✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yadda muka sha daga gobarar Legas’

A ranar Lahadin da ta gabata ce mazauna Unguwar Abule Ado da ke yankin Festak a Karamar Hukumar Amuwo Odofin a Jihar Legas  suka wayi…

A ranar Lahadin da ta gabata ce mazauna Unguwar Abule Ado da ke yankin Festak a Karamar Hukumar Amuwo Odofin a Jihar Legas  suka wayi gari da karar fashewar wasu abubuwa wadanda suka yi sanadiyar tashin gobarar da ta salwantar rayukan akalla mutum 20 tare da lalata gidaje 50 tare da jawo asarar dimbin dukiya.

Jaridar Aminiya ta ziyarci yankin da lamarin ya faru ta kuma zanta da wadansu daga cikin mutanen da suka tsallake rijiya da baya a lokacin da gobarar ta tashi.

‘Motar dakon duwatsu ta haddasa gobarar’

Bello Muhammad Abubakar magini ne da ke zaune a yankin da gobarar ta tashi kuma a nan yake  harkokinsa na yau da kullum, ya shaida wa Aminiya cewa gobarar ta samo asali ne daga wata motar da ta kawo duwatsun yin fandashin na gini, “Ka san yanayin unguwar waje ne mai ruwa saboda haka idan za a yi gini sai an haka rami an yi kankare an cike  da manyan duwatsu. To a ranar da gobarar za ta tashi akwai wata babbar mota da ta kawo manyan duwatsu ta zo za ta sauke, to  akwai wani gare da aka yi idan irin wannan mota ta kawo kayan aiki sai an biya kudi kafin a bar ta ta shiga lungu.

Direban ya zo dab da wajen sai ya kuskure ya shiga wani kwazazzabo mai ruwa, to nan ya yi ta kokarin ya fita daga inda motar ta makale yana ta bai wa motar wuta amma tayar ta kafe. Sai direban ya ci gaba da kokari amma tayar tana ta juyawa motar ta ki gaba, hakan ne ya janyo wajen ya yi zafi sai wani farin hayaki ya fara fitowa daga wurin,” inji shi.

Ya ce, “Mutane da dama sun san wajen bututun mai ne a shimfide, lokacin da ba a yi gine-gine a wajen ba za ka iya ganin bututun man daga waje  domin ba a can karkashin kasa suke a binne ba. A wannan lokacin za ka ga wani zubin man fetur na malala a kasa, daga baya ne da gidaje suka yi yawa a wajen aka sanya kasa aka rufe su. Kuma aka sanya sojoji suke gadinsu domin akwai rumfar soji da aka gina a wajen saboda tsaron bututun, saboda a baya ana samun barayin mai da suke fasa bututun su diba su tayar da wuta.”

Ya ce, a lokacin da direban motar ya ga farin  hayakin na tashi sai ya yi maza ya fita, bayan kimanin minti 20 sai aka ji karar fashewar abubuwa. Mu muna daga nesa muna ganin abin da ke faruwa a haka kowa ya fara gudun tsira.”

Bello Muhammad ya ce gobarar ta yi barna sosai fiye da yadda ba a zato domin gidajen da suka lalace sun fi 50, “Gobarar ta rutsa da mutanenmu da dama masu sana’ar acaba da suka fito daga jihohin Yobe da Borno da Zamfara da sauransu. Akwai wani dattijo Malam Ali Bagobiri mutumin kasar Nijar ne  da ke aikin gadin makarantar ’yan mata ta Betelhem da ta kone, shi ma hadarin ya rutsa da shi ya rasu kuma har zuwa lokacin da muke maganar nan da kai ba a gano gawarsa ba,” inji shi.

Ya ce, “Ni kaina Allah ne Ya yi da sauran kwanana a gaba, saboda a lokacin da abin ya faru ji  na yi kamar an yi jifa da ni, ba ma mu mutane ba, hatta motoci haka za ka ga mota ta yi sama cikin iska.  Haka gilasai suka rika fado mana muna ta gudu muna addu’a har Allah Ya tsallakar da mu. Domin muna wajen da abin ya auku tazarar babu nisa sossai.”

Muhammad Bello ya ce zuwansa Legas irin haka ya faru a wannan wuri ba sau daya ba, ba sau biyu ba, sai dai a baya yakan faru ne a cikin daji nesa da inda gidajen jama’a suke, amma a wannan karo ya faru  ne a tsakiyar gidaje don haka lamarin ya yi muni sosai.

Ya ce baya ga  inda abin ya faru, lamarin ya ratsa har cikin Kasuwar Baje-Koli ta Kasa ya lalata gine-gine da dama a cikinta.

‘Mun rabu da mahaifina ke nan gobarar ta hallaka shi’

Shi kuwa Salisu Aliyu Adamu Bagobiri dan marigayi  Ali Bagobiri da gobarar ta rutsa da shi a Makarantar Betilham ya shaida wa Aminiya cewa shi da mahaifinsa ’yan asalin Jihar Damagaran ce a Jamhuriyyar Nijar. Ya ce mahaifinsa ya dade a yankin kuma yana aikin gadi ne a makarantar sakandaren da ta kone.

Ya ce a safiyar da lamarin zai faru sun yi sallama da mahaifinsa sai ya shiga makarantar, “A daki guda muke kwana da mahaifina, bayan da gari ya waye ya yi wanka ya tafi makarantar kamar yadda ya saba ni kuma sana’ar acaba nake yi, a daidai lokacin da lamarin ya faru na dauki fasinja, da na ga makarantar ta kama da wuta sai na kira lambar wayoyin mahaifina  amma ba su shiga ba.

“Nan take na kira mutanenmu da suke kusa da wajen su ma suka kira lambar wayarsa ba ta zuwa  da abin ya lafa mun bibiyi gawarwakin da aka fito da su amma shi ba ya cikinsu, mun je asibitoci inda aka rubuta sunayen wadanda suka rasu da wadanda suka jikkata nan ma ba mu ga sunansa ba. A baya akwai katafila da ke aikin zakulo wadanda suka mutu a buraguzan ginin yanzu an dakatar da aikin an kuma hana mutane zuwa wajen, yanzu dai mun bar wa Allah, ina sauraren abin da Allah Zai yi” inji shi.

Shi ma Sabi’u Muhammad mutumin Zamfara da ke aikin gini a inda gobarar ta auku ya shaida wa Aminiya cewa yana daki a kwance lokacin da lamarin ya auku, bayan ya aiki yaronsa ya debo masa ruwan wanka “Sai na jiyo ihun yaro yana salati yana istirja’i, ko da na fito na iske yaron a kwance rigarsa a kekkece sai na lura da wata irin iska ko guguwa mai gauraye da wuta nan na ciccibi yaron muka yi waje a guje Allah ne Ya yi da sauron kwananmu a gaba.  Ba don haka ba da tuni mun zamo labari, yanzu haka riga da wando da ka gani a gare ni su kadai na tsira su ne a jikina, ba mu tsira da komai ba. Kayanmu sun kone akwai akalla runfunan mutanenmu 40 da suka kone. Akwai kudaden adashin da masu acaba ke badawa ajiya akwai kudaden masu tireda duk sun kone, da yake mutanenmu ba sa ajiya a banki,” inji shi.

Aminiya ta zanta da jagoran ’yan Arewa mazauna yankin da gobarar ta auku, Sarkin Hausawan Kasuwar Baje-Koli ta Kasa da ke Legas Alhaji Musa Sake Ali inda ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Legas da ta tarayya su kai mUsu dauki. Ya kuma yi fata taimakon da za a yi wa wadanda suka gamu da bala’in ya kai ga ’yan Arewa da al’amarin ya rutsa da su.

Gobarar ta daga hankalin al’ummar Jihar Legas wadanda suka kasance cikin zullumi da fargaba. Jami’an  Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da sauran hukumomin da al’amarin ya shafa sun kai dauki lokacin da gobarar take ci, inda jagoran Hukumar NEMA a jihohin Kudu maso Yamma  Ibrahim Farinloye ya ce mutum 15 ne suka rasu yayin da gidaje sama da 50 suka lalace sai dai adadin mutanen da suka rasu ya karu zuwa 21 kwana daya da bada sanarwar hukumar ta farko.

Malama ta rasu wajen kokarin ceto dalibai

Wani lamari da ya dauki hankalin jama’a shi ne yadda wata malamar Makarantar Bethlehem mai suna Henrietta Alokha ta rasa ranta a gobarar lokacin da take  aikin ceto daliban makarantar.

Gwamnan Jihar Legas ya yi kira ga al’ummar jihar su kwantar da hankalinsu ya kuma bada tabbacin tallafa wa wadanda bala’in ya rutsa da su, ya kuma kai wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari hotunan gobarar don ganin abin da ya faru.