Da Dumi Dumi

Yadda muka gano gawar Janar Alkali- Rundunar Soja

An gano gawar Manjo Janar Alkali a wata tsohuwar rijiya a Jihar Filato kamar yadda rundunar soja ta tabbatar, inda ta bayyana yadda suka gano gawar.

An gano gawar ce a tsohuwar rijiyar da ke garin Guchwet a yankin Shen na Karamar Hukumar Jos ta Kudu na Jihar Filato.

Komandar Runduna na 3, Brigediya Janar Umar Mohammed wanda shi ne ke jagorantar bincike a kan bacewar Janar Alkalin, ya ce daya daga cikin mutum 8 da ake zargi da suka kawo kansu wajen ‘yan sanda ne ya nuna musu rijiyar.

Komandan ya kara da cewa daga nan sai suka kwalfe rijiyar, sannan aka ciro gawar janar din a ciki, inda aka lullube tad a tutar Najeriya, kamar yadda wakilinmu ta gani da idonta.

Bayan an ciro gawar ne sai aka sanya ta a cikin motar daukar marasa lafiya a tafi.

ADVERTISEMENT
Share