Search
Subscribe
Yadda na fara sarrafa ’ya’yan itatuwa ina jus da su – Dokta Kal

Yadda na fara sarrafa ’ya’yan itatuwa ina jus da su – Dokta Kal

Malam Aliyu Idris Adam wanda ake kira da Dokta Kal, matashi ne mai son yawan bincike  a kan amfanin ’ya’yan itatuwa ga dan Adam da kuma magungunan gargajiya inda yadda ake hada su don su dace da zamani. Wannan sha’awa tasa ta sa ya fara hada abubuwan sha (Juice) daga ’ya’yan itatuwa irin su tsamiya da goriba da sauransu. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana yadda ya fara sana’ar da yadda take bunkasa har ya kai ga rajistar kamfaninsa.

Mene ne takaitaccen tarihinka?

Sunana Aliyu Idris Adam wanda wadansu ke min lakabi da Dokta Kal. An haife ni a Karamar Hukumar Kunci a Jihar Kano. Na yi makarantar allo daga bisani saboda sha’awata ta yin karatun boko na shiga makarantar yaki da jahilci a garin Funtuwa, ba zan manta ba Dokta Sani Malumfashi na Jami’ar Bayero ne ya sanya mini dan ba lokacin ya kammala jami’a ba da dadewa ba. Bayan haka sai na ga ya dace in yi karatun sakandare don haka na shiga karatun sakandare wanda ake yi mako-mako wato upgrading course. Na kammala karatun da yabo tara da kowane dalibi yake son ya fita da shi.

Daga nan na shiga Kwalejin Shari’a da Koyon Harshen Larabci ta Malam Aminu Kano na yi diploma a Harshen Larabci da Ingilishi. Kuma na je Jami’ar Bayero na yi Satificate kan ilimin Kwamfuta. Kuma saboda kasancewata mai son bincike a kan koyar da sana’a da bincike kan tsirran da muke da su, duk inda na ji labarin za a yi wani taron kara wa juna sani sai in kukuta in halarta.

Yaya ka fara ingantawa da kirkiro abubuwan sha daga ’ya’yan itatuwa?

To alhamdulillahi, da farko mahaifina masanin itatuwa ne, kuma ya nuna mana kafin Allah Ya yi masa rasuwa. Kuma ka san ma’abocin bincike ne, duk lokacin da na ga wani abu da aka ce da abubuwan gargajiya aka yi kamar turaren mota ko na ban-daki ko sabulu ko man goge baki nakan bi diddigin in gano abubuwan da aka hada ni ma in zo in yi kokarin hada nawa. Da farko na fara yin Jus na tsamiya ne a gida, ina hadawa ina rabawa kyauta kuma muna sha da iyalina ko idan na yi bako in hada masa. Daga nan sai wadansu da suke sha su ji dadi kuma su samu lafiya suka fara aikowa ana saya musu a gida. Sai suka fara yi mini magana kan ya kamata in inganta shi.

Bayan na kara bincike a kan amfanin tsamiya ga lafiyar mutane da yadda ake hada jus sai na fara saka jarin Naira dubu biyu. Cikin ikon Allah sai na fara samun kasuwa abin kullum yana kara bunkasa jama’a na tambaya, domin suna sha suna jin dadi.

Banda jus din tsamiya wadanne abubuwa kake sarrafawa?

Bayan tsamiya ina yin jus din goriba, lokacin da na fara, na yi ta samun mishkila amma da na nace da bincike a yanzu mun daidaita da ita. Kuma mutane suna sha suna samun lafiya da jin dadi. Sannan akwai jus din kuka wato na ’ya’yan kuka da aka fi sani da suna kwalba. Daga bisani sai na sake buda tunanina na kara bincike a kan amfanin giginya da yadda zan bullo da jus dinta. To shi ma dai Allah cikin ikonSa a yanzu muna sarrafa ta kuma ina yin jus dinta. Wadannan su ne wasu daga cikin kayan sha da muke yi na ’ya’yan itatuwa da muke da su a nan Arewa.

Ta fannin magunguna fa?

Akwai maganina na farko da na fara yi wanda na sa masa suna ’The wonderful coffe’ a harshen Ingilishi wanda yana maganin basir da kara karfin idanu. A lokacin da na fara shi akwai yayana Abubakar direban tirela,  shi ya rika daukar maganin yana tafiya da shi yana sayar wa abokansa direbobi. Sai suka rika kirana ta waya suna neman a tura musu maganin saboda yadda suke ganin fa’idarsa.

Bayan na ci gaba da bincike da karatun littattafan magabata, a yanzu ina da magunguna da dama da na inganta daga tsirrai. Misali akwai ‘natural tomeric shamfoo’ da ‘natural Moringa shamfoo’ wato shamfo na zogale don gyaran gashi. Akwai kuma maganin da muke kira ‘cold destroyer’ wato maganin sanyi na ruwa da na gari. Saimaganin sanyi na maza da na mata da sauransu.

Ita kanta goriba saboda maganin da take yi ina yin garinta da za ka iya lasa ko ka zuba a kunu ka sha. Akwai wanda aka sanya wa sukari kadan akwai marar sukari.

Ka taba samun wani tallafi daga gwamnati ko mutane?

Gwamnati ban taba samun wani tallafi ba, amma akwai abokan arziki da ba zan manta taimakon da suka yi mini ba musamman  maganar jari. Akwai aminina da yake sayar da waya a Kasuwar Wuse, Abuja Alhaji Umar Faruk Musa da Alhaji Usman Danfulani da Malam Sani Bala da Sakatarena Malam Falalu A. Yunus da Alhaji Yahuza Suya da sauransu da suka tallafa wajen ganin na kafa kamfanina, mai suna Garun Sheme Agro Allied and General Serbices wanda a karkashinsa ne muka fitar da Nice Maysur Islamic Chemist and Natural Healthy drinks. Na sa wa kamfanin sunan kauyenmu ne Garun Sheme.

Kawo yanzu wadanne nasarori ka samu?

A gaskiya babu abin da zan ce sai dai godiya ga Allah, tunda na fada maka da Naira dubu biyu na fara amma ga shi yanzu har mun kai ga yin rajistar kamfani kuma akwai mutanen da suke ci a karkashinsa. Ke nan na sama wa kaina da iyalaina da kuma wadansu da dama aikin yi.

Wadanne kalubale kake fuskanta?

Kalubalen dai bai wuce na jari ba. Domin da ina da jari mai kauri ina tabbatar maka cewa cikin wasu ’yan shekaru masu zuwa sai mun raba mutanenmu da shan garura da kemikal da suke sha da sunan abin sha, wadanda suke da illoli ga lafiyarsu, mu samar musu da abubuwan sha masu dadi da suke da amfani ga lafiyarsu kuma aka yi daga itatuwan da suke gonakinsu. Don haka ina kira ga gwamnatoci su juya hankalinsu wajen tallafa wa mutane masu basira da kokarin sana’a don inganta rayuwarsu da samar wa jama’a aikin yi.

Wane kira kake da shi ga matasa?

Matasa ya kamata su sani idan har kana son ka rufa wa kanka asiri, ka cire girman kai ka dauki kanka ba komai ba. Ka daina zaman jiran gwamnati ta samar maka aiki. Ni ban yarda wai babu aikin yi a kasar nan ba. Akwai aikin yi kai har ma ya yi yawa, sai dai idan zuciyarka ta mutu ne ba za ka ga haka ba.

 

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin