✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda muke amfani da cibiyarmu wajen samar da zaman lafiya – Zack Amata

Zack Amata shi ne shugaban Cibiyar Kawo Canji da Bunkasa Ci gaban Al’umma (Centre for Change and Community Debelopment- CCCD) kuma tsohon jarumi ne da…

Zack Amata shi ne shugaban Cibiyar Kawo Canji da Bunkasa Ci gaban Al’umma (Centre for Change and Community Debelopment- CCCD) kuma tsohon jarumi ne da ya yi fice a shirya fina-finai. A zantawarsa da Aminiya ya bayyana yadda suke amfani da cibiyarsu wajen wayar da kan matasa musamman mata wajen ilimi da kuma samar da zaman lafiya a Arewa

Wane ne Zack Amata?

Ni dalibi ne, dalibi ne na rayuwa. Ina matukar son in ga ina koyo, ina yin nazari da bincike sosai. Nakan yi kokari in yi bincike game abubuwa da suka shafi rayuwa ta yau da kullum. Wannan haka yake, kuma ina ganin wannan shi ne muhimmin abu da zan ce game da ni a halin yanzu.

Kana sahun farko na wadanda suka fara harkar fina-finai a Nollywood, me hakan ya haifar zuwa yanzu?

Ba na cikin wadanda suka fara kafa Nollywood amma dai ina tsammanin ina sahun gaba na wadanda suka fara shirya fina-finai da wasannin kwaikwayo a gidajen talabijin. Amma Nollywood ina ganin matasan Ibo ne suka  assasata. Amma mu mun yi aiki ne da gidan talabijin na NTA, na fito a wasannin kwaikwayo da fina-finai da dama.

Masoyanka sun dade ba su ga ka fito a fim ba, me ya faru?

Har yanzu ina fitowa a wasu fina-finai, sai dai kawai yanzu na fi mayar da hankali ne wajen daukar nauyi da kuma gabatar da fina-finai masu koyar da jama’a da kara musu kwarin gwiwa da wayar da kansu a kan wasu muhimman abubuwa. A halin yanzu haka aikin da nake shi ne yin amfani da fim don wayar da kan mutane kan muhimmancin zaman lafiya a Najeriya.

Da yake kai ne Shugaban Kwamitin Amintattu na Kungiyar CCCD, ko za ka yi mana karin haske game da kungiyar?

Haka ne, a nan Centre for Change and Community Debelopment muna yin fim don wayar da kan jama’a game da muhimmancin zama lafiya da kuma yaki da talauci da jahilci. Idan ka buda Littafin Baibul a cikin Ishaya sura ta 4 aya ta shida ta ce “Jama’ata suna hallaka ne saboda jahilci.” Haka kuma idan ka je cikin Hadisi za ka ga Annabi Muhammadu (Tsira da Aminci su tabbata a gare shi) yana cewa, “Ku je ku nemi ilimi ko da kuwa za ku yi tafiya mai nisa zuwa China ne.” Don haka ne mu a nan muke amfani da fim don wayar da kan jama’a su tashi su nemi ilimi. Wannan shi ne a takaice game da wannan kungiya.

Ko za ka fada mana wasu daga nasarorin da kungiyar taku ta samu kawo yanzu?

Haka ne, Centre for Change ta yi aiki da Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da ba da tallafi. Mun yi wa UNICEF fim amma da farko mun fara ne da yin hadin gwiwa da UNICEF din inda muka shirya taro na horarwa. Wannan horarwar an yi ta ce a kan wayar da kan jama’a su san mene ce HIB wato cutar kanjamau. Daga bisani kuma mun samu wani dan dauki daga Gidauniyar Mark Arthur. Gidauniyar ta Mark Arthur ba ta jin dadin yadda ilimin mata yake a Arewacin Najeriya. Mu kuma sai muka fada musu cewa za mu iya zuwa sako-sako mu wayar da kan mutane game da muhimmacin ilimantar da ’ya mace. Don haka sai suka ba mu kudi kuma muka yi wani fim mai suna ‘ZABINA’. Mun kuma nuna wannan fim din a jihohi uku, wato jihohin Kaduna da Kano da kuma Sakkwato.

A Jihar Kano mun nuna shi a kananan hukumomi biyu, wato  Gezawa da Ajingi. Sannan mun nuna shi a otal din Tahir a cikin birnin Kano. A Kaduna kuwa mun nuna shi a garuruwa 11. Mun je Turunku, mun je Giwa mun je Fambeguwa, mun je Soba da Kudan da Makarfi da Ikara da Dutsen-Abba. Haka nan mun je Fan-madina da Kafin-Magami da Kwada. Sannan matasa suna koyon abubuwa da dama daga fim din. Misali a Dutsen-Abba bayan mun nuna musu fim din washegari wadansu ’yan mata masu talla suka taru suka je suka samu iyayensu suka fada musu cewa su fa ba za su kara zuwa talla ba. Iyayen yaran suka je suka fada wa hakimi abin da ’ya’yansu suka ce. Wato ba za su kara zuwa talla ba. A take hakimi ya sanya aka kira masa yaran kuma ya tambaye su saboda mene ne kuka  ce ba za su kara zuwa talla ba? Suka ba shi amsa cewa saboda sun kalli fim din ZABINA kuma a cikinsa sun ga wata yarinya mai suna Mariya ta bar zuwa makaranta aka yi mata aure daga bisani ta kamu da ciwon yoyon fitsari. Sannan sun ga wata mai suna Asabe da iyayenta suka fitar da ita daga makaranta suka yi mata aure bayan ta yi aure mijinta ya rika dukanta. Haka kuma sun ga Zuwaira wacce ita a da tana talla ne amma sai ta bari ta koma makaranta daga bisani bayan ta gama ta zama Sanata. Don haka su ma suna so ne su zama kamarta.

Ko kuna da wani hadin gwiwa da wasu hukumomi ko kungiyoyi na ciki ko waje  a kan wannan shiri?

Eh, mun samu wani dan tallafi ne daga Gidauniyar Sarki Abdulazeez na Saudiyya, wacce ake kira da  ‘Ginauniyar Sarki Abdul’azeez ta hada kan addinai don zama lafiya.

Kawo yanzu wane kalubale kuke fuskanta?

Kamar a wannan horo da muke shirin bayarwa, muna hadin gwiwa da Cibiyar Zaman Lafiya da Ba da horo Kan Warware Rikici ta Kasa (Institute For Pace and Conflict Resolution). Amma dai kalubalenmu bai wuce na kudi ba. Sannan akwai wani kalubalen na samun labarai wadanda suka dace da Shari’ar Musulunci

Ko kun samu wani tallafi daga gwamnati?

Gwamnati ba ta taba ba mu ko sisi ba. Tallafin kawai da ta yi a yanzu shi ne hadin gwiwar da muka yi da wannan cibiyar da na fada maka.

Wace shawara za ka ba gwamnati?

Ba ni da wata shawara da zan ba gwamnati illa baya ga su yi aikin da jama’a suka zabe su don su yi. Su inganta tsaro su yi ayyukan ci gaba. Su samar da wutar lantarki. Ka ga yanzu haka jannareta ne na kunna haka yake aiki safe da maraice. Don haka ya kamata su inganta wutar lantarki da tsaro ba ma kamar a hanyar Kaduna zuwa Abuja. Mu ba ma son gwamnati ta ba mu ko sisi, gara ta sanya kudin da za ta ba mu ta yi mana aiki wutar lantarki.

Wace shawara kake da ita ga jama’a?

Shawara ta daya ce ga Hausawa matasa, wato su rika kallon shirinmu na Gasar Iyali wanda ake nunawa a kan tauraron dan Adam. Sannan za su iya kallon shirin ta wayoyinsu idan suka saukar da manhajar Gasar Iyali.