✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda muke ganin dare haka muke ganin rana a Kasuwar Alaba Rago – Isiyaka Mai Inji

Lura da yadda jama’a ke fama da rashin samun isasshen wutar lantarki mutane da dama sun fara tunanin yadda za su samar wa kansu isasshiyar…

Lura da yadda jama’a ke fama da rashin samun isasshen wutar lantarki mutane da dama sun fara tunanin yadda za su samar wa kansu isasshiyar wutar lantarki domin gudanar da al’amuransu na yau da kulum. A baya ’yan kasuwa kan nemi kananan injunan bada wutar lantarki lamarin da kan janyo cinkoson kananan janaretoci a kasuwanni da gidaje lamarin da ke barazana ga muhalli.

A Kasuwar Alaba Rago a Legas, amfani da kananan janaretocin wutar lantarki ya kusan zama tarihi bayan da wadansu mutane suka himmatu wajen samar wa ’yan kasuwar wadatacciyar wutar lantarki cikin rahusa, Aminiya ta zanta da daya daga cikin wadanda suka shahara a wannan harka a Kasuwar Alaba Rago mai suna Malam Isiyaka Salihu, wanda ya ce suna samar wa ’yan kasuwar wutar lantarki ta awa 24 a kan Naira 600 kacal a kullum wannan ne ya sanya mafi yawan ’yan kasuwar suka daina mu’amala da janareta wanda hakan ya rage gurbatar muhalli da yake janyowa. Ya ce ’yan kasuwar sun yi maraba da salon wutar lantarkin da suke ba su domin an dauke musu wahalar sayen janareta da  mai da kuma uwa uba gyara ko sauya shi idan ya tsufa, bugu da kari sana’arsu ta kawo karshen yawan gobara da janaretoci ke janyowa domin nasu injin dizel ake sanya masa kuma suna da kwararru da ke aikin sanya turakun wutar lantarki suna kuma bin ka’ida domin guje wa matsala.

Ya ce daga Jihar Kaduna ya zo Legas inda ya fara wannan sana’a, “A baya a Jihar Kaduna nake harkokina na saye da sayarwa tare da buga kaset da sauransu, an yi wani lokaci da aka yi mana rusau a kasuwarmu ina zaune a gida sai wani dan uwana mazaunin Legas mai suna Alhaji Rabi’u ya shawarce ni  in zo Legas in kama wannan sana’a ta bada wutar lantarki ga ’yan kasuwa domin in taimaka wa rayuwata.Wannan shi ne musababbin zuwata Legas kuma alhamdulillahi ana samun rufin asiri kuma muna taimakon jama’a domin masu kananan sana’a da yawa kan amfana, irin masu yin cajin waya, masu aski da sauransu, wadansu ana ba su daga safe zuwa rana ne wadansu kuma da daddare kawai suke bukata wadansu kuma a kowane lokaci ake ba su. Ina amfani da manyan injuna biyu ne wadanda idan daya ya yi aikin tsawon wasu awanni sai in kashe in kunna dayan, a haka muke gudanar da aikin ba da wutar lantarkin ba tare da an samu tangarda ba, kuma muna iya kokarinmu domin guje wa samun matsala, injinanmu ba su da wuta sosai kuma ba sa hayaki,” in ji shi.

Ya ce, sukan fuskanci matsalar wajen karbar kudinsu a hannun wadansu daga cikin abokan huldarsu, inda wadansu ke kin biyan kudin wutar lamarin da kan sa su yanke wutar. “Muna kashe kudi kullum wajen sayen man gas wani lokaci ma yakan yi karanci ya yi tsada a irin wannan lokaci mukan yi asara, amma alhamdulillahi domin wannan sana’a ce ta rufin asiri,” inji shi.

Isiyaka Mai Inji, ya ce da gwamnati za ta shigo harkar ta saya musu manyan injuna ta rika ba su man gas za su kula mata da injunan su sama mata dimbin kudaden shiga kuma hakan zai bunkasa tattalin arzikin jama’a da dama.