Daily Trust Aminiya - Yadda na dauki nauyin karatuna da facin taya – Isa Abba
Subscribe

Yadda na dauki nauyin karatuna da facin taya – Isa Abba

  • Kuma na fita da Digiri Mai Daraja ta Daya

Isah Adam Hussaini wanda aka sani da Isa Abba matashi ne dan shekara 30 da yake sana’ar facin taya a garin Jos Babban Birnin Jihar Filato. A tattaunawarsa da wakilinmu, ya bayyana yadda ta hanyar sana’ar facin taya, ya dauki nauyin kansa ya yi karatu tun daga sakandare zuwa jami’a, inda ya samu Digiri Mai Daraja ta Daya (First Class) a fannin kididdiga daga Jami’ar Jos:

Yaya aka yi ka kama wannan sana’a ta facin taya?

Sana’ar facin taya kusan na gaje ta ce daga iyayena. Domin kusan kowa a gidanmu yana yin wannan sana’a. Na taso na ga mahaifina da kanensa suna yin sana’ar. A wajen kanen mahaifin nawa na koyi sana’ar.

A wane lokaci ne ka bude wannan waje na yin facin taya?

Bayan da na koyi wannan sana’a a wajen kanen mahaifina, sai Allah Ya sa na bude nawa wajen. Da farko mun zauna da kanen mahaifina ne a ’Yan Taya a nan Jos. Daga nan sai ya tashi ya koma NEPA da ke  kan Hanyar Zariya a nan garin Jos. Ganin wajen da ya koma ya yi mini nisa da kuma ganin na iya wannan sana’a,  shi ne na bude nawa wajen; wanda ya yi kusa da Makarantar Jama’atu da nake zuwa karatu a lokacin.

Wadanne nasarori ka samu a wannan sana’a ta facin taya?

Babbar nasarar da na samu a wannan sana’a, ita ce, cikin ikon Allah a wannan sana’a na rika samun kudin da nake biyan kudin makaranta. A haka har na gama karama da babbar sakandare. Sannan kuma Allah Ya taimake ni na tafi Jami’ar Jos, na yi karatun digiri a fannin Kididdiga kuma na fita da Digiri Mai daraja ta Daya (First Class Degree) a shekarar nan da ta gabata. Duk da wannan sana’a na samu kudin da na yi wannan karatu.Domin na dauke wa mahaifina komai a kaina, na ce ya ci gaba da daukar nauyin kannena, domin an riga an koya mini sana’ar da zan rike kaina.

Yanzu an tura ni aikin yi wa kasa hidima. Da farko an kai ni Jihar Imo ce, da na je na ga yanayin rayuwa tana da wuya a can, sai na bukaci a taimaka mini a dawo da ni gida Jos. Na samu na dawo, yanzu ina aikin yi wa kasa hidima ne a Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da ke nan Jos, inda nake koyarwa. Kuma a kullum bayan mun tashi daga makarantar nakan zo in kama sana’ata ta faci.

Bayan haka kuma yanzu na sayi fili da zan gina gida, a garin Tilde da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi. Duk da wannan sana’a na samu wadannan nasarori.

Wadann matsaloli ka fuskanta a wannan sana’a?

Matsalolin da na fuskanta a wannan sana’a sun shafi kamar ta bangaren karatun da na yi. Wani lokaci idan na tafi makaranta saboda karatu, ba na samun lokacin da zan zo in yi  sana’a. Domin wani lokaci idan na bar wurin aiki tun ranar Asabar, sai wata Asabar din. Amma a cikin ikon Allah, a cikin wadannan kwana biyu, nakan samu kudin abincin da zan ci da dawainiyar makarantar, har wani makon ya zagayo.

Wane kira ko sako kake da shi zuwa ga matasa dangane da muhimmancin koyon sana’a?

Gaskiya ina bai wa matasa shawara cewa ya kamata su fahimci cewa yanzu an kai lokacin da ba a dogara da takardar kammala makaranta.

Akwai lokacin da wani ya kawo mini aiki daga kwalejin da nake koyarwar hidimar kasa. Bayan da na gama yi masa aiki, sai na ga yana ta kallona. Sai na ce masa mene ne ya faru na ga yana ta kallona? Sai ya ce ya ji mamakin ganin yadda ba ni da girman kai ne.

Ya ce yaya za a yi in yi karatu irin wannan amma in zo ina aiki a cikin rana? Sai na ce masa da wannan aiki na yi wannan karatu da kake magana, wanda har ya sa ka san ni.

Saboda haka yanzu an kai wani zamani da bai kamata mutum ya raina sana’a ba. Bayan karatun da mutum yake yi, ya kamata ya samu wata sana’a ya kama, wadda zai rike kansa da iyayensa da ’yan uwansa.

Wane kira ne kake da shi ga gwamnati game da tallafa wa masu kananan sana’o’i?

Gaskiya ya kamata gwamnati ta yi wani abu kan tallafa wa masu kananan sana’o’i saboda yanayin yadda abubuwa suke tafiya a kasar nan, a halin yanzu. Domin idan gwamnati tana tallafa wa masu sana’o’i, wadansu matasan da suke ganin sun fi karfin yin wata sana’a za su fito su yi. Idan aka yi haka za a rage rashin aikin yi a kasar nan, domin rashin aikin yi ne yake kawo ta’addancin da ake fama da shi, a sassan kasar nan.

texem
More Stories