✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda na yi jinyar coronavirus -Shugaban kwamitin COVID-19 na Kano

Shugaba na biyu na kwamitin kar ta kwana kan yaki da annobar coronavirus na jihar Kano,  Farfesa Abdulrazak Garba Habib, ya bayyana yadda kwanaki 20…

Shugaba na biyu na kwamitin kar ta kwana kan yaki da annobar coronavirus na jihar Kano,  Farfesa Abdulrazak Garba Habib, ya bayyana yadda kwanaki 20 da ya yi a killace yana jinyar cutar coronavirus suka kasance.

Farfesa Abdulrazak  ya kuma bayyana wasu magungunan da ya yi amfani da su a wasu sakwannin da ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ruwaito daga gare shi, wadanda ta wallafa a shafinta na Twitter.

Farfesan dai ya fara ne da sanar da sallamar shi bayan “sakamakon gwaji ya nuna ba na dauke cutar… Na kamu da cutar coronavirus ne lokacin da nake aiki da kwamitin kar ta kwana kan yaki da annobar coronavirus.”

Daga nan sai ya ce, “A lokacin da nake jinyar cutar na yi fama da zazzabi da tari da daukewar numfashi da rashin jin dandano da amai da gudawa da tsamin jiki; na yi rashin lafiya na kimanin wata daya sannan aka killace ni na kwanaki 20 ina jinya.”

Magungunan da na yi amfani

Farfesan, wanda malami ne a sashen koyon aikin likita na Jami’ar Bayero ta Kano kuma likita a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano,  ya kuma bayyana irin magungunan da ya yi amfani da su yayin jinyar tasa.

“Na yi amfani da magunguna da dama wadanda suka hada da: ruwan gishiri da sukari, da na’urar shakar numfashi, da habbatus sauda, da man kanunfari, da shayin citta….

“Cutar ta yi sanadin raguwar nauyina da kilogiram bakwai”, inji shi.

Riga kafin cutar

Farfesa Abdulrazak  ya kuma yi kira ga mutane su ba da gudunmawa wajen hana yaduwar cutar ta hanyar “ba da tazara da bin dokar hana fita da amfani da takunkumin rufe fuska, da kuma amfani da su yadda ya dace.”

An dai sallami Farfesa Abdulrazak ne ranar Alhamis.