✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda muka shafe kwana 29 a hannun masu garkuwa da mutane – Abokan ango bakwai

Wadansu abokan ango su bakwai da masu garkuwa da mutane suka sace su a hanyarsu ta zuwa daurin auren abokinsu a garin Takum na Jihar…

Wadansu abokan ango su bakwai da masu garkuwa da mutane suka sace su a hanyarsu ta zuwa daurin auren abokinsu a garin Takum na Jihar Taraba wadanda suka fito daga garin Zariya an sako su bayan sun kwashe kwana 29 a hannunsu.

Lamarin ya auku ne a tsakanin kan iyakar Jihar Binuwai da Taraba, kamar yadda Aminiya ta samu labari. Lokacin da wakilinmu ya ziyarci gidan wadansu daga cikin abokan ango ya iske ’yan uwa da abokan arziki sun taru don nuna farin ciki da godiya ga Allah tare da taya su murna kubutowa daga hannun masu garkuwa da mutanen.

Daya daga cikin abokan angon da aka yi garkuwa da su mai suna Abubakar Muhammad Salisu wanda aka fi sani da Babangida Kofar Doka ya bayyana wa wakilinmu cewa: “A ranar 21 ga Disamban bara ne za mu je daurin aure sai kawai muka hadu da wadansu mutane bakwai dauke da manyan bindigogi sun tare hanya, inda suka kama mu suka shiga da mu cikin wani daji da sai da mukayi tafiya ta kusan awa uku a mota kafin mu kai wani dan daki a cikin dajin.Kafin nan sun daure mana idanu da wani bakin kyalle kuma suka daure mana hannuwa,  bayan mun sauka daga motar sai suka hada rigunanmu suka daddure suka jera mu, sannan suka yi mana bulala 12 kowannenmu, kuma suka kwace duk wani abu mai kyau da ke wurimu suka bar mu daga mu sai suwaita. Kuma sau daya suke ba mu abinci doya gasasshiya suke ba mu sau daya a kullum haka muka zauna a hannunsu.”

Ya kara da cewa: “Sallah ma idan za mu yi sai dai mu yi taimama domin ruwa ma sau daya suke ba mu kuma ga zagi da wulakanci iri-iri haka dai muka zauna, mu takwas a wani dan karamin daki domin mun samu wani mutum a cikin dakin kuma shi ya riga mu zuwa hannusu, sai dai da muke hira da shi ya ce mana shi mutumin Jihar Kogi ne. To a ranar Litinin 14 ga Disamban bara sai suka zo suka ce mana gobe za su sake mu domin mutanenmu sun biya abin da aka ce su biya. To washegari ranar Talata da misalin karfe uku na yamma sai suka zo suka yi mana albishir cewa za mu tafi gida. A wannan rana ta Litinin an ba mu abinci har sau uku kuma suka kawo mana naman bera gasasshe wai don girmamawa gare mu, ka ji yadda aka yi har sai da muka kwashe kwana 29 a hannunsu.”

Babangida Kofar Doka ya ci gaba da cewa, “Amma shi wanda muka tarar a dakin mu bar shi a can sai dai mun yi masa alkawarin cewa in Allah Ya yarda za mu yi iya kokarinmu mu ga cewa mun fito da shi ta hanyar biyan kudin da suka sara masa.

Aminiya ta ji ta bakin daya daga cikin iyayen abokan angon mai suna Khadi Aliyu Abdurrahman, inda ya ce, “Muna wa Allah godiya da Ya amsa mana rokommu tare da biya mana bukata Ya kwato mana ’ya’yammu daga hannun wadannan miyagum mutane. Bayan mun samu labarin abin da ya faru sai muka sanar da jama’a a taya mu rokon Allah, kuma ganin cewa dukammu ’ya’ya ne na Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, sai muka sanar da shi ga abin da yake faruwa. Nan da nan ya daga waya ya kira Janar T.Y. Danjuma kuma na jin abin da ya fada masa cewa an kama ’ya’yansa a Jihar Taraba a kan hanyarsu ta zuwa daurin aure har su bakwai. Sai Janar Danjuma ya yi wa Sarki jaje kuma ya ce zai sanar da Gwamna domin a dauki mataki. Kuma Allah Ya sa aka sako su bayan sun kwashe kwana 29 a hannunsu don haka muna godiya ga babbammu Mai martaba tare da sauran ’yan uwa da suka taya mu da addu’o’i.”