani guda biyu, kodayake, ya ce bai jin dadin yadda ake ci gaba da dora wa Fulani laifin ta da zaune tsaye, alhalin kuma su ne suka fi tafka asara.
“Mutanenmu ne ake dora wa laifin da wasu suka aikata. A sace mana dabbobi, wanda a wasu lokuta idan aka yi rashin sa’a makiyayanmu su rasa rayukansu a kokarin kare dukiyoyinsu. Ka ga mu muka fi kowa asara, amma abin mamaki mu ake dora wa laifi a kowane lokaci.” Inji Ardon.
Ya kuma bayyana cewa barayin shanun na cin karensu babu babbaka a yankin. Malam Salisu ya ce a kwanakin baya, an sace  shanu da suka tasamma guda 50 a kauyukan Numba  da Malam Karo da kuma Kuchiko, inda wani Bafullatani da ke kauyen Malam Karo ya rasa ransa, bayan  samun nasarar kwato dukan shanun da aka sace.
“Ba ma iya runtsawa da idanunmu. Mukan shafe duk tsawon dare muna duba shanunmu, idan kuma muka ji wani motsi mukan yi kokarin sanar da ’yan uwanmu ta waya. Hakazalika, muna da lambobin wayar jami’an tsaro, musamman ma jami’an ’yan sanda da kuma ’yan sintiri, wadanda muke tuntuba a lokacin da bukatar hakan ta taso, saboda yadda suke agaza mana sosai.” Inji shi.
A kasuwar kauyen Dikko, wani jagoran Fulani ne mai suna, Ardo Wuse, Alhaji Yunusa Magingi, wanda ya ce jama’arsa sun kasance a cikin mawuyacin hali a lokaci mai tsawo. Ya ce, “ina samun rahotonnin satar shanu da kuma farmakin da ake kai wa mutanenmu ba tare da laifin zaune ba, bare na tsaye. Ban san dalilin da laifin wani zai shafi na wani ba.”
Jagoran Fulanin ya ce hare-haren ba su bar hatta ’ya’yansu ba kuma mutanensu sun zama wadanda kowane mahaluki zai zo ya huce takaicinsa a kai. “Me ya sa kowa yake zarginmu da ta da zaune tsaye, musamman ma idan hari ya faru a kan wasu da  ake gani ba ma ga-maciji da su?” Inji shi.
Ya ce mutane da dama suna shiga rigar Fulani don ta da zaune tsaye, wanda daga baya  ake dora musu alhakin aikata hakan.
Alhaji Yunusa ya ce Fulani sun dade suna cikin wannan halin, wanda idan da lissafawa za a yi, asarar da suka yi za ta tasamma biliyoyin Naira. Ya kuma koka  da cewa, “Ba wanda yake maganar biyanmu diyya duk da kiraye-kirayen da jama’armu suke yi na neman agaji don a kawo karshen wadannan rikice-rikicen da kuma matsalar satar shanu.”
A karshe ya ce, a matsayinsa na shugaba ba zai ce ba bata gari a cikin jama’arsa ba, wadanda a wasu lokuta suke ta da zaune tsaye. “Amma wannan ba ta zama hujja da za a dogara da ita kan cewa dukkanninmu masu ta da zaune tsaye ne ba.”
Ya ce matsalar ta fi kamari a bara, amma a bana mutanensu sun yi kaura zuwa Kudancin kasar nan, inda a can ma suke fuskantar farmaki da kuma kisa a wurare da dama.
Malam Abdullahi Usman shi ma wani jagoran Fulani ne, wanda ya ce jama’arsu a yanzu suna fuskantar dimbin kalubale kuma suna iya kokarinsu wajen wanke kansu daga duk wani zargin aikata laifin da ba su da masaniya a kai.
Ya ce kwana-kwana nan aka sace wasu shanu mallakin wani shugaban al’ummar Gbagyi, amma sai wasu suka ce Fulani ne suka aikata hakan. Ya ce shugaban ne ya kashe wutar rigimar inda ya ce, “Ya san Fulanin masarautarsa ba za su aikata hakan ba”.
Malam Abdullahi ya ce, “Da abin ya koma rikici saboda yadda al’ummar Fulani suka fusata ganin yadda su kansu sun taba yin asarar shanu fiye da guda 100 kafin batar na sarkin, amma ba wanda ya jajanta mana, sai lokacin da sarkinsu ya yi asarar nasa ne za su ce mu ke da alhaki. Wannan ba adalci ba ne.” Inji shi.
Dalilan da suka sa Fulani ne matsalar ta fi shafa
Wasu Fulani sun bayyana cewa rayuwarsu ta ta’allaka ne a kan  kiwon dabbobi, amma a cewarsu, a da tsoron da suke da shi lokacin da suka tafi kiwo shi ne na muggan dabbobin dawa, wadanda kan kawo masu farmaki. Amma sun ce kalubalen da suke fuskanta a yanzu ya fi kuma yanayin ya canza, matsalar tana shafar mutane da dama.  
A cewar Usman Abdullahi, yanayin mahalli ya kara taimakawa wajen fuskantar farmaki daga barayin dabbobi. Ya ce Fulani mutane ne makiyaya, suna yawo daga wuri zuwa wuri, wanda wannan kan sa yana sa su kara fuskantar hare-hare duk lokacin da suka fita kiwo.
Ya ce: “A duk lokacin da mutanenmu ke tafiya, ba a rasa wasu da suke biye da su da munmunar aniya don sace masu shanu, ko kai masu farmaki. Wannan ya sa a yanzu ba ma iya barin kananan yaranmu tafiya kiwo, saboda yadda hatta manyan ma ba su tsira ba.”
Ya ci gaba da cewa makaman da Fulani ke rikewa don ko-ta-kwana, makamai ne kanana kamar su adda da wukake, wadanda kuma yanzu jami’an tsaro ke karbewa daga gare su. Wannan ma na kara sa su fuskantar farmaki. “Saboda a duk lokacin da aka kawo musu hari, ba sa iya kare kansu. Su kuma maharan sukan tasar masu ne rike da manyan makamai, kamar bindigogin zamani. Bafullatani yana rike da sanda ne a kowane lokaci, wadda kuma ba zai iya kare kansa da ita ba. Kuma idan aka same ka da wani makami za a ce kana neman ta da zaune tsaye ne. Wasu mutanen kuwa an bar su su rike makamai da sunan kare kansu. Me ya sa mu za a haramta mana yin hakan?” Inji shi.
 A cewar Ardon Wuse,  Fulanin sun yi amannar cewa hare-haren da ake kai wa jama’arsu na jefa su cikin mawuyacin hali: “Idan aka kai mana farmaki, a ce mun yi laifi. Har ila yau, idan muka tashi domin kare kanmu, shi ma ba mu tsira ba daga zargin aikata laifi.” Inji shi.
Damuwar da Fulanin ke ciki
Akwai karuwar damuwa daga bangaren matasan Fulani, wadanda suke ganin wani yunkuri ne na durkusar da sana’ar da suka gada iyaye da kakanni. Amma a ganinsu ba za a iya raba Bafullatani da shanunsa ba. Saboda yadda duk wani abu da ya shafe su, ya shafe shi. “Ba wani Bafullatani da zai rayu ba tare da shanunsa a kusa ba kuma rayuwarsu ta ta’allaka ne a kansu. Bugu da kari, Bafullatani ba ya mutuwa ba tare da ya bar wa ’ya’yansa gadon shanu ba.”’ Inji wani matashi Bafullatani.
Hare-haren da ake wa matansu ya kasance wani abu da shi ma yake ci wa Fulani tuwo a kwarya. daya daga cikin matasan ya ba da misali da abin da ya faru da wata Bafullatana da ke unguwar Dei-dei, inda ya ce: “Ba za mu sanya ido mu ga ana yi wa matanmu fyade ba. Idan ba wanda zai kare su, mu za mu kare mutuncinsu. Saboda Fulani ba wawaye ba ne kuma ba masu ta da zaune tsaye ba ne.” Inji shi.