Daily Trust Aminiya - Yadda muke kula da yara marayu a Jihar Bauchi – Hassana Arki
Subscribe

Malama Hassana Arkila

Yadda muke kula da yara marayu a Jihar Bauchi – Hassana Arkila

Malama Hassana Arkila ’yar kasuwa ce kuma ’yar siyasa da ta rike mukamai da dama a Jihar Bauchi. A halin yanzu ita ce Shugabar Hukumar Kula da Marayu da Marasa Galihu ta Jihar Bauchi (BASOBCA). A hirarta da Aminiya ta bayyana yadda take gudanar da ayyukan gidanjen marayu da yadda take taimaka wa sauran marasa galihu a sassan jihar:

Tarihina

Sunana Hassana Arkila an haife ni a Dashem Yelwa,  garin Boi na Karamar Hukumar Bogoro. Mahaifina Basayi ne mutumin Marti amma mahaifiyata Bafullatana ce sunanta Fatima. Mahaifina ya je kiwo wajensu ne ya aure ta. Mun girma a ruga ne, na yi tallar masa na yi na koko da kosai sannan na yi sana’ar kunun gyada,  na yi kuli-kuli kai komai da ake yi a ruga na yi. Sannan Allah Ya taimake mu Ya albarkaci mahaifanmu da ’ya’ya 12.

A cikin ’ya’yan nan 12 akwai Honorabul Ibrahim Kadiri wanda ya yi hadari ya rasu akwai Ishaya Kadiri wanda ya rasu yana Shuguban Hukumar DSS sannan akwai Dokta Tambaya Kadiri muna da lauyoyi da Kyaftin na soja da ma’aikatan banki duk cikin dakinmu. To ke nan ka ga ni Basaya ce amma dangin uwata Fulani ne, kuma ina iya magana da harshen Fulatanci kamar yadda nake magana da kai da Hausa.

Ilimi

Allah Ya taimake ni na yi firamare na yi sakandare na yi diploma na yi babbar diploma (HND) kuma na yi hidimar kasa (NYSC).

Aiki

Da yake na shiga harkar kasuwanci da siyasa  baki daya, zuwa yanzu na rike mukamai da dama kamar haka; ni ce tsohuwar Shugabar Karamar Hukumar Bogoro kuma tsohuwar Shugabar Mata ta Bauchi ta Kudu ta Jam’iyyar PDP, yanzu kuma ni ce Babbar Jami’a Ed Officio ta kasa ta PDP, kuma ni ce Shugabar Hukumar Kula da Marayu da Marasa Galihu ta Jihar Bauchi, (BASOBCA).

​Abin da na fi sha’awa a rayuwa

Abin da na fi sha’awa a rayuwata shi ne duk inda na ga mutum yana cikin matsala in ga na warware masa. Wannan ne kawai burina ba ni da burin yin dukiya  ko tara wasu abubuwa da za mu bar su a duniya. Ku je ku tambayi ’ya’yan da mahaifiyata ta haifa 12 nan mutum biyar zuwa shida a ciki za su fada muku ga yadda Hassana take. In na ga mutum a matsala ina iya sayar da zanen jikina don in taimaka masa.

Ban kafa kungiya ba

To ni inda na samu wannan matsala ke nan ban kafa kungiya ba, amma duk inda na samu irin wannan zan taimaka musu don saboda ni ’yar kasuwa ce, kasuwancina na sayar da gwanjo ne. Da wannan kasuwancin kawai nake kokarin taimaka wa mutanen da na ga cewa suna bukatar taimako. Amma yanzu a bangaren kasuwancin taimakon ya kasa don yawan mutanen da nake da su. Don haka tilas sai na sa kaina​ a siyasa wajen taimaka wa ’yan siyasa fitattu don ni ma idan Allah Ya ba ni matsayi sai in yi amfani da matsayin in fadada yawan taimakon da nake da burin yi. Amma ban kafa wata kungiya ta kaina ba. Sai dai in wadansu sun kafa a sani a ciki muna yi tare ina bada gudunmawa, amma ina da niyya in Allah Ya yarda in kafa kungiya ta taimakon mutane.

Marayun da muka tsinta bayan zuwata wanna hukuma

Daga zuwata wannan hukuma mun tsinci yara hudu. Daya da muka samu shi ne wata da kanta ta dauko danta ta kawo mana shi nan. Yarinyar sunanta Asma’u wacce ta samu juna biyu a makaranta, watakila za a kira shi tsautsayi ne ya auku. Ta fito ne daga Jihar​ Nasarawa,​ sai iyayenta suka nuna sun ki ta. Don haka sai ta yanke shawarar babban abin da za ta yi shi ne ta kashe wannan yaro. To kafin ta aikata haka ne ma’aikaciyarmu ta ji labari sai muka karbi yaron. Daga baya sai muka duba  halin da matar take ciki wanda ya nuna kamar akwai tabin hankali.

Mukan yi kokari mu karbi irin wadannan yara amma idan muka ga kamar uwar yaron tana da matsala ce ta ciwo za mu kai ta sashen walwalar jama’a wato Social Welfare.  Amma yara kanana daga haihuwa zuwa shekara 18 a nan gidan marayu muke ajiye su. Shi wancan yaron mun sa masa suna Bala Muhammad yana nan kyakkyawan yaro mun karbe shi.

Sannan akwai wata daga Misau ita ma tabin hankali ne tana da yarinya kuma tana yawo da yarinyar wacce ta kai shekara biyar,  sai muka ga yarinyar nan gaskiya ita ma barinta da uwar wanda ba ta da hankali​ akwai hadari. Ita ma matar an kai ta wajen da ake lura da mahaukata, yau da safen nan aka kawo mini ’yarta sai na ce maza a kai ta gidan marayu a saka ta a makaranta.

Akwai wani yaro kuma wanda shi ma ina ga iyayen suna nan Bauchi ta wajen Nasarawa. Mahaifinsa ya rasu uwar ta ce za ta kaura ta koma wata jiha daban ta bar nan sai yaron karami dan shekara bakwai zuwa takwas ya ce shi karatu zai yi, ya ki bin ta. Sai na ce a nemo uwar yaron nan idan ta yarda ta bar yaron ya yi karatu ni zan dauki nauyinsa ya zauna a cikin wannan gida na marayu a yi masa rajista ya fara karatu. An kusa a dauko shi ya dawo cikin gidan nan na marayu kuma za a dinka masa kayan makaranta da littattafai da takalma da safa.  Yadda na yi wa yara dubu biyar din nan haka shi ma za a yi masa, za a kuma ba shi ci da sha, shi ma ya zama dan gida.

Sannan akwai wata Bafullatana wanda mota ta kade ta bai fi wata daya ba, ita ma ta bar yara bakwai dan karamin cikinsu ne iyayen suka zo suka ce sun rasa yaya za su yi da shi. Sai na ce in dai ba uwa ba uba don na ji uban ma an ce ya rasu. Sannan ga sauran yara bakwai, saboda haka nauyi ya yi yawa wa baffansu. Don haka sai na ce manyan yaran zan iya bada gudunmawa gare su a matsayinsu na marayu amma karamin yaron idan zai zamo

musu nauyi idan sun yarda don komai sai da yarda su kawo shi wannan gida namu na marayu. Don mu ba ma karbar yaro sai da yardar iyayensa sannan lauyoyinmu su sanya hannu kafin mu karbe su a wannan gida. To wannan ne ya sa na ce a je a dauko min yaron amma iyayen kuma ba su yanke hukunci ba tukuna. Saboda haka idan sun yi niyya kofarmu a bude take, kuma shi ma wannan yaro yana zuwa za mu​ sanya shi ya fara karatu a gidan marayu nan. Don haka ina da tanadi na shirye-shirye da nake da su na yara da aka yar ko kuma aka tsinto su ko kuma wadanda suka haife su suka ce ba su so sai a kawo su nan gidan.

Yadda ake yi da yaran idan suka girma

Kafin a kawo yaran nan akan yi da wajewa da iyayen yaran ko danginsu. Tunda duk wanda aka gani akwai dalilin zuwansa nan ba wai kawai ana dauko yaro ba ne ko da tsinto su aka yi an san wanda ya kawo su don haka muna yin yarjejeniya da su cewa wadannan yara za mu lura da muhallinsu daga shekara daya zuwa 18, idan suka wuce shekara 18 za mu mika su zuwa Social Welfare.

Misali yanzu muna da wani yaro kurma da aka tsince shi a daji shekara da shekaru, macizai ne da wasu dabbobi suke ba shi abinci wannan yaro yanzu yana da kusan shekara 20 a nan Bauchi. Wannan yaro yau din nan na sayo masa fam na Cibiyar Koyon Sana’o’i (NDE).  An riga an cika fom din kuma insha Allahu za mu tura a rubuce cewa wannan hukuma ta saya masa gida yana gama koyon sana’a idan ya yi niyyar aure a yi masa aure idan bai yi niyya ba, mu za mu hada kai da Social Welfare su ci gaba da rike shi. Domin yaro​ in ya kai shekara 18 zai fita daga hanunmu.

Kalubale

​Kalubalen da muke samu  shi ne wanda bai san hawa ba bai san sauka ba game da hidimar wannan gida sai su dauki maganar da ba ta taka kara ta karya ba su yi ta yi. Amma irin su ana musu uzuri, duniyar nan fa tun fil azal an yi ta ne da Shaidan a ciki kuma aikinsa ne yakan kawo irinsu, sai dai mu ce Allah Ya shiga tsakaninmu da su.

Burin da nake son cimmawa

Bayan da na yi nazari na lura cewa a mukamina na yanzu, idan na mayar da hankali wajen gabatar da ayyukan gine-gine har in gama shekara hudu ba  za a ci moriyar wannan gida na marayu ba. Don haka yanzu ina so in bar batun gine-gine a gefe. Ba wai na ki ba ne kuma ba wai don ban san muhimmancinsu ba ne. Amma akwai gidajen marayu da suke wahalar gaske, akwai marayu da yawa da ba su da abin da za su ci.  Burina in ga cewa na kula da su ta bangaren kiwon lafiya da koyon sana’o’i da bunkasa tattalin arziki na wadannan gidaje.  Idan mutanen gidan sun kai goma nakan tallafa wa mutum daya ya tsaya a kan kafarsa ta yadda zai iya rike mutum takwas.

Sannan bangaren ilimi muna son mu ga cewa yaran nan da a da su dubu uku ne yanzu kuma na mayar da su dubu biyar, to kafin nan da wata daya ina da burin in je in roki Mai girma Gwamnan Jihar Bauchi cewa makarantarmu ta nan Misau wacce aka kashe sama da Naira miliyan 300 zuwa miliyan 500 aka gina ta ga ta nan tana zaune ba dalibai. Ya kamata ya farfado da ita a sanya ’yan mata marayu. Saboda an yi ta ce domin a koya wa yara ’yan mata kwasa-kwasai na wata hudu idan suka tafi kuma sai an sake rabin​ shekara ana jira a sake kawo wadansu. Kun ga wannan zaman da suke yi ma’aikata kuma ana ta biyansu kudi ba tare da suna aiki ba asara ce.

texem
More Stories