✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Najeriya za ta fafata gasar Cin Kofin Duniya na ’yan kasa da shekara 20

A ranar Lahadin da ta gabata ce aka raba rukunan gasar cin Kofin Duniya na ’yan kasa da shekara 20, inda Najeriya ta fada Rukunin D…

A ranar Lahadin da ta gabata ce aka raba rukunan gasar cin Kofin Duniya na ’yan kasa da shekara 20, inda Najeriya ta fada Rukunin D (Rukuni na 4).

A rukunin, Najeriya za ta fafata ne da kasashen Amurka da Ukraine da Katar.

Bikin raba rukunan ya gudana ne a birnin Gdynia da ke kasar Poland, wanda ya samu halartar manyan baki irin su Bebeto da Fernando Couto.

Kasar Poland ce za ta dauki nauyin gasar ta bana, kuma yadda tsarin yake an sanya ta ce a rukunin A, wato rukuni na daya tare da kasashen Kolombiya da Tahiti da Senegal. Kasar Afirka ta Kudu ce ta kasance a cikin rukuni mafi zafi, wanda ake wa lakabi da rukunin mutuwa, inda za ta hadu da kasashen Ajentina da Portugal da Jamhuriyar Koriya a Rukunin F.

Ita ma Mali wadda ta doke Najeriya a wasan karshe na cin Kofin Nahiyar Afirka, tana Rukunin E ne, inda za ta kece raini da kasashen Saudiyya da Faransa da Panama.

Najeriya za ta fara wasa ne a ranar 24 ga watan Mayu da kasar Katar a filin wasa na Stadion Miejski a Tychach.

Najeriya ta kasance daya daga cikin kasashen da suka yi fice a wasannin masu kananan shekaru, musamman a gasar cin Kofin Duniya na ’yan kasa da shekara 17, wadda a duk duniya Najeriya ta fi kowace kasa lashewa, sai kasar Brazil ke biye mata. Haka ma gasar ’yan kasa da shekara 20, wadda duk da cewa Najeriya ba ta taba lashewa, ba za a ce mata kanwar lasa ba, domin manyan kasashen suna tsoron haduwa da ita.

Idan ba a manta ba, tun a gasar ’yan da kasa da shekara 20 ta shekarar 2005 da ta wakana a kasar Holland lokacin ana kiran gasar Youth Championship, inda Ajentina ta lallasa Najeriya da ci biyu da nema, a nan duniya ta fara ganin Messi da Di Maria da sauransu. A wannan gasar, Mikel ne ya kamata ya samu kyautar wanda ya fi iya taka leda, amma kasancewar Messi ya zura kwallo biyu a wasan karshe sai ya doke shi. Wannan ya sa Mikel ya zama na biyu.

Ganin irin ’yan wasa da Najeriya za ta shiga wannan gasa da su, ana tsammanin za su yi abin a zo a gani.

Ga ’yan wasan nan da kuma kungiyar da suke buga kwallo.

Mai horar da ’yan wasa: Paul Aigbogun

Gola: Akpan Udoh ( ba a fada ba); Olawale Oremade (Oasis FC, Legas); Detan Ogundare (Kogi United)

Masu buga baya: Mike Zaruma (Plateau United); Ikouwem Utin (Enyimba International); Igoh Ogbu (Rosenburg FC, Norway); Solomon Ogberahwe (El-Kanemi Warriors); Balentine Ozornwafor (Enyimba International); Olasunkanmi Aliyu (Emmanuel Amuneke Academy)

’Yan wasan tsakiya: Peter Eletu (Prince Kazeem Academy); Kuadri Liameed (36 Lions); Aniekeme Okon (Akwa United); Jamil Muhammad (Kano Pillars); Afeez Aremu (IK Stat, Norway)

’Yan wasan gaba: Adamu Alhassan (Kano Pillars); Yahaya Nazifi (Sonderjyske FC, Denmark); Ibrahim Aliyu (Oasis FC); Adeshina Gata (Wikki Tourists); Ibrahim Abubakar (Plateau United); Okoh Bictor (Real Sapphire FC) da Madwell Effiom (Enyimba International).