✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda muka gano matattu na karbar albashi da fansho a Bauchi – Sanata Gumba

Kwamitin da tsohon Shugaban Ma’aikatan Jihar Bauchi Sanata Adamu Ibrahim Gumba ya shugabanta ya ce ya gano matattu sama da 500 suna karbar albashi a…

Kwamitin da tsohon Shugaban Ma’aikatan Jihar Bauchi Sanata Adamu Ibrahim Gumba ya shugabanta ya ce ya gano matattu sama da 500 suna karbar albashi a jihar, yaya aka yi?

Yaya kuka gudanar da aikin da aka dora muku?

Wannan kwamiti na tantance ma’aikata da fari an yi zaton su  dubu 41 da 448 da ba su da lambobin tantacewa na asusun ajiya a banki, amma da muka fara aiki sai muka fahimci ma’aikata dubu 30 da 226 ne ba su da lambobin tantancewa wato BBN. Da muka fara aiki mun zaga dukkan kananan hukumomin jihar a makon farko muka bada rahoto aka biya ma’aikatan gwamnati da muka tantance albashinsu, muka sake komawa kananan hukumomi muka tantance ma’aikatan kananan hukumomi da ’yan fansho, nan ma muka dawo da sunayen mutanen da muka tantance muka yarda aka biya su albashinsu. Tantancewa ta karshe da muka yi makon  jiya ita ce wadda yanzu haka mun samu ma’aikatan jiha 300 da na kananan hukumomi 869 wadanda muka bada shawara a biya su albashinsu na watan Oktoba da Nuwamba da Disamba. Insha Allahu za mu mika sunaye ga Akanta Janar domin a yi aiki a kansu a biya su. Amma duk da dogon lokacin da muka bayar domin ma’aikata da kuma masu karbar fansho su bayyana a gabanmu akwai da yawa da suka ki bayyana. Kuma dole ne mu kammala aikinmu, mu mika rahoto saboda haka lokacin da muka kammala aikinmu akwai mutum 4,578 da suka ki bayyana a gabanmu duk da dama da muka ba su na su bayyana a gabanmu sau biyu. Ba mu san dalili ba. Watakila cikinsu ana zargin ana iya samun wadanda ba ma’aikata ba ne, ana kuma iya samun cikinsu wadanda ba su samu labarin ayyukan kwamitinmu ba. Wadannan ma’aikata mun mika sunayensu ga Mai girma Gwamna kuma mun bada shawarar a ba su dama ta karshe domin su bayyana a gaban kwamitin, in kuma ba su bayyana ba, to shi ke nan za a dauka cewa su ba ma’aikata ba ne. Lokacin da muke aikin mun samu mutane wajen 596 wadanda mun tabbatar da cewa sun rasu amma ana karbar fansho da kuma albashinsu. Wadannan mun bada shawara ga Mai girma gwamna a cire sunayensu gaba daya. Amma gaba daya daga cikin mutum dubu 30 da 226, mun tantace mutum dubu 24 da 796 wadanda muka tabbatar ma’aikata ne ko masu karbar fansho a Jiihar Bauchi mun bada shawara a biya su, akwai kuma mutum 256 wadanda sun bayyana a gabanmu sau daya sun sake bayyana na biyu amma muna tababar cewa ba ma’aikatan kwarai ba ne, ba mu yarda da takardunsu ba, mun bada shawarar yadda za a yi. Watakila kwamitin aiwatar da wannan rahoto ya sake bada dama a gan su, a samu wani sabon bahasi kafin a ce an cire sunansu daga cikin wadanda ake biya albashi.

Me ya sa ake samun kwan-gaba-kwan-baya na yawan ma’aikatan?

Tun farko akwai tsohon Kwamishinan Kudi na Jihar Bauchi wanda ya yi murabus, shi ne ya bada adadin nan na farko na dubu 41 da 488 da aka kafa kwamitinmu sai muka tafi ma’aikatar muna neman a ba mu sunayen gaba daya, babu wanda ya ba mu, muka je wajen Akanta Janar shi ya ba mu nasa amma bai kai wancan adadi ba, muka sake dawowa wajen sabon kwamishina muka ce ya bincika ina sauran mutane da ba su da BBN shi ma sabon kwamishina ya ce ba shi ne ya bada wancan na farko ba, saboda haka abin da Akanta Janar ya bayar mu yi aiki da shi don shi ne tabbas a wajensa.

Me ya sa ba ku koma wajen tsohon Kwamishinan da ya yi murabus din ba?

Gaskiya babu damar mu koma wajensa, amma a gaskiya abin da ya sa ba mu damu mu koma ba, ai wadannan ma’aikata kadan ne daga cikin ma’aikatan Jihar Bauchi, don akwai mutane fiye da dubu dari da su ma ya kamata a tantance su a dubi halin da suke ciki. Shi ya sa ba mu damu ba muka hakura da dubu goman watakila a gaba za a iya tantance su.

Yanzu me cece fatarka a karshen wannan aiki?

Ni fatar da nake da ita tunda wannan gwamnati mai adalci ce to ta yi adalci ta sake ba su dama, don ka ga da ita wannan lambar tantacewa ta BBN da a cikin ka’ida cewa sai kana da ita za a biya ka albashi, bai fi shekara hudu zuwa biyar ba da aka fara amfani da ita. Gwamnati ce yanzu ta ce ya kamata a sa BBN cikin tsarin biyan albashi. Muna fata gwamnati za ta yi amfani da damar da ta samu domin daukar sababbin ma’aikata saboda akwai ma’aikatunmu da yawa da suke bukatar a kara ma’aikata.