✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda muka tsira daga masu garkuwa bayan kwana 10 a tsare – Dokta Adamu Chonoko

Dokta Adamu Chonoko Malami ne a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da kanensa Dokta Umar Chonoko da ke koyarwa a Kwalejin Kimiyya da Sana’a…

Dokta Adamu Chonoko Malami ne a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da kanensa Dokta Umar Chonoko da ke koyarwa a Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Kaduna, sun samu kubuta daga masu garkuwa da mutane bayan sun kama shi kanen nasa kuma ya kai kudin fansa.  Ya bayyana wa Aminiya yadda aka sace shi a gidansa da yadda suka samu gudowa daga dajin bayan kwana goma:

Yaushe aka sace ka aka yi garkuwa da kai?

Al’amarin ya faru ne ranar wata Alhamis da misalin karfe 2:30 na dare,  lokacin ina cikin daki ina barci sai na ji motsi. Da na farka sai na ji dakin da ke gabana ana ta motsi, wanda hakan ya sa nake tunanin ko miji da mata ne ke fada. Duk da yake na san mijin ba ya nan amma a tunanina ko ya dawo da dare ne amma suke fada.

Sai na fito daga dakina domin ganin abin da ke faruwa sai kurum na ga wadansu matasan Fulani rike da bindigogi a tsakar gida, wadansu kuma na rike da wukake. Da suka gan ni sai na daga hannayena sai suka tambaye ni ko ina da kudi? Na ce eh, domin akwai wasu ’yan kudi a cikin dakina, sai suka bi ni dakin. Duk suka bincika na fito musu da kudin, suka karbe wayoyina sannan suka kwashe wasu abubuwa a cikin dakin.

Babbansu ya umarce ni da in saka riga in bi su, sai na tambaye shi ina za mu je bayan na sanya rigar? Sai ya ce da ni kada in sake yi masa tambaya. Daga nan sai na yi shiru, amma sai na bukaci su bari in rufe dakina, sai suka amince min in yi hakan. Tun daga nan muka fara tafiya wato kusan misalin karfe 2:30 ba mu tsaya ba sai kusan karfe 4:00 na asubahi.

Daga nan sai me ya faru?

Haka muka ci gaba da tafiya cikin dare har muka kai lokacin da suka fito da baburansu. Nan ma muka fara wata sabuwar tafiya amma a kan babura kusan sa’o’i biyu. Daga nan suka ce mu sauko daga kan baburan domin za a rufe mana idanu, saboda mun yi kusan kai inda za a ajiye mu.

Daga nan ne suka rufe mana idanu muka ci gaba da tafiya. Bayan mun kai maboyarsu sai suka fada min cewa sun dade suna nemana, domin wani ya fada musu cewa idan suka same ni zan iya ba su Naira miliyan 50. Na yi mamakin jin cewa wani da ya san ni ne ya fada musu haka. Ni kuma sai na ce masu ta ina wadannan kudi za su fito, tunda na san ba ni da su? Muka ci gaba da tattaunawa domin sun bukaci Naira miliyan hamsin daga wajena, har muka tsaya a kan Naira miliyan biyu da dubu dari hudu.

Suna son a ba su Naira miliyan biyu zunzurutu sannan Naira duba 360 a saya musu babura sannan sauran dubu 40 kuma na zirga-zirga. ’Yan uwana sun binciki irin baburan da suke nema ba a samu ba har sai da aka je Zariya sannan aka samu. Shi kuma kanena wanda ya kai musu kudin sai suka rike shi, shi ma tare da bukatar sai an kara musu kudi. Sai na tambaye su wai me suke bukata ne? Suka ce wai wani ya ba su labarin wai yana shirin aiko musu da Naira miliyan goma a matsayin kudin fansa, ni kuma nake tambayarsu wane ne wannan mutumin? Saboda ni dai na san babu wanda suke magana da shi in ba kanena Umar ba.

Dalilin rike kanenka Dokta Umar ke nan?

Eh, wannan shi ne dalilin rike shi ke nan, domin suna zaton cewa shi ya yi masu wannan alkawari. Da na ji haka kuma sai aka fara sabuwar tattaunawa. Sai muka sake tsayawa a kan Naira miliyan uku. Muka sake neman Naira miliyan uku aka ba su. Kudi suka zama Naira miliyan biyar da dubu 400. Da aka ba su kudin sai na dauka za su sallame mu daga nan, sai muka fahimci kamar akwai yaudara a cikin lamarinsu saboda sai su ce za su sallame mu yau amma washegari ba za su zo ba.

Kwana biyu da suka wuce sai na sake tambayarsu cewa wai me ke faruwa ne ko dai ba su da niyyar sallamarmu ne? Sai suka ce wai sun fahimci ’yan jarida sun yada labarin kuma wai inda nake aiki yana da maiko, wato Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) sannan wai ina da alaka da Gwamnan Jihar Kebbi da Gwamna El-Rufa’i. Sannan wai a cewarsu, suna kokarin nemo kudi domin su biya fansa a sako ni.

Daga nan ne muka fahimci ba su da niyyar sakinmu, don mun fahimci suna ganinmu ne a matsayin saniyar tatsa, wato za su rika tatsar mu ne har zuwa lokacin da suka tatse mu baki daya.

Wannan ne ya sa kuka yanke shawarar gudu?

Eh, domin tunda muka fahimci kamar ba su da wannan niyya sai muka yanke wannan shawara. Sannan da taimakon Allah da addu’o’in da ake yi mana har Allah Ya kubutar da mu. Mun fice daga cikin dajin ne tunda dare misalin karfe 11:30, muka yi ta tafiya har zuwa wayewar gari, karfe kusan 11:51 na safe.

Ko suna barinku ku yi Sallah?

Suna bari mu yi Sallah amma fa sai ka tambaye su amma su ba su yin Sallah.

Yaya batun abinci fa?

Suna ba mu abinci da suke dafawa wasu lokuta amma fa babu mata a wajen, su ke yin komai cikin dajin. Koda suka fara kai ni can dajin, na tarar da wani mutum daya da suka rufe wa idanu sannan suka daure shi da bishiya. Da muka zo sai suka karo mutum biyu duk tsofaffi. Daya tsohon ma ya je gonarsa ce domin duba shuka suka kama shi. Mutanen da ganinsu ka san ba su da kudi amma sun kamo suna bukatar wasu makudan kudi.

Ke nan kun baro su a can?

Gaskiya dai kam, domin sulalewa muka yi da tsakar dare muka tafi abinmu, lokacin masu gadin namu suna barci. Haka muka shiga daji muna tafiya ba tare da sanin inda za mu ba cikin duhu. Kai ban taba ganin tashin hankali irin wannan ba tunda nake. Domin tafiya muke yi har sai da gari ya waye har Allah Ya sa muka fito bakin titi. Akwai wani kauye da muka tarar, na tambaye su suka ce ai gari na gabanmu shi ne Buruku. Daga can ne muka samu wadanda suka dauko mu a babura zuwa Kaduna.

Wace rawa Jami’ar Ahmadu Bello ko jami’an tsaro suka taka wajen fito da kai daga hannun masu garkuwar?

Gaskiya a can Jami’ar Ahmadu Bello yanzu na dan je hutun sa-kai da ake nema wato sacondment domin aiwatar da wani aiki a nan Kaduna. Amma duk da haka sun taimaka mini matuka, musamman ta bangaren tara kudin fansa. Amma ga su jami’an tsaro ba ni da masaniya, tunda ina tsare a lokacin.