Da Dumi Dumi

‘Yadda na dambace da dan bindiga muka tsira daga masu satar mutane’

Yadda na dambace da dan bindiga

Malam Manu Buba (ba sunansa na ainihi ba) magidanci ne da ya yi jarunta, inda ya kubutar da kansa da sauran mutane daga hannun masu garkuwa da mutane a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna; bayan sun yi kokarin tafiya da su cikin daji. Manu ya rike bindigar daya daga cikin masu garkuwar ne, inda suka yi kokawa da shi har sai da harshasan bindigarsa suka kare sannan ya kwada wa dan bindigar dutse ya dauke bindigar. Ga yadda hirarsa da Aminiya ta kasance:

Yaya aka yi ka kwaci kanka daga hannun masu garkuwa da mutane?

Abin ya faru ne kusan makonni biyu kafin Babbar Sallah da ta wuce, muna dawowa daga Birnin-Gwari a cikin wata mota kirar Sharon, mu tara a cikin motar. Mun iso wani kauye da ake kira Labi sai muka tarar da motoci an tsaitsaya a kan hanya, da muka tambaya sai aka ce mana ai fashi ake yi a hanyar; don haka sai muka tsaya. Kamar kowane lokaci idan ana fashi, da zarar an bude hanya motoci kan yi jerin gwano ne su tafi.

To, mu dama motarmu ce ta karshe, don haka da aka bude hanya sai muka fara tafiya, ga alama motar tana da matsala, domin mun tsaya a wani kauye ya gyara birkinsa. Bayan an yi gyaran, ashe ba a yi mai kyau ba, haka muke tafiya kuma duk motoci sun riga sun wuce, mu ne na karshe. Muna cikin tafiya sai muka tarar da wata motar Dangote, an faka ta tare da wata mota kirar Bibe. Ina ganin haka na ce wannan wurin sai a hankali, ban kammala ayyana abin a zuciyata ba sai kurum na ji harbi a sama.

Mutum biyu suka fito suka yi harbi a sama sai na ce da direba ya taka birki, mutanen ne suka sake fitowa. Muka fito daga cikin motar a guje amma akwai mata biyu da gaskiya ba su iya fitowa ba, domin sun dan manyanta. Mu kuma da muka fito sai muka ruga a guje, ashe barayin sun rabu gida uku – biyu na farko biyu na gaba sun yi wa wajen kofar rago ke nan. Mun wuce wancan a guje ashe suna ta harbi amma sai gudu nake.

ADVERTISEMENT

Da muka kai gaba sai wadansu suka fito suka ce mu kwankwanta. Sai muka kwanta a kan titi, sai ya karbi wayata, dama ina sauraren karatu ne da wayar, sai na ba shi, sai ya ce mu shiga daji. Amma gaskiya ni fa tun ina kwance na yanke wa raina ba zan bi su ba, ko da na tashi har na dauki dutse sai na yar, na ce bari dai in yi magana da sauran wadanda aka kama mu tare. A cikinmu akwai direban da wani jami’in Hukumar Kare Hadurra (FRSC). Jakata kuma na hannun dan fashin kuma akwai kudi ciki da kwamfuta Laptop, akwai POS da agoguna. Sai hankalinsa ya koma kan jakar da yake ya ga kudi ciki.

Da na lura hankalinsa ya koma kan kudin sai nake fada wa abokan tafiyata cewa zan koma in rike mutumin nan, ku zo mu kashe shi. Sai na ga kamar ba su ji ba, sai na ce to zan koma in buge mutumin nan za mu kashe shi. Sai duka suka amsa, da na ji duk sun amsa sai na kara samun kwarin gwiwa. Na fada musu cewa da na ce biyu, zan rike shi. Ina kuma fadin haka sai na rike bindigar, amma sai saura abokan kamuna suka gudu.

Ni kuma sai na ga idan na sake shi zai harbe ni, sai na rike bindigar, shi kuma sai ya kalle ni ya ce min yau na mutu. Na dai rike, ya ja, na ja; ya rika harbe-harbe. Muka fadi kasa duk da haka sai harbi yake yi shi dai kokarinsa ya harbe ni. Ni kuma ina ta kaucewa har Allah Ya taimake ni harsasansa suka kare. Sai muka koma fada da hannu har da naushi. Can dai sai na kara kada shi har na samu dutse a gefe. Shi ne fa na fara kwankwatsa masa dutsen har jini ya fallatsa a jiki na. Ina ganin ya kasa komai sai na zare bindigarsa na gudu.

Da nake gudu a dajin sai nake jin karar titi, sai na rika bin gefen hanyar har na hadu da direbanmu a gabana yana gudu, ban bi ta kansa ba ma, kawai na wuce shi. Da na lura akwai bindiga a hannuna kuma ga shi akwai ’yan sanda a kan titin sai na wurgar da bindigar cikin ciyawa, domin gudun kada su dauka ni ma dan fashin ne kuma ga jini a jikina. Da muka isa wajen ’yan sandan sai suka kwashe mu a mota. Gaskiya sun yi kokari matuka, duk da cewa su ma cikin dar-dar suke. Na fada musu cewa na fa wurgar da bindigar mutumin da muka yi fada da shi a daji.

Suka ce mu shiga mota kurum mu wuce domin wurin na da hadari sosai. Bayan mun shiga motarsu sai suka mayar da mu inda tamu motar take. Da direbanmu ya shiga mun fara tafiya ke nan sai ga daya daga cikin matan da ke cikin motarmu ta fito daga daji, ta ce ai lokacin da muka fara fada da wancan, mun cukume da shi kuma sai harbi ake sai ta shige cikin rami ta kwanta.

Mun zo Buruku sai na tsaya ina wanke jikina, na ce da direban babu inda za shi. Akwai mutum daya wanda Fasto ne, ashe sun dauke shi. A hanya sai muka rika ganin mutanenmu daya bayan daya suna fitowa muna daukarsu.

Lokacin da kuke kokawa yana harbe-harbe, ’yan uwansa ba su kawo masa dauki ba ne?

A’a, ai su tunaninsu da yake harbi yana kora mu ne cikin daji, ni kuma sai da na ga mun yi nisa da su sannan na fara dambe da shi.

Me ya ba ka karfin gwiwa ka tunkari mutumin duk da yana rike da bindiga?

’Ya’yana na tuna, domin ’yar karamar yarinyata koda zan fita gida sai take ce min Baba Allah Ya kiyaye saboda haka suke jin mahaifiyarsu na fadi. Da har na ce musu Zariya za ni, to idan na je Zariya nakan dawo a ranar ce kuma komai dare sai sun jira na dawo za su kwanta. Sai na fada musu cewa Birnin Gwari zan je, don haka sai ita da babban dana suka ce Allah Ya kiyaye Baba. Na ce amin. Ina kwance a kan kwalta sai tunaninsu ya fado min, na ce kai gaskiya ba zan bi mutanen nan ba sai dai in gawata ce amma ni ba zan bi su ba; hankalin mutane ya tashi. Kuma a kai kudi duk da haka a wahala. Shi ya sa na yanke cewa ba zan bi su ba.

Yaya ka yi da direban da daya mutumin da suka gudu bayan sun nuna za su taimaka maka idan ka kwace bindigar?

Bayan mun je ofishin ’yan sandan farin kaya domin ba da bahasin abin da ya faru, saboda ka san kayana da wayata na hannunsu, don kada su je su aikata wani abu. Ina isa sai na tarar da shi jami’in kiyaye hadurra ya je yana ba da bayanin abin da ya faru, har yana fada wa ’yan sandan cewa mun yi fada da masu garkuwa da muaten, bai sani ba ko sun kashe ni. Sai kawai ya gan ni, ni kuma sai na ce da shi gaskiya bai kyauta ba. Sai ya ce in yi hakuri shi tsorata ya yi. Abokina da nake tare da shi a lokacin sai ya ce da ni kada in tada hankalina, tunda Allah Ya kubutar da ni, in rabu da shi kawai.

Shi kuma direban ina ganinsa amma dai ni na rigaya na yanke shawarar ban sake shiga motarsa, domin ba ta da kyau.

Su masu garkuwa da mutanen, wadanne iri ne su?

Ai Fulani ne, ai idan ka ga Bahaushe cikinsu sai dai dan aike ne kawai ko kuma mai ba su bayanai a kan mutane amma sauran masu garkuwa da mutanen Fulani ne.

Wane hali ka bar mutumin da kuka yi dambe da shi a cikin daji?

Ai shi wannan ko ya yi rai ba zai moru ba gaskiya, domin gaskiya sai a hankali. Ni dama fa bukatata ita ce ba zan shiga daji ba, wanda hakan ya sa ko ta kan jakata ban yi ba, duk kuwa da ga jakar kuma zan iya daukarta. Allah ne dai Ya kawo min natsuwa da kuma addu’ar jama’a ta cewa Allah Ya kiyaye hanya da sauransu da kuma yawan azkar da mutum ke yi.

Yanzu dai kayanka suna wajensu?

Eh, gaskiya domin ko dayan ma da aka sake shi ya ce min wai kayana suke sakawa domin jakunkuna biyu nake tafe da su. Kwamfuta kuma na saka lambobin sirri saboda haka ba su iya bude ta ba. Wayoyina kuwa ina ganin a wajen da muka yi fada suka zube, domin ko karamar da ke hannuna da ban ba su ba, a wajen nake tsammanin ta fadi. An kira wayar amma ba ta shiga ba saboda haka nake tunanin a wajen fadan ne suka zube.

Yanzu dai duk wanda ke cikin motar an sake shi ko?

Eh an saki wannan Faston, domin kuwa ya ce min ya jikkata sosai,saboda  a lokacin da ake tattauna sakinsa sun ce su ba za su sake shi ba saboda wai na raunata musu dan uwa, don haka ba za su sake shi ba.

Amma ga alama wanda kuka yi kokawar da shi ba  mai karfi ba ne ko?

A’a, ai irin wannan idan Allah Ya kawo wa mutum natsuwa ba za ka kalli girman mutum ba a lokacin. Sannan wata natsuwa ce ta zo, da yake Allah Ya san akwai sauran kwana. Sannan shi wanda muka yi fada da shi bai kai shekara talatin ba. Da ganinsa ba zai wuce shekara 27 ko 28 ba, babbansu ne nake ganin zai kai kila shekara 40.

Wane jan hankali za ka yi ga jama’a, musamman direbobin da ka ce wasu motocin nasu ba su da kyau amma kuma suke daukar fasinja?

Al’umma dai mu koma ga Allah kawai, domin mun taba Allah da yawa. A Birnin Gwari na yi karatu, na san garin sosai, gaskiya an taba Allah. Akwai almajirin da an taba kwakule masa ido. An yi lokacin da wannan gari ya koma kamar dandali ne na karuwai, har cutar AIDS ta yi yawa. Akwai abubuwa da yawa da aka yi a garin irin su shirka da sauransu. Saboda haka abin da kawai ya dace shi ne mu koma ga Allah domin an taba Allah.

Sannan  wadannan abubuwa da suke faruwa alamu ne na karshen duniya saboda haka sai dai kurum su yi sauki. Da farko an soma ne da Boko Haram, aka zo aka yi satar shanu, sai rikicin manoma da makiyaya, sai kuma yanzu ake batun garkuwa da mutane. Daga wannan fitina sai waccan, duk alamu ne na karshen duniya. Sai dai kurum a samu sauki.

Jami’an tsaro na kokarinsu matuka, musamman wadanda ke sintiri a yankin Birnin Gwari har ya zame min ka’ida ne, idan har zan je garin nan sai na ba su Naira dubu daya, sai mu dan yi wasa da su kafin mu wuce. A wannan rana sun fada min cewa sau uku suna korar wadannan mutane amma suna dawowa. Abin mamaki a ce wai ana tattaunawa da mutanen har sa’a daya amma a ce wai ba za a iya gano inda suke ba. Amma idan aka kama wani babba za ka ga cikin karamin lokaci an gano inda suke. Wannan gwamnati dai tana nan kuma abin da take yi yana nan har ila yau abin da muke aikatawa yana nan, domin kowa ya san abin da yake aikatawa.

Share