✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda muka hadu mu hudu muka rubuta tarihin Shata – Aliyu Kankara

Dokta Aliyu Ibrahim Kankara, malami ne a Jami’ar Tarayya Dutsin-ma. A kwanakin baya ya fitar da sabon littafin tarihin marigayi Alhaji Mamman Shata, wanda ya…

Dokta Aliyu Ibrahim Kankara, malami ne a Jami’ar Tarayya Dutsin-ma. A kwanakin baya ya fitar da sabon littafin tarihin marigayi Alhaji Mamman Shata, wanda ya sa wa taken SHATA: Mahadi Mai Dogon Zamani. Mun fara tattaunawa da shi a makon jiya, yau kuma ga ci gaba:

 

Bayan ka dawo daga Legas, me kuma ya faru?

Na dawo daga hidimar kasa a 1995. Sai abokan aikina na Kano suka nuna gazawa, ga buga littafi na jan kafa. Waje daya kuma na samu labarin Ibrahim Sheme daga Ya’u Wazirin Shata da wani abokina Kabir Dan’azumi Kankara. Kafin Ya’u waziri ya kara tunkara ta da maganar Sheme sai kwaram ran nan Shata ya yi mini bayaninsa. Ya ce mini na san shi? Na ce masa ‘ban san shi ba, ba mu taba haduwa ba.’ Shata ya ce mini ya kamata mu hadu, abin da ba ni da shi ya taimaka mini da shi, shi ma abin da ba ya da shi, da ni nake da shi sai in ba shi’ amma bai nuna yana so mu hade ba, amma ni a fahimtata haka Shata ke nufi, da yake yana da yalwatacciyar basira.  Magana daya yana iya karya ta ya shiga lunguna, ya bad da mutum. A waje daya, Ibrahim Malumfashi (wanda ya zama Farfesan Hausa daga bisani) ma ya taba yi mini maganarsa, amma ba shi ya kai ni wurinsa ba. Ni na kai kaina wurin Sheme a gidansa na Badikko din nan da dare, ina kuma zaton cikin 1995 ne, don lokacin ban ma gama hidimar kasa ba. Kabir Dan’azumi shi ya kai ni wurinsa (ba Ibrahim Malumfashi ba).

Sheme ya yi murna da ganina, cewa ya dade yana jin labarina amma sai ran nan muka hadu. Ya zaunar da ni, ya dauko mini aikinsa na littafin Shata na gani, na kuma yaba. Tun daga ran nan ba mu kara haduwa ba sai cikin 1997 da na koma Kwalejin Kimiyya ta Kaduna da koyarwa. Ya taba tarar da ni a ofis, ya nuna ya kamata idan za mu hade ayyukanmu wuri daya mu yi haka, idan kuma ba mu yi to kowa ya kama gabansa. Ma’ana, ya zo ya ji matsayina a kan batun.

Ran wata Asabar da safe Ibrahim Sheme ya zo wajena ya ce in dauko masa littafina ya gani. Ba musu, na shiga na dauko littafi gaba daya na ba shi. Muna nan muna nan sai ya tura ni in yi hira da wadansu mutanen Shata, don shi ayyukan ofis sun sha masa kai. Kuma ina ta yi masa biyayya saboda ko ba komai akwai tazarar shekara kimanin 2 ko 3 ma kuma yana gabana a jami’a. Inda duk ya tura ni ba gardama sai in tafi, wato a nan Kaduna. Sannan  nakan dauke shi in kai shi ga wadansu da Shatan ya yi wa waka da shi bai ma san su ba. Misali, Malam Nagwandu Mai Nama, wanda ta hanyar Ahmadu Doka na san shi a Kaduna yake da zama. Sannan na dauke shi na kai shi ga Hauwa ’Yarbori, matar marigayi Sarkin Bori Sule a Titin Bashama Tudun Wada Kaduna.

To yaya batun hadewarku da sauran marubuta tarihin Shata biyu?

A cikin 1998 sai Sheme ya tafi Funtuwa, ya tarar da Shata, har makadin ya yi masa korafin cewa ya kwanta asibiti a Kano, inda ya samu labarin wadansu ’yan Kano su 2 suna rubuta tarihinsa daga bakin Shatan, don sun ma same shi aasibiti sun nuna masa aikin da suka yi. Ya ce wa Sheme ya tafi Kano ya nemo su, ya ce su zo Funtuwa yana kiransu don ya sanya su hade da mu. Amma Shata ya yi masa kashedin kada ya bayyana musu cewa bukatarsa a hade. Sheme ya dawo Kaduna ya same ni gidan marigayi Adamu Yusuf na BBC da dare, ya bayyana mini abin da ke faruwa. Har na bata rai sai ya ba ni hakuri ya ce haka Allah Ya so kuma mu yi fatan Allah sa abin ya zama alheri. Muka sa ranar tafiya Funtuwa, wato Asabar ta ran 19/9/1998. Tun ran Juma’a Sheme ya dauke ni a motarsa, tare da wani abokinsa muka tafi. Wanshegari da safe muka hadu da baki daga Kano a gaban Shata, har suka taho da abokinsu su ma, wani Aimana Datti Usman. Amma kafin haduwarmu sai da muka dan bi wadansu mutane muka yi hira da su a nan Funtuwa da safe, kamar Shehu Maigidaje da Hajiya Iya matar Shatan ta farko. Bayan an gaisa, ba bata lokaci Shata ya nuna da za a hade da ya fi, amma mu je mu yi shawara. Muka fito garejin motarsa, karshe muka yanke shawarar mu hudu mu zama daya ga wannan tafiya. Muka koma mu ka shaida masa.

Amma cikin ikon Allah sai Allah Ya mantar da Shata bai tuna wa Sheme da sauran bakin nan wancan zancen littafinsa da nake yi tare da kungiyar YWC ta Kano ba. Ni kuma saboda kawaici sai Allah Ya rufe mini baki saboda ma ina ganin ga wani sabon aiki an bude, to me za ya sanya in kawo zancen abin da ma ya wuce kuma? Muka koma waje muka rubuta takarda cewa mun hade wuri daya. Ibrahim Sheme shi ya rubuta takardar, ya mika mana muka rattaba hannuwa, sannan muka koma cikin zaure muka tarar da Shata. Ni da kaina na amshi takarda daga hannun Sheme na ba Shata ya sa hannu shi ma, a gurbin inda sunansa yake.

Ko yaya yarjejeniyar take a tsakaninku?

Da aka natsa sai daya daga cikinmu, Ali Malami ya tambayi Shatan cewa idan an kaddamar da littafin, me Shata ke so a ba shi a matsayin sallamarsa? Ya ce idan aka raba abin da aka samu kashi uku, aka ba shi kashi daya ya yi? Mu duka muka ce ya yi daidai, har yana barkwanci, yana cewa a ranar kaddamar da littafin ko motsi ya yi a wurin taron sai an yi ihu, muna ta dariya.

A nan take muka sanya Sheme ya jagoranci wannan tafiya. Amma ko a sannan din yawan littattafan da na rubuta na Hausa suna da yawa, ba a kan Shatan na fara rubutu ba. Mun aminta ya zama jagoranmu saboda shi ke da kwanfuta don haka a kyauta ya ce zai sanya a buga littafin kafin a kai shi madaba’a kuma sannan ya gwanance wajen rubutu tare da basirar rubuta littafi. Muka dauki hotunan tarihi tare da Shata har iri 12.

Tun daga nan kuka dasa aikin ke nan?

Akwai hirarrakin da abokanmu suka yi da wadansu jama’a a cikin kasa-kasan rikoda da ba su kai ga rubutawa ko fassara su ba, suka tattara suka ba mu. Shi kuma Sheme ya ba ni su, tare da ba ni umarnin in zauna in rubuta su in ba shi. Na himmatu na yi aikin na kai masa. Daga cikin hirarrakin akwai na Sidi Mijin Hotiho da Hauwa Mai Tuwo.  Shi ma Sheme, hirarrakin da ya yi a kaset-kaset ya ba ni in dai rubuta, a ciki akwai ta Laila Dogonyaro da Musa Musawa da Bawa Dungun Mu’azu.

Ya sanya ni na dukufa wajen nemo sauran hirarraki daga mutane, shi ma yakan dan yi hira da wadansu kadan, don ba ya da lokaci, tunda ga ni ya samu.

Yaya tafiyarku ta kasance kuma?

Kwaram tun ma ba a je ko’ina ba, bayan wata tara sai Allah Ya yi wa Shata rasuwa ranar Juma’a 18/6/1999. Hakazalika Sheme ya kirkiri wallafa Mujallar FIM a cikin watan Mayu 1999, ga kuma aikin rubuta tarihin Shehu Musa ’Yar’aduwa da sabuwar Gwamnatin Obasanjo ta ba shi a kakashin wata Cibiyar Tunawa da Shehu Musa ’Yar’aduwa. A lokacin an sallame ni daga Kwalejin Kimiyya ta Kaduna ta hanyar rage ma’aikata, saboda haka ina zaune a Kaduna ba ni aikin komai sai dai rubuce-rubucen da ba za a rasa ba.

Wannan ya kara ba ni damar ci gaba da farauto labaru daga jama’a. Kuma Sheme kan tura ni ya ba ni kudin mota da na abinci zuwa Musawa. Dama tun cikin Maris din 1998 ya tura ni Gombe da Bauchi don ganawa da mutanen Shatan na can wajen. A takaice ba a gama aikin littafin nan ba sai ina da kashi 65 na aikin littafin. Sheme ya ba da gudunmawar kashi 25, sauran abokanmu daga Kano sun ba da gudunmuwar kashi 10.

Game da wakokin Shata da na ba da shawarar a tattara su a bangare daya na karshen littafin, shi da kansa Sheme ya ba ni aikin nemo su. Gaba dayan wakoki 638 da aka sanya duk ni na ba da su. Yadda aka yi na tattara su shi ne, da na ji wata waka ta Shata sai in rubuta ta a takarda in je ofishinsa in ba shi, koda ban tarar da shi ba sai in tura takardar a ’yar kafa ta karkashin kofa. Shi kuma da ya zo ya bude kofa sai ya gani. Sai ya dauka ya rubuta a kundin littafin.

A littafinmu mai dauke da shafuka 604, na gana da Hakimin Musawa, Inde Magajin Musawa da Sa’in Katsina Amadu Na-Funtuwa da wadansu dattawan Musawa, Hauwa matar Sarkin Bori Sule da Hassan na Husaini Mai Tsuntsaye da Babba Na-Kofar Gabas da Maigarin Sayaya Yahaya Salmanu da Tijjani Hashim Kano da Walin Kano Mahe da Ada Tela Daura da Ali Scorpion da Dagacin Falgore, Shu’aibu Bada-Bada da Alaramma Sulen Shata da Ali Dankane Musawa da Mamman Tsalahu Musawa (da matansu) da Hajiya Safiya Kumbula kanwar Shata da Danbaba Makadi Musawa (makadinsa na farko). Saura su ne Balan Guzun da kanen Shata da Bilkin Sambo da Sani Bakatoshi da Inuwa Dalibi da Uwawu Kano da Mairo Munar da Indo Musawa da Indon Danbaki da Garba Dan Ammani da Musa Dan Amare Musawa da Ayuba Mai Nama Musawa da Bala Abdullahi Funtuwa da Halle Jani da Garba Ja da Abba Natiti da Sabo Dogarai Kano. Sai Ahmadun Kari Garkuwan Bauchi da Bappa Ahmed Gombe da Musa Usman (tsohon Gwamnan Arewa maso Gabas) da Hajiya Indo ’Yar Mamman Gombe da Magaji Mai Ido Daya da Amadu Doka Mai Kukuma da kuma Alhaji Mayau Kaduna. Sai ’ya’yan Kungiyar Makada da Mawaka ta Kasa da Ali Dansaraki ’Yankara da Musa Danbade da Sarkin Damben Hadeja da Sankira Isiyaku Usman Galo da Abashe Yaro Maihoto da Dauda Mani da Garba (Yaro) Nagwandu Mai Nama da Ado Kankiya da Garba Kwagira da Salisu Bangul Dandaudu da Yahaya Dandaudu da Shehu Tsatso da kuma Abubakar Kashe-Kura Na Kofar Kaura.

Wadanda kuma suka rasu, na tattauna da iyalansu, sun hada da Sarkin Katsina Nagogo da Haruna Kasim da Maude Tabako da Ali Bagobiri da Mati ’Yammama da Dan Lagai-Lagai da Sani Audi da Sule Dan Wazifa da Sani Stores da Mamman Da da Garba ’Yammama da Alhaji Abdulwahabu Malumfashi da Sani Dankwara Malumfashi da Ahmadun Gaya da Ciroman Gombe Umaru da Adamun Pankshin (Ladi) da Garba Sarkin Malamai. Na kuma ziyarci Rediyon Tarayya na Kaduna sau da yawa, na yi hira da ma’aikatansu kamar su: Ofishin kasuwancin su, Dakin ajiye faya-fayai da Lawal Yusuf Saulawa da Nasiru Maiwada Malumfashi da Ahmed Aja Gwarzo da Rashida Bello da Shafi’u Zangon Aya da Yakubu Gombe da Ladan Kontagora da Ibrahim Bako da Ahmed Girei (dan uwan Dahiru Modibbo). Ni ne kuma na yi hira da wadansu ’ya’ya da matan Shata kamar su: Binta Mami da Magaji da Salisu da Sanusi da Amina da Mamuda da Binta Iya da Asabe (Zuwaira) da Hurera Yamai, Hadiza Falgore, Amina Dikke, Nasara Musawa, Yalwa, Binta Kankara, Hajiya Kulu Kaduna, Halima, Jamila. Wasu ma mutanen da na gana da su na manta da su.

Za mu kammala