✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Najeriya za ta shiga harkar kiwon lafiya ta na’ura a duniya – Farfesa Dambatta

NCC na ciga da hadin gwiwa da asibitocin koyar wa Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Sadarwa ta Najeriya (NCC) Farfesa Umar Garba dambatta ya bayyana…

NCC na ciga da hadin gwiwa da asibitocin koyar wa

Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Sadarwa ta Najeriya (NCC) Farfesa Umar Garba dambatta ya bayyana cewa, Najeriya za ta bi sahun sauran kasashe a ci gaban da ake samu a fannin kiwon lafiya ta na’ura.

dambatta, ya bayyana ayyukan ci gaban da hukumar ke yi na kawo sauyi a fannin fasahar kimiyya da ake samu a kasar nan, don haka ya bukaci a kaddamar da cibiyoyin bayanan jama’a a shiyyoyin kasar nan  zuwa babbar cibiyar a Hukumar Bayar da Katin Shaidar Zama dan kasa, (NIMC).

Shugaban NCC ya bayyana haka ne lokacin karbar ayarin wadanda suka ziyarce shi daga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja wanda Shugaban masu ruwa-da-tsaki na asibitin Dokta Sam Jaja  da Babban Daraktan Asibitin Farfesa Bisallah Ahmed Ekele, suka jagoranta don kai ziyarar aiki zuwa hedkwatar Hukumar NCC a Abuja.

“Muna tafiya daga wani mataki zuwa wani na sauya kasar nan zuwa matakin fasahar kimiyya, za a samu nasarar haka ne idan an bi matakai daya bayan daya. Lokaci zai zo da kowa zai yi amfani da Intanet, idan za a shigar da bayanan mara lafiya a tura zuwa wani asibiti. Sai dai a danna alama daya kawai za ta bankado tarihin wanda ake bincike.

Yayin da marar lafiya zai fita daga kasar nan zuwa kasashen waje don yin jinya ba a bukatar takardun da ke bayyana abin da ke cutar da marar lafiya a ci gaban fasahar sai dai kawai shigar da sunan mai jinyar ta hanyar na’urar kwamfuta don sanin abin da ke damun mai jinyar duk wannan na cikin amfani da na’urar kiwon lafiya da za a ci gaba da amfana nan gaba.

dambatta ya kara da cewa, amfani da fasahar sadarwa zai taimaka wajen tabbatar da shigar da bayanai da saurin binciken cutar da ke damun marar lafiya don yin magani a asibitocin kasar nan.

Gudunmawarmu na hada kan jami’o’in kasar nan a kan wasu ayyuka da za su hada jami’o’in wuri guda, za ta zama wata hanya mafi saurin samun sadarwa a tsakanin jami’o’in. Asibitocin koyarwa na jami’o’in kasar nan sun fi muhimmanci a kan wannan aikin da aka sanya a gaba. Yayin da akwai cibiyoyin shigar da bayanan abubuwa mafi muhimmanci da aka aiwatarwa wadanda suka hada da: wajen adana bayanan dalibai da bayanan sakamakon karatu da bayanan kiwon lafiya da sauran bayanan wadanda ajiye kwafin takardun zai zama wani abu mai wahala. Mun yanke shawarar cewa, za a kaddamar cibiyoyin tattara bayanai a jami’o’in kasar nan kamar jami’ar Abuja don a samu sahihan hanyar ajiyar bayanai wanda za a iya binciko abin da ake bukata,” in ji dambatta.

A jawabin Dokta Jaja ya gode wa Shugaban Hukumar  NCC a kan kokarin da suke yi wa asibitocin kasar nan. Babban Daraktan Asibitin Farfesa Ekele, ya ce, shirin NCC na ba da gudunma wa ga cibiyoyin lafiya abu ne na farko da ya fara maraba da shi tun shekara 25 da suka gabata.