Da Dumi Dumi

Yadda na zama Kanar din soja daga almajiranci – Adamu Girbo

Sheikh (Kanar) Adamu Girbo Muhammad (mai ritaya)
Sheikh (Kanar) Adamu Girbo Muhammad (mai ritaya)

Sheikh (Kanar) Adamu Girbo Muhammad (mai ritaya) ya ce da aikin tuka babbar motar dakon kaya aka dauke shi aikin soja a 1967 a matsayin kurtu. A haka har ya samu damar yin karatu bayan ya halarci fagen fama an fafata da shi a Yakin Basasa a 1967 zuwa 1968 da wasu yake-yaken kasashen duniya:

Yaya aka yi ka shiga soja, bayan kai direba ne?

Ni tsohon soja ne mai mukamin Kanar. Na yi aikin soja tsawon shekara 35 kuma na shiga aikin soja ne lokacin da aka sanya ni a makarantar allo, lokacin ina fadar Mai martaba Sarkin Gombe. A lokacin ana Yakin Basasa (Yakin Biyafara) aka zo ana neman sojoji masu sana’a, ni kuma na iya tuka babbar mota, har Bature ya ba ni lasisin tuki, sai aka dauke ni a matsayin kurtu direba a 1967.

Da shiga ta soja sai muka tafi filin yaki, muka gwabza Yakin Biyafara na shekara daya. Bayan yaki ya kare sai muka  dawo Kaduna. Da yake babbar mota nake tukawa kuma aikinmu ba koyaushe ba ne, iyakaci mu je Legas mu dauko kayan yaki masu nauyi, don haka muna iya yin watanbiyu zuwa uku muna zaune ba mu je ko’ina ba. Wannan zaman da muke yi ne ya ba ni dama na yi ta karatu a gida, irin karatun zauren nan har na sauke Alkur’ani a wajen wani mutumin Zariya mai suna Malam Muhammadu. A yawon karatun da nake yi ne har na hadu da Sheikh Abubakar Mahmud Gumi. Ina karatu a gabansa har muka hadu da Sheikh Isma’ila Idris Zakariyya Jos, shi ma yana karatu a wajen Gumi. Ganin cewa ni soja ne sai Abubakar Gumi ya karfafa mini gwiwar yin karatu, inda ya ce me ya sa ba zan samu wata makaranta in shiga ba? Sai na ce masa ai gidan soja ba za su bari ba. Hakan ya sa ya rubuta takarda ya tura wa Runduna ta Daya, ya roke su a kan su tura ni wajen Limamin Soja wanda hakan zai ba ni dama in tafi karatu. Da damar ta samu bayan yaki ya kare ina zaune a Kaduna, sai na tafi Katsina Teachers’ Collage a 1976, na yi Higher Islam, lokacin ana kiran makarantar H.I.S. na yi shekara 4, kafin in dawo Kaduna Kungiyar Izala ta fito kuma sai na samu kaina a ciki. Saboda ni da Isma’ila Idris mun yi karatu tare a wajen Gumi sai ya zama muna da dangantaka ta ilimi muna hulda, ana taron kafa kungiyar a tsakanin  1976 zuwa 1979. Ni kuma na gama makaranta a 1980, da na dawo sai soja suka gane cewa na zama dan Izala. A lokacin Shugaban Limaman Soji, dan Darikar Tijjaniya ne, hakan ya sa muka samu matsala, ya rasa yadda zai yi da ni; a tunaninsa duk inda ya kai ni zan yada Izala. Wannan ya sa na zauna na wasu watanni sai ya ce in je in nemo wata makaranta zai bar ni ina tafi. A lokacin sai na gamu da wani mutumin Gombe, Bappah Muhammad Umar, ya sama min izinin shiga Kwalejin Koyon Aikin Shari’a ta Misau a Jihar Bauchi. Na yi shekara uku, na samu Diploma sai aka mayar da ni wani gari gaba da Kalaba mai suna Abaka, Bataliya ta 41. Ni nake limanci, daga baya muka samu matsala sai aka dauke ni a wajen, aka mayar da ni Bataliya ta 31 a garin Takum a Taraba. Duk da haka da aka ga na dawo Arewa kuma duk inda Izala take wa’azi da ni ake yi a Takum da Ibbi da Donga, sai abin ya dame su, sai aka kira ni Legas don a yi min intabiyu, za a ba ni anini daya; lokacin kuma igiyata biyu ce (Kofur).

Mu 72 aka kira, ni kadai ne soja, sauran duk fararen hula ne aka gayyato su daga makarantu daban-daban. A ciki mu takwas ne muka yi nasara, sai muka je Jaji muka yi kwas, aka daura mana anini. Mu hudu aka daura mana anini daya saboda ba mu da digiri, sauran hudu kuma anini bibbiyu saboda suna da digiri. Daga nan sai na ci gaba da gwagwarmayar neman ilimi da karatu. Hakan ya sa aka yi ta yi mini canje-canjen wuraren aiki har aka kai ni Maiduguri na samu dama na yi digiri a Nazarin  Addinin Musulunci. Wannan ya ba ni dama na yi ta samun karin girma har na zama Laftana Kanar. Zan zama Kanar sai shekarun aikina suka cika 35, sai na rubuta zan bar aiki sai aka ce min in bari sai na daura mukamin Kanar. Aka ce tunda lokaci ya yi zan ajiye aiki.Sai na ce a’a, sai aka ce to an ba ni Kanar tare da yin ritaya a lokaci daya. Hakan ya sa wadansu suke kirana Kanar amma amma ni Laftana Kanar ne.

ADVERTISEMENT

Lokacin da nake Gombe na zama Sakataren Kungiyar Izala, daga baya na zama Shugaban Majalisa ta Bauchi da aka raba Gombe daga Bauchi sai na zama Shugaban Malamai na Gombe gaba daya, inda na yi shekara goma. Na taba zama Shugaban Majalisar Malamai ta Adamawa, lokacin ina aiki tun tana Gongola. Na zama Shugaban Majalisar Malamai ta Katsina, lokacin da nake karatu a H.I.S. Na zama shugaba lokacin ina Ilorin a Barikin Somi, ina Limamin Soja. Da na koma Maiduguri ma ni ne shugaba, na yi shekara hudu. Da na koma Depot a Zariya na yi shekara uku, na zauna a Jaji, inda ake bai wa manyan hafsoshin soji horo; na yi shekara daya da wata takwas, sannan na yi ritaya a shekarar 2005. Bayan na dawo Gombe mun samu rikici a Kungiyar Izala har ta kai aka cire ni aka mayar da ni Mataimakin Ko’odineta na Kasa na Izala, daga baya aka canja ni na zama Shugaban Masallatai na Kungiyar na Najeriya. Ka ji yadda na yi gwagwarmayar neman ilimi ina aikin soja tun daga tukin mota.

Bayan alakarka da Sheikh Isma’ila Idris a wajen Sheikh Abubakar Gumi, yaya aka yi ya zama soja?

Ni ne na sa Sheikh Isma’ila Idris ya shiga soja saboda lokacin da muka hadu a gaban Gumi muna karatu, yana da kaifin basira, ya fi mu fahimta. Sai na dauke shi na kai shi wajen Daraktan Harkokin Addinin Musulunci a Kaduna sai ya ce ya kamata a dauke shi soja, zai taimaka wa addini. A lokacin ne aka dauke shi soja a matsayin Saje. Su takwas suka je kuma shi ne karami a cikinsu, aka bai wa sauran Sitaf-Saje, shi ma ya zama Limamin Soja, daga karshe sauran aka ba su Warrant Officer II; shi kuma ya zama Sitaf-Sajen kuma da wannan mukamin ya bar aiki, har Allah Ya karbi ransa.

Daga Yakin Biyafara ba ku sake zuwa wani yakin ba ne?

Mun je yaki kuma mun je a matsayin masu sa-ido. Bayan gama yaki an kai ni kasar Lebanon amma nan mun je shiga tsakani ne. Da na dawo sai yakin Laberiya ya tashi, nan kuma mun je raba fada ne, sai yaki ya ritsa da mu. Sai ya zama yakin ya koma kanmu sojojin Najeriya, inda muka buga da sojojin Charles Tailor. Nan ma na yi shekara daya na dawo.

Ka ce kun yi yaki da sojojin Charles Tailor, ba ya mika wuya  ba?

Eh, mun yi yaki da shi amma daga baya ya mika wuya da kansa don yin sulhu amma mun fafata da sojojinsa, domin duk inda suke tunanin za su je, sojojin Najeriya sun mamaye wajen; shi ya sa dole ya yi saranda.

A matsayinka na wanda ya je yake-yake a duniya, ga shi yanzu rikicin Boko Haram ya ki karewa; wace gudunmawa za ka iya bayarwa don cin nasarar yakin?

Idan ka lura, mu da muka yi Yakin Biyafara da sauran yake-yake, mu muka san yadda yaki yake. Muna jin mamakin yadda za a ce dan kato-da-gora wato dan Boko Haram zai gagari manyan kasashen Afirka hudu, yau shekara 10 ana bugawa. Gaskiya akwai lauje cikin nadi, dalili kuwa shi ne, Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi duk kasashe ne da suke da zaratan sojoji, sannan mu a Najeriya da muke da sojojin sama da na kasa da na ruwa da kowane irin soja amma dan kato- da-gora da bai da horo kowane iri; a ce ya gagari wanda ya samu horo daban-daban har a kai shekara 10 ana bugawa; akwai abin dubawa.

Yanzu idan aka ce ka sanya kakin soja ka fito filin daga don jagorantar sojoji wajen yaki da Boko Haram za ka je?

Idan aka nemi mu shiga gaba, mu tsofaffin sojoji za mu shiga sannan za mu ba da shawarwarin da in Allah Ya yarda za mu gama da ’yan Boko Haram cikin wata uku kuma Shugaban Kasa ya neme mu ya ga aiki da cikawa.  Sai an nemi Boko Haram an rasa, domin muna da dabarun yaki da muka yi amfani da su wajen cin nasarar yake-yaken da muka yi a baya sannan muna da dauriya da juriya kuma takenmu shi ne ba gudu ba ja da baya. Idan aka karanta mana “Sand Model” sai dai ka ga kawunan ’yan Boko Haram a hannu, wadansu kuma mun kamo su daurarru.

 

  Kanar Adamu Girbo Muhammad (mai ritaya), a fagen daga
Kanar Adamu Girbo Muhammad (mai ritaya), a fagen daga

Wadansu na cewa sojojin ne ba su da horon da ya dace, haka ne?

Ba gaskiya ba ce. Lokacin da na shiga aikin soja horon mako shida kawai na samu kuma na tafi yaki na zama kwararren soja da zan iya korar abokan gaba kamar 30 ni kadai, domin a lokacinmu kowane bangaren soja 12 ne Filatum kuma soja 30, ni kadai zan kori filatum guda tare da mataimakina (2IC).

Wadansu za su ga cewa kai limanci ka yi a gidan, ba ka fafata a fagen daga ba; ta yaya ka zama kwararren soja?  

Ba na gaya maka limancin daga karshe-karshe na shiga ba? Ai ni da na shiga soja sai da na yi shekara 15 sannan na kama limanci. Ba abin da ban yi ba a aikin soja, na shiga rami na yi kwanaki ruwa ya dake ni, na dauko makamai da mota an yi mini fitar burtu na sha a lokacin da na dauko bindogogin yaki daga Owerri zuwa Enugu. Na kuma tsallake tarkon abokan gaba ya fi sau 30. To, mene ne ake nema a soja da ya fi haka?

Wane kalubale ka fuskanta da ba za ka manta ba?

Kalubalen shi ne, akwai lokacin da aka zo yi mana karin girma daga anini biyu zuwa Kyaftin, sai Limamin Rundunarmu ya boye takarduna, ya hana. Shi ya sa za ka ga duk sa’annin aikina a soja sun zama cikakkun Kanar amma ni ina Laftana Kanar. Lokacin da zan yi ritaya aka ba ni Kanar amma kuma ban taba fuskantar kotun soja ba, sai dai an zarge ni cewa ina Musuluntar da sojoji da mayar da su ’yan Izala. Wani abin godiya ga Allah kuma shi ne, na gama aiki lafiya ba ko kwarzanen ciwo.

Share