Da Dumi Dumi

Yadda na zama Lauya ina maraya bayan na shekara 12 a kurkuku – Lauya Edeno

Lauya Akpoghene Edeno
Lauya Akpoghene Edeno

Kwanan nan ne Akpoghene Edeno wanda ya shafe shekara 12 a gidan yari ya samu nasarar zama cikaken lauya, duk da cewa maraya ne shi da ya rasa iyayensa. Ya bayyana wa jaridar The Punch yadda ya yi fadi-tashi har ya kai ga cin ma burinsa.

Labarin yadda aka kama ka kuma aka tuhume ka da laifin kisa, sannan aka tura ka gidan yari har ka shafe shekaru 12 da kuma yadda aka sallame ka har ka zo yanzu ka zama lauya, ya dauki hankalin jama’a. Ko za ka fada mana yadda abin ya wakana?

An kama ni a cikin shekara ta 2000 a kan zargin kisan kai, wanda wani abokina ya aikata. Akwai zargin cewa na san inda ya tafi ya boye, don haka sai na yanke shawara na kai kaina ofishin ’yan sanda don in wanke sunana. Bayan watanni uku sai suka kama abokina din amma kuma sai aka tuhume mu da laifin tare sannan aka tasa keyarmu zuwa kurkuku aka tsare.

A lokacin da aka fara shara’a, Mai Shari’a Marshal Umukoro ya gaggauta shara’ar tamu, bayan duk masu gabatar da kara sun gabatar da hujjojinsu, sai aka juyo kanmu don mu kare kanmu, lauyan mai kare wanda ake zargi na farko ya gabatar da bukatar a kori karar, wanda Alkali Umukoro ya yi watsi da wannan bukata tasa. Amma sai suka daukaka kara a kan hukuncin Umukoro zuwa Babbar Kotu ta Benin.

A Babbar Kotun Benin sai aka rika jan kafa a kan sauraren karar, wanda ya sanya mahaifina, Patrick wanda malamin lissafi ne ya nemi a gaggauta yin shari’ar don muhimmancin yin hakan wajen sanin wane mataki zai dauka. Wanda ake tuhuma na biyu, wato abokina Samson da kuma ni kaina muna amfani da lauyar nan ne da yake kare wanda ake tuhuma na farko a matsayin lauyanmu. Don haka mahaifina a kodayaushe yana tattaunawa da baban Samson don ganin sun samu an saurari karar cikin lokaci a Babbar Kotun.

ADVERTISEMENT

Ku nemi Jaridar AMINIYA don samun cikakken rahoton.

 

Share