✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda muka jefa siyasar Kudancin Kaduna a tsaka-mai-wuya – Dokta Bege

Dokta Katuka Humble Bege shi ne Shugaban Riko na Karamar Hukumar Kaura a Jihar Kaduna, kuma ya rike mukamai da dama a Jam’iyyar APC ciki…

Dokta Katuka Humble Bege shi ne Shugaban Riko na Karamar Hukumar Kaura a Jihar Kaduna, kuma ya rike mukamai da dama a Jam’iyyar APC ciki har da Shugaban Riko na Karamar Hukumar Jama’a sau uku. A tattaunawarsa da Aminiya, ya tabo abubuwa da dama da suka hada da batun siyasar Kudancin Kaduna:

Mene ne takaitaccen tarihinka?

Sunana Dokta Bege Katuka, na fito daga Karamar Hukumar Jama’a ce ta Jihar Kaduna. Na yi makarantar firamare a SPS da ke Keffi a Jihar Nasarawa. Daga nan na wuce Kwalejin Gwamnati ta Keffi, inda na koma Kwalejin Gwamnati da ke garin Kagoro a Jihar Kaduna. Bayan na kammala karatun sakandare sai na wuce Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda na zama Likitan Dabbobi (DBM) a shekarar 2007 zuwa 2008. A yanzu kuma ni ne Shugaban Riko na Karamar Hukumar Kaura a nan Jihar Kadunba.

Daga shiga siyasa cikin lokaci kankane ka shahara a Kudancin Kaduna, mene ne sirrin?

Godiya ta tabbata ga Allah wanda Shi ne kashin bayan dukkan nasarorin da na samu. Baya ga Shi kuma ina godiya ga ubangidana, wato Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i. Baya ga nan, zan iya cewa yarda da kanka da kuma shirya wa gabatar da abubuwa masu kyau tare da zaben mutanen kwarai a lokacin da ya dace, sun taimaka min matuka. Na fara shiga harkokin siyasa ne da wata kungiya da ake kira DEM, wacce jagoranta, Sanata Caleb Zagi ya jawo hankalina zuwa ga shiga siyasa. Duk da cewa a lokacin ban shiga cikin Jam’iyyar PDP gadan-gadan ba, amma wannan shi ne matakin farko. Tun daga nan kuma sai likafa ta yi ta ci gaba har zuwa lokacin da na zama Sakataren Kwamitin Shirye-Shiryen Karbar mulki na Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna a shekarar 2015. Sannan na zama Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna, na kuma zama Babban Mataimaki na Musamman (SSA) ga Gwamnan Jihar Kaduna kan Ayyuka na Musamman. Na kuma yi Shugaban Riko na Karamar Hukumar Jama’a har sau uku kuma yanzu na Karamar Hukumar Kaura a nan Jihar Kaduna.

Wadansu na ganin dukkan ayyukan da kake gudanarwa a Karamar Hukumar Kaura na da alaka da gina kanka a siyasance, me za ka ce?

Wannan shi ne matsalar mutane, musamman a fagen siyasa. Duk lokacin da ka yi yunkurin aikata kyawawan ayyuka sai su fassara su da siyasa. Ni kam zan ce ba haka ba ne. Ni fa dan rajin kare hakkin bil Adama ne tun ina makaranta. Ka san yawancin ’yan siyasarmu na Nahiyar Afirka sun mayar da siyasa wata kasuwa ce ta kudancewa. Siyasa ita ce ka tafi da kowa da kowa kan sha’anin mulki da wajen gudanar da ayyukan gwamnati domin talakawan nan da kake mulka suna da hakkin a sanar da su inda kudadensu ke zuwa. Kuma wadannan ayyukan da ka ga ina yi ina son haska wa wadanda za su biyo baya ne.

Me za ka ce kan yanayin siyasar Kudancin Kaduna?

A matakin farko dai zan ce ’yan siyasar ba ni na iya ne kawai suka shigo cikin siyasar Kudancin Kaduna aka bari suka zama masu fada-a-ji har suka kai ga nasarar canja akalar siyasar da kuma ma’anar dimokuradiyya ta hanyar raba kan jama’a don a ci gaba da mulkansu ta hanyar son zuciya. Amma game da zaben 2019 kuwa, gaskiya ce mun jefa siyasarmu cikin halin tsaka-mai-wuya saboda mun tattara dukkan karfinmu da kwayayenmu a kwando daya kuma ga shi kwandon ya fadi ya fashe, an bar mu muna ta bara a kufai, ba mu ga tsuntsu ba mu ga tarko.  Hakan ya faru ne sanadiyyar ayyukan wadansu ’yan siyasarmu na PDP da suke tunanin jam’iyyarsu za ta dore tana mulki har abada, kuma suna kallon Jam’iyyar APC a matsayin wata annoba da ta zo lahanta yankin. Abu daya da nake so mutane su gane musamman ’yan uwanmu a Kudancin Kaduna shi ne duk wani abu da dan Adam ya tsara, duk irin kyansa, sai an samu abin da ya fi shi wata rana ko kuma ya lalace kwata-kwata a bukaci canjawa da wani. Siyasa da jam’iyyun siyasa dukkansu kirkirar dan Adam ne don haka dukkansu na iya canjawa a kowane lokaci. Maganar Allah ce kawai tabbatacciya da ba ta canjawa.

’Yan siyasarmu sun cika mutane da karairayin cewa suna kokarin kwato musu ’yancinsu ne, wanda kuma ba haka ba ne. Babu wata bukata ta jama’arsu da suke karewa face son zuciyarsu kawai. Amma mutane sun riga sun fada komarsu, suna cikin dimuwa ko da sun ga gaskiyar ba sa gane ta. Ni ba zan canja ra’ayin wani bisa tilas ba, sai dai ina da gamsassun dalilai da suka sanya nake ganin ya kamata mutanen yankinmu su shiga cikin Jam’iyyar APC a dama da su.

Tunda kasar nan ta dawo siyasa tsawon shekara 16 muna yin jam’iyya daya ce kawai a Kudancin Kaduna kuma babu wani abu da jam’iyyar ta tsinana mana ta fuskar gine-gine da kayayyakin aiki ko kuma kyautata rayuwar mutanenmu. Ta ina suka bunkasa tattalin arzikin Kudancin Kaduna? Tunda na shigo ofis a matsayin shugaban riko a wannan karamar hukumar mutane ba su daina zuwa daga cikin gari da kauyuka don su nuna godiyarsu da irin ayyukan da suke gani ba.

Me za ka ce game da aikace-aikacen Kungiyar SOKAPU musamman bayan gudanar da zabukan sababbin shugabanni?

Ba kasafai na cika son yin magana kan SOKAPU ba. Amma gaskiya guda daya ce. Sanin kowa ne kowace kungiya a kan gina ta ce kan wasu kyawawan manufofi da ka’idoji kuma na tabbata kan irin haka ne magabatan SOKAPU suka assasa ta, irinsu marigayi Dokta Chris Abashiya da ayarinsa da suka kafa kungiyar wacce ta ginu a kan cicciba siyasa da tattalin arziki da kuma al’adun mutanen Kudancin Kaduna wacce kuma take tafiya da kowa da kowa ba tare da la’akari da kabilarsa ko addininsa ko jam’iyyar siyasar da yake yi ba. Kuma kan haka SOKAPU ta ci gaba da tafiya kafin zuwa wannan lokacin da abubuwa suka tabarbare saboda shigo da siyasar jam’iyya cikin tafiyar kungiyar ta yadda kuru-kuru suke nuna Jam’iyyar PDP ce kawai tasu.

Matsala ta biyu ita ce yadda hatta malaman addininmu ba sa taimakawa wajen magance wannan matsala domin su ma sun zama ’yan siyasa ne a fili sanye da rigunan addini. Har kwanan gobe ina jiran ganin SOKAPU da za ta mayar da hankalinta da kwanjinta wajen ganin ci gaban yankinmu da tallata kanmu a kasuwar duniya.