✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mazauna Kaduna ke kallon tsawaita dokar hana fita

Mazauna Kaduna na ci gaba da fadin albarkacin bakinsu game da sanarwar da gwamnatin jihar ta bayar cewa ta tsawaita dokar hana fita da kwana…

Mazauna Kaduna na ci gaba da fadin albarkacin bakinsu game da sanarwar da gwamnatin jihar ta bayar cewa ta tsawaita dokar hana fita da kwana 30 kuma ta kara tsanani a wasu bangarorin.

Suleiman Abubakar Baba magidanci ne a jihar, ya kuma ce karin kwanaki 30 din da gwamnatin ta yi zalunci ne ga talaka domin ba wai an yi wa talakan wani abu ba ne da zai rage masa radadi.

“Ya kamata idan har gwamnati za ta kara ta yi wa mutane wani abu na tallafi wanda zai rike su ko da na sati biyu ne akalla.

“Amma a ce tsawon kwanaki 60 ba a yi wa mutane komai ba, gaskiya wannan zalunci ne. Kuma ya kamata a gyara,” inji shi.

Da aka tambaye shi ba ya ganin gwamnatin jihar ta dauki matakin ne domin kare rayukan jama’a, sai ya ce, “Eh abin da ta yi abu ne mai kyau amma sai a duba a gani cewa akasarin mutanen Kaduna sai sun fita za su nemo abin da za su ci. Abin da ya kamata gwamnati ta lura da shi ke nan kafin daukar wannan mataki na karin kwanaki talatin,” inji shi.

Shi ma ‎Abdulkadir Isa Toro magidanci ne mazaunin Dan Mani.

A cewarsa matakin da gwamnan ya dauka na karin kwanaki 30 ya yi tsauri matuka idan aka yi la’akari da halin babu da jama’a ke fama da shi.

“Zan iya cewa gwamnatin ta dauki matakin ne saboda kare rayukan al’umma kuma hakkinta ne ta yi hakan. Amma ya kamata mai girma gwamna ya tausaya ya bar kwanaki biyun da ake fita duk mako ba tare da ya rage zuwa kwana daya ba.

“Idan ya so sai ya matsa wajen ganin duk wanda zai fita waje ya sanya takunkumi da safar hannu in ya so duk wanda aka samu bai sanya takunkumin ba ko safar hannu sai a yi masa tara.

“Yin hakan zai zama kariya ga mutane domin a yanzu [saboda] rashin fitar mutane na cikin wani hali na rashin kudi,” inji shi.

Ita ma Malama Halimatu Rani, malama a makarantar Islamiya ta Ulul’Albab Tudun Wada Kaduna da Solid Learning Field dake Hayin Malam Bello Rigasa  ta nuna rashin gamsuwa da matakin gwamnatin.

“Yanzu haka a matsayin mu na malamai muna nan a gida babu albashi babu komai saboda sai iyaye sun bayar da kudin makaranta ake samun biyan malamai da shi.

“Ga Azumi an fara, amma babu kudi; saboda haka ni a ra’ayina karin kwanaki 30 da gwamna ya yi bai yi mana dadi ba saboda mu da koyarwa muka dogara”, inji ta.

‎Auwal Tela ma cewa ya yi, “Gaskiya muna cikin radadi sai dai kurum mu nemi Allah ya yaye mana wannan matsifa.

“Abin babu dadi ko kadan musamman rage kwanaki daga biyu zuwa daya da ya yi. Allah dai ya ba mu mafita”, inji shi