✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda nake aikin daukar hoto da shirya fim – A’isha Shehu Kaikai

A wani faifan bidiyo da kafar labarai ta BBC ta wallafa inda ta zanta da wata Bahaushiya mai shirya fina-finai a kasar Amurka mai suna A’isha…

A wani faifan bidiyo da kafar labarai ta BBC ta wallafa inda ta zanta da wata Bahaushiya mai shirya fina-finai a kasar Amurka mai suna A’isha Shehu Kaikai.

A’isha Shehu Kaikai, wacca take aikin daukar hoto da shirya fina-finai ta bayyana cewa sha’awa ce kawai take yi, kuma ta samu goyon bayan iyayenta matuka.

A cewarta, “Ni mai daukar hoto ce kuma mai shirya fina-finai, kuma ina da kungiyar taimakon marasa galihu kuma ina kirkirar shafin yanar gizo.”

A’isha Shehu Kaikai wadda ’yar asalin Jihar Katsina ce, ta bayyana irin nasarori da kalubalen da take fuskanta a yayin da take a bakin aikinta.

“Mutane na yi mini wani irin kallo na cewa ni mace ce. Wani lokaci idan na je aiki sai su rika tunanin ko su rika ganin kamar ba zan iya ba, musamman a fannin daukar hoto ko shirya fim, amma kuma sai na gama kuma sai su rika mamaki suna yabawa. Suna mamaki wai mace na aikin maza,” inji ta

Game da samun goyon bayan iyaye kan bangaren da ta dauka kuwa, A’isha ta ce, “Na samu goyon bayan daga iyayena a duk mataki na rayuwa. Kasancewata mace bai hana ni samun goyon bayan da nake bukata ba.”

A karshe A’isha ta shawarci mata cewa su dage wajen neman ilimi sannan su dogara da kansu, kada su yarda cewa wata sana’a ta maza ce kawai domin duk abin da suke so za su iya.