✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda na musulunta -Abdullahi Edward

Abdullahi Edward baturen Amurka ne da ya shafe fiye da shekara 40 a kasar nan, a tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana yadda aka yi ya…

Abdullahi EdwardAbdullahi Edward baturen Amurka ne da ya shafe fiye da shekara 40 a kasar nan, a tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana yadda aka yi ya karbi addinin musulunci da yadda dangantakarsa da iyalinsa take da kuma dangantakarsa da Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero.Ga yadda hirar ta kasance.

Aminiya: Ka zo Najeriya a matsayin mabiyin addinin kirista, yaya aka yi ka zama musulmi?
Abdullahi: Na fara ganin musulunci a karo na farko ne a lokacin yakin basasa. Ranar jumu’a na tafi babban masallacin jumu’a na Kano, wanda ke bayan gidan sarki, lokacin da na isa sai na ga dubban mutane suna sallah a tsanake. Ban san abin da suke cewa ba, ban kuma san abin da suke yi ba, amma na jinjina musu saboda yadda na ga suna yinsa.
Aminiya: A wannan lokacin ne ka fara ganin musulmi suna sallah?
Abdullahi: kwarai kuwa, saboda kafin wannan lokacin babu abin da ya taba hada ni da su. Lokacin da na je wurin, da yake lokacin yakin basasa ne, sai na fara tunanin cewa, da ni matukin jirgin yakin Biyafara ne idan zan jefa bam a Kano a masallacin zan jefa lokacin sallar jumu’a. Na tsaya ina kallo, ina mamakin yadda mutane suke yin komi a tsanake, babu wanda yake magana ko dariya ko yin wani abu daban, kowa ya yi shiru yana sauraron karatun liman. Sai na fada wa kaina cewa lallai wannan abin mamaki ne. Duk da cewa abokan gaba na iya jefa musu bam din Biyafara, amma duk da haka suka taru a wuri guda suna sallah. Wannan ne karo na farko da ci karo da addinin musulunci.
Bayan shekaru da dama, a cikin shekarun 1980 ina zaune a Landan, wanda a wancan lokacin Naira 400 ta ishe ka zuwa da dawowa, daga Kano zuwa Landan. A wancan lokacin mutanen Kano suna zuwa Landan hutun karshen mako, domin haka ina haduwa da abokaina akai-akai, kuma da dama daga cikinsu suna zuwa masallaci a Landan. Sai na fara sauraron wa’azin Ahmad Deedat a kaset din bCR. Ana nan kuma da na dawo Kano sai na fara sauraron tafsirin Isa Waziri da yake yi a gidan talabijin na Kano CTb a lokacin azumin watan Ramadan. A wannan lokacin ina fahimtar Hausa sosai, domin haka na fahimci cewa lallai wannan mutumin yana da basira, domin ya kan dauko abu mai sarkakiya ya mayar da shi mai sauki. Isa Waziri ya kan je Landan ya sauka a gidan Galadima. Bayan ya tashi daga wurin Tafsiri Isa Waziri ya kan gayyace ni cin abincin dare, daga nan sai mu zauna mu yi hirar duniya. Wata rana da ya gayyace ni, lokacin da zan fita sai ce masa, ‘’Malam kada ka yi mamaki idan wata rana na zo ina buga maka kofa,’’ ya ce sai ka zo.
Bayan wadansu shekaru, da na dawo Najeriya sai na wuce kai tsaye gidansa na buga masa kofa, sai na ce masa gani na zo, ya yi muemushi ya ce, Bisimillah. Sai ya tambaye ni sunan da nake so a kira ni da shi, sunan da na fara fada masa shi ne ‘Abdullahi’, yadda sunana ya zama Abdullahi ke nan. Kodayake tun tuni na riga na sanya wa dana suna Abdullahi, domin ina sha’awar sunan. Da yake Bashir Tofa yana tare da ni a cikin jirgi lokacin da zan dawo Najeriya, yana sane da niyya ta ta karbar musulunci.
Aminiya: Ka ce danka ya riga ka amfani da suna Abdullahi, yaya aka yi haka?
Abdullahi: An haifi dana ne a Ingila a shekarar 1983, shi ba musulmi ba ne, amma na sanya masa wannan sunan ne saboda ina sha’awar sunan. Na bar matata ta sanya wa ‘yarmu suna, ni kuma na sanya wa danmu namiji suna.
Aminiya: Yaya iyayenka da abokanka suka ji da ka zama musulmi?
Daga hagu, Abdullahi Edward ne rike da dansa Abdullahi(Anis),sai Sarkin Kanem, sai Mai martaba Sarkin Alhaji Ado Bayero, sai dansa Abdullahi, sai kuma matarsa Hauwa da sauran ‘ya’yansa da kuma wadanda yake goyonsu, lokacin da ya kai wa Sarkin Kano ziyara.Abdullahi: Da farko dai ni ba ina zaune tare da iyayena ba ne, sun samu labari ne cewa na musulunta. Ban cika zuwa Amurka ba, amma idan na tafi ba na samun matsala da sunana. Amma kakana bai ji dadi ba, saboda shi ya fi kula da addini fiye da iyayena. Ya fada mini cewa iyayensa duk ‘yan darikar katolika ne, haka ‘ya’yansu, a tsawon rayuwarsu. Ya ce bai ga wata matsala tattare da addinin ba, domin haka babu dalilin da zai sanya in canja addini. A bangaren mahaifiyata kuwa ta dade da sanin cewa ina da ra’ayin kaina, saboda haka ba ta yi mamaki ba da ta ji labarin na musulunta. Shi ma mahaifina bai damu ba.
Lokacin da nake zaune a Landan, wani abokina dan kasar Liberiya ya taba tambaya ta, ya ce, ‘’meye dalilin da ya sanya kake son zama a nahiyar Afirka, bayan kai mutumin Amurka ne, amma kullum kana maganar komawa Afirka ka yi aiki?’’ sai na ce masa, babu kidahumai irin Amurkawa, domin suna da wayewar kai amma ba su san komi ba. Na biyu,tun ina dan shekara 20 na fahimci wani abu game da Afirka, bayan shekaru da dama ne aka taba tattauna kalmar Islam a Amurka. Na yi tsanmanin a rika yi mini irin tambayoyin da kuke yi mini lokacin da na koma, maimakon tambayoyi irinsu: mutane suna kwana a kan bishiyoyi ne a Najeriya?
Aminiya: Irin tambayoyin da ake yi maka ke nan?
Abdullahi: kwarai kuwa,duk mutumin da ke  da irin wannan tunanin kuma ya kasa rabuwa da shi, ba zan iya zama da shi ba.
Aminiya: Ta yaya ka hadu da matarka?
Abdullahi: Lokacin da na hadu da matata Hauwa, ‘yar dandagoro a jihar Katsina, na riga na haifi ‘ya’ya biyu da matata ta farko ‘yar Najeriya. Sai na fada wa abokin aikina cewa ina so in samu wata matar da za ta taimaka mun wajen kula da ‘ya’yana. Sai ya ce akwai wata yarinya ‘yar shekara 15 zuwa 16, amma ta ce ba za ta yi aure ba sai ta kammala karatun sakandare. Ya yi mun magana da uban goyonta. Bayan ‘yan kwanaki sai ya zo ya fada mini cewa ya ce in zo in yi magana da ita, na je muka tattuna da ita a wani shago da mutane da yawa suke taruwa, muka yi zance na farko, daga nan muka ci gaba. Ta kammala karatunta a watan Yunin 1996, amma an aurar mini da ita a watan Afirilu, daga nan na dauke ta zuwa Kano. Daga shekarar 1996 zuwa yanzu ta haifi ‘ya’ya 7 da 2 da ta same ni da su, sun zama ‘ya’ya 9 ke nan a gabanta. Abokin aikin nawa da ya hada aurenmu ya ba ni diyarsa guda in rika masa, muna tare da ita fiye da shekara 8 yanzu, domin haka yaran da muke kula da su guda 10 ke nan.
Aminiya: Duk da bambance-bambancen da ke tsakaninku yaya kuke zama?
Abdullahi: Ta kammala babban sakandare a Najeriya, ni kuma ba’amurke ne, na grime ta da kusan shekara 35, an haife ta a shekarar 1977, ni kuma an haife ni a shekarar 1942. Mun fahimci bambance-bambancen da ke tsakaninmu, mu san yadda za mu girmama junanmu, shi ya sanya har yanzu muke tare. Tana da ilimin addinin musulunci sosai, hasali ma dai lokacin da na aure na fada mata cewa ina da ka’idoji guda biyu, na farko ba na son gulma, na biyu, dole ne ki rika tashina in yi sallar asuba.
Aminiya: Me ya sa ita za ta rika tashinka?
Abdullahi: Haka nake,na tashi a cikin gida mai ‘ya’ya 7, kuma su ne suke tashina a kowane lokaci, domin agogo ba ya iya tashina. Yanzu haka ‘ya’yanmu uku na farko sun sauke Alkur’ani.
Aminiya: Ka dade da haduwa da Sarkin Kano ne?
Abdullahi: kwarai kuwa, na hadu da shi ne a shekarar 1977, kuma shi ne ya tsaya mini na samu takardar shedar zama dan kasa a shekarar 1991, wanda ya tsaya mini na biyu shi ne Turakin Gumel, a yau ni cikakken dan Najeriya ne.