✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda muka shafe kwana 8 a hannun masu garkuwa da mutane – Dan jarida

A ranar 7 ga Maris din nan ne, (7-3-19) daya daga cikin ma’aikatanmu Ahmed Garba Mohammed ya fada hannun masu garkuwa da mutane shi da…

A ranar 7 ga Maris din nan ne, (7-3-19) daya daga cikin ma’aikatanmu Ahmed Garba Mohammed ya fada hannun masu garkuwa da mutane shi da wadansu fasinjojin wata mota da suka nufi Kaduna daga Abuja. An sace su ne bayan sun gota kauyen Rijana kadan. Wakilinmu ya tattauna da shi inda ya yi bayani dalla-dalla kan yadda suka shafe kwana 8 a hannun masu garkuwa da mutanen da irin taskun da suka shiga:

Yaya aka yi ka tsinci kanka a hannun masu garkuwa da mutane?

A ranar Alhamis 7 Maris, 2019 bayan na baro Abuja da nufin in kwana a Kaduna domin a duk ranar Juma’a nakan ziyarci likatana saboda rashin lafiyar da nake fama da shi. Mun yi sallama da editana da misalin karfe 2:00 na isa Zuba inda na shiga mota da misalin karfe 3:00 na rana tare da wani abokina wanda zuwanmu aka ce dama mutum biyu ake jira.

Direban motarmu wanda daga baya na fahimci soja ne zai wuce Zariya ne sai ya dauki fasinja domin ya samu na mai. Da muka isa Jere sai ya ce zai sayi balangu, sai na ce ni fa idan ina tafiya ban cika son tsaye- tsaye a hanya ba. Ya ce mu yi hakuri ya sayi naman, har ya ce da mai naman ya dan yanka mana mu dandana. A cikin notar mun kai mu 11 kuma mutum biyar daga ciki sun sayi naman.

Bayan mun ci gaba da tafiya kuma sai ya sake tsayawa ya ce wai zai sayi itace sai na ce da shi haba yamma fa na yi domin tafiyar da ba ta wuce sa’a daya da rabi ba, ga shi muna neman sa’o’i uku saboda yawan tsaye-tsaye da yake yi. Ina ta yi masa kashedi cewa hanyar ba ta da kyau domin ba na son mu yi Magariba a hanya. Shi kuma sai cewa yake da ni maigida babu damuwa ni kuma na ce Allah Ya sa.

Da muka iso Rijana sai daya daga cikin fasinjojin, ya ce shi zai sauka a Rijana, lokacin kusan karfe 7:00 na yamma. Yana sauke wannan fasinjan mu da direban ba mu lura cewa motoci sun daina wucewa ba, wanda hakan ke nuna akwai matsala.  Ba mu kai kilomita daya ba daga Rijana zuwa wajen wata gada, mun shawo gangara ke nan sai muka fara jin karar harbi, akwai motoci biyu a gabanmu tamu ce ta uku. Da muka iso sai motocin biyu suka tsaya, mu ma muka tsaya tare da kashe wutar motar. Bayan sun yi barin wuta na kusan minti biyu sai wurin ya yi sit, sannan ga duhu ba a jin wani motsi. Nan take sai daya daga cikin fasinjojin motarmu ya ce me zai hana direbanmu ya yi ribas ko Allah zai ba mu dama mu tsira. Sai direban ya karbi shawararsa ya kunna motar ya koma da baya, sai suka biyo mu a guje, yana cikin komawa da baya sai motar ta fada rami. Ganin haka sai direbanmu ya fita da gudu ya tunkuri daya daga cikin ’yan fashin da nufin ya karbe bindigarsa. Amma saboda suna da yawa sai suka taru masa suka harbe shi. Ganin haka na fito daga motar da nufin in gudu cikin daji ashe wani ya biyo ni a guje, sai na ji saukar kokara a kaina. Da na fadi sai ya ce ina wayar hannuna sai na mika masa. A cikin motar mutum daya ne kawai ya tsira shi din ma ban san yadda aka yi ya tsira ba, sai bayan an tattara mu ne ban gan shi ba. Na dauka sun kashe shi ne, amma daga baya na samu labarin ya tsira.

Direbanmu da suka harbe shi sai suka ja shi cikin daji da nufin su tafi da mu baki daya, amma saboda ba zai iya tafiya ba yana wayyo -wayyo su ba shi ruwa ya sha, sai suka ce mu yi kama-kama mu tafi da shi amma abu ya gagara.

Suka ce ya tashi tsaye ya ce ba zai iya ba, suka kara cewa ya tashi ya ki sai kawai suka bude masa wuta suka kashe shi muna gani. Daga nan suka tasa mu cikin daji tun misalin karfe 8:00 na dare ba mu muka tsaya ba sai wurin karfe 12:00 na dare. Muna tafiya suna bugunmu, babu takalma a kafafunmu ga kayoyi amma babu ruwansu sai haska mana hanya kurum suke yi. Mu haura kwari mu shiga rafi haka muka rika tafiya har muka kai inda suke so.

A cikinmumu bakwai maza ne mace daya wata budurwa mai kimanin shekara 22, wadda ta ce ita ’yar wajen Sabon Tasha ne. Da muka isa wani waje sai suka kira ’yan uwansu a babura kusan 10 suka rika dibar mu bibbiyu da mai bindiga a baya suka kwashe mu.

Gida suka kai ku a dajin?

A’a babu gida ko gari ko daya, kunkurmin daji ne kawai. Daga bakin titi inda suka kama mu a kiyasin da na yi mun yi tafiyar kusan kilomita 40 a daji. Bayan mun isa inda za su a jiye mu sai suka yi harbi a sama, sai muka ji wadansu sun yi harbi daga nesa alamar an kawo mu ke nan. Can sai suka bude wata ciyawa da ke kewaye da wani dutse aka ce mu shiga. Muna shiga sai muka tarar da wadansu matasa su 8 ko 11, wadanda aka yi garkuwa da su. Ranar da aka kawo mu sun yi kwana uku a wajen. An ce daga Zangon Daura Jihar Katsina suke kuma ’yan ga-ruwa ne da suke hanyarsu ta komawa gida. Muna shiga wajen sai shugaban masu garkuwa da mutanen ya umarce su da su tashi tunda an yi baki.

Bayan sun tashi sai muka kalli juna mu da su, daga nan sai ya ce da su, su je su kwanta, bayan sun kwanta sai shugaban ya zo inda muke zaune ya gaishe mu sannan ya fara shaida mana ka’idojinsu a wajen.

Wadanne ka’idoji ke nan?

Daga ciki shi ne sun kamo mu ne saboda su samu kudi, na biyu kuma duk wanda yake son ransa kada ya nemi ya gudu ko ya yi wata hayaniya. Ya ce ko kwana nawa mutum zai yi a wajen muddin ya bi ka’idojinsu zai koma gida lafiya. Kuma ya nuna ladabi da biyayya abin da aka ce, ya yi kawai babu gardama, ya ce idan suka kama mutum yana kokarin gudu ko ya boye wani abin daukar magana a jikinsa to, kashinsa ya bushe. Ya kara da cewa ko a cikinmu akwai wanda bai san direbanmu an kashe shi ba?

Muka ce mun sani. Sai ya ce to, akwai wadansu da za a kashe domin daga cikin daya motar da aka tsare mu tare wanda aka ce sun fito ne daga Jihar Ondo an kashe direban motarsu.

Sai dai wancan direban ba a can aka kashe shi ba domin a kafa suka harbe shi suka dauko shi a kan babur har cikin dajin daga bisani ya rasu. Amma kafin ya rasu yana ta ihu yana cewa su ba shi ruwan sha amma suka ki domin a cewarsu ko sun ba shi ruwan ma mutuwa zai yi. Da gari ya waye bayan su ga takardar shaidar aikina a jikina da ta nuna musu cewa ni dan jarida ne sai hankalinsu ya komo kaina.

Ke nan akwai masu ilimin boko a cikinsu?

Eh, akwai wanda suka iya karatu cikinsu. Sun kuma caje mu tas domin babu inda ba su duba ba a jikinmu, daga sama har kasa.

Wadanne irin mutane ne?

Fulani ne matasa ’yan shekara 20 zuwa 25, babbansu ne kawai dan kimanin 30, suna ce masa Kwamanda. Sannan akwai wanda suke yi wa inkiya da Sa-Wuta-A-Biya-Ka. Da sun ce da shi sa wuta zai dauki bindiga ya yi ta harbi a sama tatata-tatata har ya saba mana da jin karar bindiga. Kuma duk suna sanye ne da kayan sojoji har da hula. Daga nan suka bukaci ni dan jarida in je in taba gawar wanda suka kashe, haka suka umarce mu daya bayan daya. Sai suka tambaye mu abin da muka ji, muka ce sanyi. Sai shugabansu ya ce, to, duk wanda ya nemi yin taurin kai shi ma zai mutu kamar wannan. Sai aka bai wa wadansu matasa daga cikinmu cebur su je su haka rami a kusa da wata fadama su binne gawar domin kada ta dame su da wari.

Babu Sallar Gawa?

Ina ruwansu da wata Sallar Gawa? Ai ba su Sallah ma balle ta gawa.

Yaya yanayin zaman wajen da kuka yi yake?

A nan muke zama da su a tsandaurin kasa. Sai dai mu dan yanko ganye wanda zai zama mana kamar katifa da filo mu shimfida. Kayan jikinka da su za ka yi ta rayuwa, idan singileti ce a jikinka haka za ka zauna a dajin babu ruwansu. Muna kwantawa za su kwanta suna zagaye da mu, wadansu kuma ba su kwanciya suna tsaye.

Yaya kuke yin Sallah?

Akwai wani dattijo mai kimanin shekara 60 a cikinmu shi yake yi mana limanci idan lokacin Sallah ya yi. Suna bari muna Sallah sai dai su ba su yi. Idan mun kammala Sallah sai mu yi addu’o’inmu a asirce. Nan za mu zauna har rana ta dago sannan su dora abinci, wato shinkafa zalla wani lokaci kuma shinkafa da wake. Sai a dan zuba manja kawai domin ta dan canja launi amma ba don ta yi dadi ba. Sun kai sama da mutum 20, idan sun debi nasu abincin sai su zubo mana namu a leda kamar awaki mu hadu mu ci. Ita kuma macen tana gefe an zuba mata tata ita kadai. Ko wajen kwanciya ita tana gefe ne ba tare ake hada mu ba.

Ba su yi mata wani abu na cin mutunci ba?

A’a gaskiya ba su yi mata komai ba, domin a gabanmu shugabansu ya gargade su cewa duk wanda ya nemi yi mata wani abu zai kashe shi. Ya ce dokarsa a wannan waje bai taba lalata da wata mace ba, kuma ba zai yarda wani ya yi ba. Ya ce matsalarsa kudi ne don haka idan ya samu labarin wani daga cikinsu ya yi lalata da ita ya rantse da Allah sai ya kashe shi. Kuma suna jin mugun tsoronsa, don haka har muka yi kwana takwas din nan babu wanda ya taba ta. Sai dai kawai su tsokane ta su ce suna sonta amma ba su taba ta ba. Haka muka yi rayuwa a wajen idan rana ya fito mu tashi mu koma inuwa. Kuma hada salloli muke yi wato Azahar da La’asar da Magariba da Isha’i. Da mun ci abinci bayan Sallar Isha’i sai su ce kowa ya kwanta ko kana jin barci ko ba ka ji.

Babu batun hira ke nan?

Ina Babu hira sai dai mu rika jin su suna hira tare da yin ihu cikin Fulatanci, amma idan za su yi magana da mu Hausa suke yi. A cikinnu akwai wanda ke jin Fulatanci amma ba su sani ba. Da yake ina kusa da shi yakan dan kyankyasa min abin da suke cewa. A kwana uku na farko da muka yi ba su yi mana komai ba, har sai da suka sallami matasan da muka fara gani bayan an biya kudin fansarsu sun tafi. Sun yi musu kudin goro Naira miliyan daya, sai Naira dubu 50 da suka ce a sayo musu katin waya saboda sun fahimci ba su da kudi.

Daga nan sai aka canja mana wajen zama zuwa kusa da wani kogi domin a zagaye muke da kogi babu yadda za ka yi ka gudu domin ba ka ma san ta inda aka biyo ba tunda da daddare aka kawo mu wajen. Kuma a saman kogin akwai wadansu da ke gadinmu. Ba na kuma tsammanin jami’an tsaro za su iya shiga cikin wannan daji har su yi nisan tafiya zuwa wajen da mutanen suke. Idan kuma an je gaskiya za a rasa rayukan wadanda aka kama aka yi garkuwa da su.

Bayan wadancan matasa sun tafi sai muka fara ganin tasku, daga lokacin ne suka fara zagi da dukanmu domin a cewarsu ba su kawo mu domin su ciyar da mu ba. Har suna cewa wai iyayenmu ko ’yan uwanmu ba su kaunarmu tunda ga shi cikin kwana uku babu wanda ya kira ya nemi a sake mu. A cewarsu, ba sa wuce kwana uku suke ajiye mutum. Ko dai su saki mutum idan an biya kudin fansarsa ko su kashe mutum. Ga shi mu har mun kai kwana hudu zuwa biyar babu labari. Muka ba su hakuri daga nan sai aka sanya farashi a kanmu.

Ni dai farashin Naira miliyan 30 shugaban ya dora a kaina, ya ce saboda ni dan jarida ne kuma mu muke haddasa rigima a kasa sannan wai muke sa gwamnati tana kai musu hari a daji. Wai mu ke sa a kashe su domin abin da ba su yi ba sai mu ce sun yi. Wai mu ke sa da an ga Fulani a buge shi kamar kurege sannan wai dama ba su taba kama wani dan jarida a dajin ba, don haka suka sa ido a kaina. Ya ce shi ya sa ya yi min farashin Naira miliyan 30. Ni kuma sai na ce da shi ai ko gunduwa- gunduwa zai yi da namana babu yadda zan yi a samu Naira miliyan 30. Ya ce haka na ce, na ce ni ba na ce ka yi gunduwa- gunduwa da ni ba ne, amma dai ina fada maka gaskiyar magana ce.

Daga baya ya rage zuwa Naira miliyan 15 duk wannan tattaunawa ba da ni yake yi ba, da gida yake yi sai in ta kama ne zai ba ni wayar in yi magana. Daga baya ya dawo Naira miliyan biyar kai da suka lura babu kudin sai suka sake fito da mu suka ce sun lura gaskiya ba mu da kudi, don haka kowa ya fadi abin da yake ganin zai iya bayarwa. Da aka zo kaina na ce zan iya bayar da Naira dubu 500, sai ya ce bai yarda ba. Suka ce sun yanke min Naira miliyan biyu. A cikinmu akwai wanda aka ce zai biya Naira miliyan daya, akwai wadanda aka hada su su biya Naira miliyan daya da rabi akwai masu Naira dubu 300.

Wato naka kudin fansar ya fi yawa saboda aikinka?

Eh, ni nawa kudin ne mai yawa saboda ni dan jarida ne, ya kuma ba mu zuwa ranar Alhamis din makon jiya mu tabbatar an kawo kudi kuma zai kashe mu in har ranar Alhamis babu wanda aka kawo kudinsa. Hankalinmu ya tashi domin ni na dauka duk sun kammala magana da gida. Daga bisani sun rage Naira dubu 500 daga cikin Naira miliyan biyu da suka dora min wai saboda mahaifiyata ta kira tana yi musu kuka. Har suka tambaye ni cewa ashe ina da mahaifiya na ce eh. Su ma sauran an kawo kudinsu amma ba duka ba, domin mai Naira miliyan daya an samu dubu 500, masu Naira miliyan daya da rabi Naira dubu 600 aka bayar kuma duk sun karba. To, ni sai aka ce an samu miliyan daya a kasa amma ba su kira ba saboda miliyan daya da rabi ake nema a kaina.

Da shugaban ya zo ya ce an biya kudin mutum shida don haka ni dan jarida da wani yaro daga Kudan ne ba a kawo namu kudin fansar ba, don haka ya ce idan a gobe Juma’a ba a kawo kudinmu da misalin karfe 9:00 na safe ba, ya rantse zai kashe mu.

A nan ne na roke shi ya ba ni wayar in kira gida inji abin da ake ciki. Sai ya ce abu ne mai saukin yi su da suke neman kudi. Da ya ba ni na kira lambar abokina da ke hada kudin sai ya ce ai Naira miliyan daya suka hada. A lokacin da muke wayar sai wani ya kira shugaban hankalinsa ya dan gusa daga kaina. Ganin haka sai na shaida wa abokin nawa cewa su kawo Naira miliyan dayar da ke hannunsu.

Ko da shugaban nasu ya dawo sai ya ce yaya ya ga na kashe wayar? Sai na fada masa cewa Naira miliyan daya suka samu. Ya ce na tabbata kudin ya cika Naira miliyan daya? Na ce eh. Ya kara cewa idan ba su cika Naira miliyan dayan ba zai kashe ni.

Da gari waye bai zo ba sai da misalin karfe 10:00 na safe, ya zo ya ce da ni dan jarida ina yi muku murna, an kawo kudadenku kuma sun cika don haka za ku tafi gida.

Da muka tashi tafiya sai suka raba mana Naira dubu daya da dari biyar kowanenmu wai kudin mota. Wajen su bakwai suka rako mu daga dajin suka nuna mana wata hanya suka ce mu ci gaba da tafiya har mu fita daga dajin. Ga shi dukanmu babu takalma, kafafunmu kuma duk sun kumbura.  Ita ma yarinyar har da ita aka sako domin ita ba ta da waya ballantana a kira gidansu a nemi kudin fansa, saboda haka sai suka hado mu da ita muka tafi. Sun dai taimaka mata amma fa ita duk jikinta ya kumbura saboda cizon sauro da sauransu. Da suka kai wani waje sai suka ce za su koma amma mu ci gaba da tafiya za mu ga hanyar da za ta kai mu Rijana.  To, tun karfe 10 na safe da muka fara tafiya har karfe 2:00 na rana ba mu kai garin Rijana ba. Ga shi ba ni da lafiya har ta kai abokan tafiya ke goyona a baya, haka muka yi ta tafiya a cikin daji. Har muka hango wadansu Fulani dattawa a kan babur, suka tsaya suka tambaye mu yadda aka yi muke tafiya a daji ba ko takalma. Muka fada musu abin da ya faru, sai suka ce wane taimako muke so? Sai abokan tafiyata suka ce su taimaka su dauke ni a babur domin ni ne ba ni da lafiya. Suka dauke ni a babur har inda zan shiga mota. A kan babur din ma sai da muka yi tafiyar kusan awa daya a cikin daji kafin muka shiga gari. A Rijana na sayi takalmi aka taimaka min na samu motar da ta kawo ni Kaduna.

Mene ne sakonka ga wadanda suka taimaka Allah Ya sa ka dawo gida lafiya?

Ina godiya ga Allah da kuma iyayena da ’yan uwa da abokan arziki da Kamfanin Media Trust kan irin taimakon da suka ba ni da duk wadanda suka rika yin addu’o’i a masallatai. Kuma a ci gaba da yin addu’a Allah Ya kare mu daga shairrin irin mutanen nan. Domin akwai wanda ya fada min daga cikin masu garkuwa da mutanen cewa wai ba a son ransa yake yi ba, domin shi daga Jihar Zamfara yake kuma wai an kashe masa iyaye da sauran ’yan uwa, don haka shi kadai yake rayuwa a yanzu. Sannan su a yanzu suna daukar garkuwa da mutane a matsayin wata sana’a ce, doan haka suna bukatar addu’ar Allah Ya shirye su su bari. Sun kuma kara yin gargadi a kan bin hanyar Abuja zuwa Kaduna inda suka nemi mu yi taka-tsantsan da bin hanyar tare da yin Addu’ar Allah Ya shirye su su daina. Ya ce da Musulmi suna yi musu addu’ar shiriya kila da Allah Ya sa sun daina maimakon tsine musu da ake yi.