✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda muka fara jaridar Trust shekara 20 da suka wuce – Malam Kabiru Yusuf

A ci gaba da shirye-shiryen bikin cika shekara 20 da fara buga jaridar Trust da Aminiya, Shugaban Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust…

A ci gaba da shirye-shiryen bikin cika shekara 20 da fara buga jaridar Trust da Aminiya, Shugaban Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya da sauransu, Malam Kabiru Yusuf ya yi bayanin yadda suka fara buga jaridar shekara 20 da suka gabata.

Malam Kabiru Yusuf ya fadi a lokacin da yake zantawa da manyan editocin kamfanin a babban ofishin jaridar da ke Abuja, cewa “Muna bukatar aiki ne a lokacin, shi ne sai muka nema wa kanmu, ga shi yanzu mun kai shekara 20.” 

Malam Kabiru Yusuf ya ce sun fara buga jaridar ce a daki daya a Kaduna, inda suka fara da Weekly Trust wadda a lokacin ake bugawa ranar Jumu’a. “Mun fara buga jaridar Weekly Trust ce a lokacin mulkin marigayi Janar Sani Abacha, amma lokacin mun dauki aniyar yin aiki ne mai inganci ba wai mu zama ’yan amshin shata ba.

“Bayan ’yan watanni sai Janar Abdulsalami Abubakar ya karbi mulki da alkawarin cewa zai mayar da mulki ga farar hula, wanda hakan ya sa muka yi tunanin fara buga jaridar a kullum da jaridar siyasa,” inji Malam Kabiru Yusuf.

Ya kara da cewa duk da cewa sun fuskanci kalubale da yawa, kamfanin ya ci gaba da aiki har shekara 20, “A cikin shekara 20 da suka wuce, Kamfanin Media Trust ya kirkiri wasu bangarori da dama. Bayan fara jaridar Weekly Trust wanda yanzu ake kira Daily Trust on Saturday a watan Maris na 1998 a Kaduna, kamfanin ya fara buga jaridar kullum wato Daily Trust a watan Janairun 2001 a Abuja.

An fara jaridar ranar Lahadi wato Sunday Trust wadda ake yanzu ake kira Daily Trust on Sunday a shekarar 2006, sai kuma jaridar Aminiya wadda aka fara a shekarar 2006, sai jaridar yara mai suna Teen Trust da aka fara a shekarar 2015 da kuma ta wasannin mai suna Trust Sport da aka fara bara,” inji shi.

Hakanan kuma kamfanin yana buga mujalla da ke nuna al’adun Afirka mai suna Kilimanjaro, da mujallar mata mai suna Tambari da wasu bangarorin wasanni irinsu Golf Digest.

Da yake bayanin yadda karancin kudi ya yi barazana ga kamfanin a baya, Malam Kabiru Yusuf ya ce, “Muna da sa’a sosai. Duk da cewa akwai kalubale, amma burinmu shi ne mu samar da jaridar da za ta zamo amintacciya a ko’ina. Za mu ci gaba da fuskantar kalubale, amma za mu yi kokari mu magance su a duk lokacin da suka zo.”

Ya kara da cewa murnar cika shekara 20 murna ce “Ta samun damar cika shekara 20, kuma lokaci ne da za mu yi waiwaiye sannan mu gode wa Allah da Ya sa har yanzu muke ci gaba da aiki.”

Taron bikin cika shekara 20 din, zai kunshi taron tattaunawa inda za tara manyan ’yan jarida  da masu kamfanonin buga jarida su tattauna a kan: Aikin jarida a matsayin kasuwanci- labarai, ra’ayoyi da kuma tallace-tallace.”

Ya ce yanzu kamfanin na da babban ofishi a Abuja, kuma yana da ofisoshin da ke buga jaridar a Legas da Kano da Maiduguri baya ga Abuja, kuma kwanan nan za a bude na Sakkwato.

Da yake amsa tambaya a kan me ya sa kamfanin ba ya yin tallace-tallacen da ke da alaka da kayan maye da ire-irensu, Malam Kabiru Yusuf ya ce, “Ba ma so mu mutane su ci gaba da amfani da su ne saboda suna da illa.”

Ya kara da cewa nan gaba dole kamfanin ya yi amfani da ci gaban kimiyya domin ci gaba kamfanin, sannan ya bayyana cewa suna shirin zuwa kasuwar zuba ta Najeriya domin samun wadanda za su sanya hannun jari a kamfanin.