✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda na samu kaina a wakokin Sudan – Shetima Mansur

Aminiya ta sami tattaunawa da mawakin Hausan Sudan, Shettima Mansur, wanda a yanzu haka yake zaune a garin Maiduguri Jihar Borno, a dangane da tarihin…

Aminiya ta sami tattaunawa da mawakin Hausan Sudan, Shettima Mansur, wanda a yanzu haka yake zaune a garin Maiduguri Jihar Borno, a dangane da tarihin rayuwarsa da kuma yadda aka yi ya tsinci kansa a cikin sana’ar wakokin Sudan, duk da cewar asalinsa dan Najeriya ne, tare kuma da irin gwagwarmayar  da ya sha a rayuwarsa.

 

Ko za ka fada mana takaitaccen tarihinka da kuma irin gwagwarmayar da kasha a rayuwarka?

Ni dai na farko Bahaushe ne Uwa da Uba, domin Mahaifina mutumin Getsone kuma Mahaifiyata mutumiyar Daura ce. Amma kuma ni sun haifeni ne a kasar Sudan a kan hanyarsu ta zuwa Saudiyya don su sauke Farali.  Ka san a wancan loacin Iyaye da Kakanninmu suna tafiya Saudiyya a kasa ne amma sukan yada zango a wata kasa su yi noma sannan kuma sai su kara gaba, kafinnan sukan hayayyafa a wurin da suka yada zango, kamar yadda namu Iyayen sukayi don sun haifemu a Kasar Sudan Ni da wasu Yayyena, to amma ni kuma tun ina dan shekara tara Iyayen nawa suka dawo Kano a nan Najeriya, shikenan sai muka ci gaba da zama a nan Kano na dan wasu shekaru, sai ni kuma Sana’ar aikin Mota ta kawoni nan Maiduguri, domin a zaman da mukayi a Kano ni Direban Manyan Motocin Tirela. To kasan na gaya maka cewar ni Direbane don na zama Karen Mota a Kananan Motoci kama-kama har nazo na iya jan Mota har kuma nakai ga jan Tirela tun daga Kano har zuwa Maiduguri, har zama ya zo ya kasance a Maiduguri, to ana nan a hankali kasan in nan taki sai a koma can idan kuma can  taki sai a koma wani wurin to a haka dai akayi ta gungurawa,  cikin waka ta zame mini gaskiya tun ina yi da wasa da wasa sai mutane suka mayar mini da ita gaskiya, domin ina  ganin wasa ne don ba gadona bane aa haye ne kawai nayi, amma mutane sai su rika kirana sai su ce in zo in yi wasa a gidan aure ko suna ni kuma sai ina ganin sa ni ban kai matsayin da za a kirani ba.

 

To amma mene ne ya ba ka sha’awa har ka tsunduma cikin wakokin kasar Sudan? Domin wadansu sun dauka kai mutumin Sudan ne ka zo nan Najeriya kake yin wannan wakar.

Eh to to ai na gaya maka tun muna Sudan  ni da iyayena sukan tasa Rediyo a gaba idan an sanya wakokin Muhammadu Wardi suke sauraro, musanmmama Mahaifiyata, idan mun dawo daga Makaranta  za muga tana sauraron Rediyo ba kuma komai take sauraro ba sai wakokin Dan Wardi, wato Muhammadu Wardi, don a lokacin Dan Wardi suke ce masa, wato Babansa Wardi shi kuma Muhammadu sai ta kore mu ta ce mu bar ta ta ji wakokin Dan  Wardi, har sai muna dariya sai mu ce wanene kuma Dan Wardi tun ban gane ba har na zo na gane Muhammadu Wardi tun a can Sudan har muka dawo Najeriya wakokin Muhammadu Wardi na ke sauraro a ko wani lokaci kuma shi na ke son sa. Sai Allah ya hadani da wani bawan Allah a nan Kano shima mai yawan jin wakokin Muhammadu Wardi, to idan mun zo nan Maiduguri sai mu je babban layi wajen wani Alhaji Nasiru sai ya sayi Kaset-Kaset na Sudan kala-kala  sai  mu kai Kano mu yi ta sauraro kuma anan ne na san wasu daga cikin sunayen mawakan Sudan har ya kasance ina tukin Mota Kaset dinsa na ke sakawa a duk inda zan tafi kama tun daga Kano har zuwa ko wani gari kuma ko wani kasa saboda son sa da nake yi har ta kai ga na haddace akasarin wakokinsu kuma na san ma’anansu.

 

To ka yi suna a kan wannan sana’ar ta wakokin Sudan amma da Hausa kuma a ina ka smu kayayyakin kade-kade irin na Sudan?

A gaskiya yadda aka  tallafa mini anan garin Maiduguri shi ne akwai wani ana ce masa Kamal Yakubu, don tare muke fita dashi kuma tare muke wakoki sannan wata rana ina yi masa kida wata rana in yi busa.

Muna nan dai muna yi tare da yake faduwace ta zo daidai da zama, na zo nan garin na taras da yanayi ni kuma ina son wakokin irin na Sudan kawai sai na saje dashi to lokacin kusan zan ce na iya wakoki amma Kamal Yakubu ya taimaka mini da kayayyakin wakoki da kuma irin tasa fasahar don na karu matuka don tare muke yi dashi a ko wani lokaci zamuje in da duk aka kira mu muyi wasa tare.

 

Ka ce Kamal Yakubu yana daya daga cikin wadanda suka tallafa maka wajen waka to kamar ta yaya?

A’a ai na fada maka cewar na riga na iya wakata tun ina sana’ar Direba na koyi wakokin Sudan saboda yawan sauraronsu da na ke yi, kuma tsohuwata ta cusa mini son abin a zuciyata, sannan na fada maka akwai wanin da muke yawan zuwa da shi nan garin Maiduguri da mota musanmman muna sayan kaset na Sudan. Ai na riga na iya su tun kafin in dawo nan Maiduguri. Shi dai Kamal Yakubu ya taimaka mini da kayan kide-kiden shi ne kawai, don da na zo na same shi yana dan tabawa sai ni kuma na wafce don na riga na fada maka cewar ba gadona bane.

 

To yanzu yaya yanayin sana’ar wakar take, tana nan kamar da ko abu ya sauya?

E to Alhamdulillahi, ba abin da zan ce sai godiya, domin babu wani abin da ya sauya abin da na ke samu ada yanzu ma ina samun sa, sai dai kuma dan abin da ba a rasa ba, kuma kasan ada kudi ya na da daraja ba kamar yanzu ba. Sannan kuma zamani ya canza ba kamar a da, to amma abin da aka samu ada ana nan ana ta riritawa, kuma na sami arziki a gwamnatocin baya, sannan kuma a yanzu ana gayyatata a ko wani wurin da ake da bukukuwa bama a Borno ba har jihohin Kudancin Kasar nan dama kasashen makwabta. Na  mallaki motoci kusan 10, na yi aure da yarana 10, na mallaki gidaje na kaina, sannan kuma wannan Mai Martaba Shehun Bornon Alhaji Abubakar Umar Grabai, Al-Amin EL-Kanemi, ya kai ni na sauke Farali a Saudiyya. Ai na gode Allah, a gaskiya zance na sami rufin asiri da daukaka da wannan wakar. Ba abinda zan ce sai dai Alhamdulillahi, na gode Allah.’’

 

Akwai wani yunkuri da na ga ku mawakan Borno kuna yi na hada kai da nufin zama tsintsiya madaurinki daya, shin ina aka kwana ne?

E to gaskiyane muna  kokarin yin hakan kuma muna fata ya dore,domin daukacin mu mawakane na ko wani irin yare ko kuma harshe muka hadu muka ga ya kamata mu zama tsintsiya madaurinki guda. Don wani ba ko ina ne in yaje ake kallonsa ba ballantana a bashi dama aji irin tasa basirar balle ayi maganan alkharin da zai samu, kuma ka ga mawakan zamanin nan sun taho da tasu, don a wani lokacin mu kan zama ‘yan kallo ne, muna ji muna gani sai mahukunta su gayyato wasu mawakan a wani wuri can da nisa amma mu gamu anan ba za a kallemu ba, kuma za su basu dimbin dukiya, amma mu anan sai mu kwana da yunwa alhali muna da tamu basirar da hikimar da Allah ya hore mana wanda zamu iya bayar da tamu gudunmuwar wajen gina kasa ta hanyar gyaran tarbiyyar yaran zamani ta na mu irin hikiman da Allah Ya bamu, amma sai kaga ana kokarin taushe mu bayan kuma shi ne hanyar abincinmu, shi ya sa mu ka ga ya kamata mu hada kai da kafa, muyi magana da murya daya mu zama tsintsiya madaurinki daya.