Da Dumi Dumi

Yadda muka kama mai kisan mata a otel – Kwamishinan ’Yan sanda

A ranar Juma’ar da ta gabata ce Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ribas, Malam Mustafa Dandaura ya tara manema labarai a ofishinsa don nuna musu kasurgumin dan ta’addar nan da ake zargi da kashe mata a otel-otek mai suna Greceous Dabid West. Ana zarginsa da yaudarar mata yana kaiwa otel daga bisani kuma bayan ya yi lalata da su, sai ya kashe su.                                                                                                                                                           

Kwamishinan ya bayyana wa manema labarai cewa ana zargin Dabid West ya kashe mata 11 ta irin wannan hanya.

Bayan ganawar da Kwamishinan ya yi da manema labaran, wakilin Aminiya ya tattauna da Kwamishinan don jin yadda aka yi jami’ansa suka yi kama wanda ake zargin:

Aminiya: Ranka ya dade kun yi nasarar kama wanda ake zargi makashin mata ne wato Greaceous West, wace dabara kuka yi kuka gano mutumin ganin cewa, yana wasan- buya da jami’anka?

Mustafa Dan Daura: Eh to kamar yadda na shaida muku a wancan bayanai da na yi ga manema labarai matakan da muka dauka su ne mun tilasta su masu otel-otel a nan su sa kyamarar da take daukar hoto, wadda idan mutum ya zo zai shiga otel za ta dauki hotonsa sannan idan ya shiga cikin otel din akwai wata a kofar shiga wadda idan za ka shiga daki nan ma an sa kyamara da za ta dauki hoto. Sannan muka ce musu kowa ya zo ya nuna katin shaida (ID Card) dinsa. Sannan ya bayar da lambar wayoyinsa kuma a tabbatar da lambar wayar da mutum ya bayar ita ce yake amfani da ita.

ADVERTISEMENT

To abin da ya faru shi ne daya daga cikin wannan otel din da suka dauki wannan matakai shi ne inda ya yi kisa na karshe. Ya kashe mace ta  9 a otel din an dauki hotonsa kuma sun ba mu wannan bidiyo na hoton kisan da ya yi suka dauka bayan mun je mun cire gawar da ya kashe a cikin daki, da suka ba mu bidiyon shi ne muka duba muka je kuma sa muka dudduba muka ga kamanninsa da ita yarinyar da ya tafi da ita mun ga fuskarta da komai kuma mun tabbatar da ita ce aka kashe lambar wayar da ya bayar ita ma muka yi amfani da ita, ita ce muka yi ta bi muna ta duddubawa har muka zo muka kama shi a hanyar East-West hanya ce ta zuwa Akwa Ibom

Aminiya: Kamar yadda ya yi muku bayani ko akwai hannun wadansu da suke sanya shi aikata haka kuma idan ya yi kisan mai yake yi da gawar ko yana cire sassan jiki?

Mustafa Dan Daura: Eh, shi ma wannan bayanin mun riga mun yi shi tun baya cewa, duk kisan da yake yi ba ya daukar komai a jikin gawa, bai cire komai a jikin mamatan. Saboda haka ba ya daukar komai don haka da muka kama shi sai muka ce to me ya sa ba ya daukar wani abu na jikin wadda ya kashe? Sai ya ce, shi abin da yake dauka kawai wayar salula na matar, idan tana da katin ATM (na cirar kudi) zai dauka da ’yan kudinta da suke cikin jakarta ya dauka. Sannan ya ce wa matar ba zai kashe ta ba, saboda haka ta ba shi  lambar sirrin katin. To sai bayan  an masa wadannan abubuwa ne sai yasa hannu ya makure ta ya kashe. Kuma mun tambaye shi wa yake sanya shi wannan abin ya ce, babu wanda yake sanya shi. Kawai abin yana zo masa ne haka kawai sai ya ji yana sha’awa ko yana so ya kashe mace kawai .

Aminiya: Yana wannan ta’addancin ne da taimakon wadansu ko shi kadai yake yi?

Mustafa Dan Daura: A bayanin da na yi maka yanzu kuma ya yi mana shi daya yake wannan abu. Mun tambaye shi su wane ne abokan wannan kisa. Ya ce mana shi daya ne kuma mun tabbatar shi dayan ne yake haka saboda duk inda ya je ya yi kisan a cikin otel shi kadai yake zuwa. Daga shi sai matar da ya dauko zai kashe. Mun tambaye shi me ya sa ne yake wannan kisan ko akwai abin da yake damunsa ko akwai abin da mata suka yi masa? Ya ce, a’a shi dai abin yana zo masa ne haka kawai sai ya ji abin kamar ya dan tabu haka, sai ya ga idan abin ya zo masa idan ba wannan kisan ya yi ba, ba ya samun kwanciyar hankali, kuma da ya yi kisan sai ya zo ya yi nadama. Sannan daga baya ya manta kuma ya koma. To ka ji bayanin da ya yi mana kuma mun gamsu da bayanin saboda mun bincika mun ga babu wani abokin da suke wadannan abubuwa tare kuma babu wanda ya ce yana taimaka masa yana yin wadannan abubuwa. Shi dai ya ce shi daya yake wannan abu kuma abin da ya yi mana bayani ke nan kuma ba nan Fatakwal ya yi wannan kisa ba ya  fara kisan ne a Legas ya kashe wata mata a Ikeja a wani otel sannan ya dawo Owerri a Jihar Imo ya kashe wata a otel sannan sai ya dawo nan Fatakwal ya ci gaba da abin da yake yi. Lokacin da muka kama shi a nan Fatakwal ne ya fi yawan kisa.

Aminiya: Mutum nawa ya kashe a nan Fatakwal?

Mustafa Dan Daura: Ya kashe tara a Fatakwal, ya kashe daya a Legas ya kashe daya a Owerri.

Aminiya: Wane hali wanda ake zargin yake ciki?

Mustafa Dan Daura: Yana nan muna tsare da shi ana ci gaba da yi masa tambayoyi da bincike kuma akwai abubuwan da muke so mu gano bayan wannan bayani da ya yi mana. Muna sa rai akwai ’yan kungiyarsa da suke sanya shi yana yin wadannan abubuwa kuma muna sa rai zai yi mana bayani kuma bai bayyana abokansa ba. Mun dauki lambar wayarsa muna nan muna ta bincike a kan lambar wayar mun ga mutanen da yake mu’amala da su yake yawan magana da su muna nan muna ta bi muna so mu gano idan yana da wata kungiya ce da suke yi kada mu dogara cewa shi daya ne yake aikata wadannan abubuwa mu bar wadansu kuma daga baya su zo su fara yi .

Aminiya: Idan kun gama yin binciken yaya za ku yi da shi?

Mustafa Dan Daura: Ah,  zai tafi  kotu mana. Kotu za a kai shi, kotu za ta yanke masa hukunci mun gama bincike, idan mun gamsu mun samu duk abin da muke bukata za mu gurfanar da shi gaban kotu kuma wannan ya rage wa su alkalai su je su yi aikinsu.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya