✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda nake hada kasuwanci da waka – MD Anas

Aminiya ta zanta da wani matashi kuma fitaccen mawakin Hausa a Jihar Kaduna mai suna Muhammad Anas Abubakar wanda ake masa lakabi da Ali Nuhun…

Aminiya ta zanta da wani matashi kuma fitaccen mawakin Hausa a Jihar Kaduna mai suna Muhammad Anas Abubakar wanda ake masa lakabi da Ali Nuhun Kaduna. Matashin wanda kuma dan kasuwa ne, ya bayyana yadda yake hada kasuwancinsa da harkokin waka da fim. Da yadda a haka har ya kammala karatunsa na digiri a jami’a. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Mene ne tarihinka a takaice?

Da farko sunana Muhammad Anas Abubakar  amma an fi sanina a harkar waka ko fim da MD Anas. Na fara karatu a makarantar Silber Bell Nursery, Primary and Secondary School da ke Kawo a Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa a Jihar Kaduna. A gefe daya kuma ina Makarantar Islamiyya ta Madarasatul Elhasan Sa’adatul Abadiyya a Kawo. Sai na yi firamare a Makarantar ’Ya’yan Sojoji (Army Children School New Cantonment da ke Barikin Kotoko, NDA, Kaduna. Sai sakandare a makarantar Dokta Ahmad Makarfi Secondary School a Unguwar Hayin Banki. Daga baya na je makarantar Best Start Comprehensibe College da ke Mando, Kaduna, inda na kammala sakandare. Daga nan na tafi Jami’ar Jihar Kaduna, na yi digiri na farko, kuma na yi wa kasa hidima a Jihar Kogi. Yanzu haka ina shirye-shiryen komawa karatu domin YIn digiri na biyu. Sannan a daya gefen, na ci gaba da karatun Islamiyya a makarantar Hayatul Islam da ke Hayin Banki. Yanzu ni  dan kasuwa ne da ke tafiye-tafiye zuwa jihohi kuma ina yin harkokin waka da fim.

Me ya ja hakalinka ka fara harkokin waka da fim?

A gaskiya na fara shiga sutudiyo domin in yi waka ce a shekarar 2007 ko 2008. Kuma abin da ya ja hankalina shi ne tun lokacin da nake firamare na fara sha’awar waka bayan da na kalli fim din Sangaya, inda wakokin fim din suka burge ni, haka shi ma fim din ya kayatar da ni. To tun lokacin nake da sha’awar waka.

Wakokin kawai kake yi ko kana hadawa da fim?

Ni dai mawaki ne a masana’antar Kannywood, amma kuma nakan hada da harkar film din.

Ko za ka tuna wakokin nawa ka yi zuwa yanzu?

Ina da wakoki akalla za su wuce 100, domin na manta da wasu kasancewar na dan dade a harkar, musamman idan ba wakokin da suke kundin da ka fitar ba. Amma dai a cikinsu na saki albam wato kundi a kasuwa guda biyu wadanda sun kunshi wakoki da dama. Akwai wanda na yi wa suna APC Karen Bana, wanda ya kunshi wakar da na yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da sauran wakoki da kuma kundina na kowa da gwaninsa wanda ya kunshi wakokin soyayya ne da fadakarwa da nishadantarwa.

A cikin wakokinka ko akwai wadda ka fi so, kuma me ya sa?

Gaskiya akwai wakar da na fi so. Kuma wannan wakar ita ce ‘Tantabara,’ dalili kuwa shi ne budurwar da zan aura na yi wa wakar. Kuma ka san duk inda ka ji an ce Tantabara, Hausawa sukan ce uwar alkawari.

Ko kana da wani ubangida a harkar waka?

Gaskiya ba ni da wani takamaiman ubangida a harkar waka, sai dai ina da mashawarta wadanda nake tuntuba tare da neman shawararsu idan bukatar haka ta ta so. Ka san mutum bai zama wani, ko ya zama wanda za a bi, sai in shi ma ya kasance mai biyayya ga na gaba. Don haka nake shawara da na gaba.

Na ji ana kiranka Ali Nuhun Kaduna, me ya jawo ake kiranka da wannan suna?

Kirana da suna Ali Nuhu, ya samo asali ne tun daga makarantar sakandare. A lokacin ina mamba a Kulob din Hausa, inda duk lokacin da muke harkokinmu nakan yi kokari in kwaikwayi yadda Ali Nuhu yake yi. Ka san na fada maka cewa tun daga fim din Sangaya na fara sha’awar waka da fim. Ka ga ke nan ba abin mamaki bane idan na kwaikwayi Ali Nuhu. Haka kuma wadansu mutane suna cewa muna yanayi da shi watakila saboda yanayin tsayi da launin fata.

Mene ne burinka a harkar waka?

Burina kamar kowane mawaki shi ne Allah Ya yi min nasibi da ludufi in samu daukaka a harkar fiye da yadda nake a yanzu. Kuma ina da burin ganin mu bunkasa harkar ta yadda za ta yi gogayya da sa’o’i masu irin wannan sana’ar a duniya irin su Indiya.

Wace riba ka samu tun fara wannan sana’a?

Alhamdulillah, na samu riba da yawa a wannan harka domin zan iya cewa da taimakon wannan sana’ar na samu na yi karatu har zuwa matakin jami’a har na kammala. Na kuma san jama’a, jama’a sun san ni a dalilin wannan harka domin wakokina sun je inda ban je ba. Da yawa idan na je waje da an ji sunana sai ka ji ana ga MD Anas. Sannan ina da rufin asiri da ba abin da zan ce sai godiya ga Allah. Haka kuma ta taimaka min a bangaren kasuwancin da nake yi. Sannan kuma ina cikin mawakan APC da aka gayyata domin nuna godiya gare su bisa irin gudunmawar da suka bayar waje zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a zaben 2015, wanda Gwamnatin Jihar Kaduna a karkashin Malam Nasir El-Rufa’i ta shirya. A takaice dai ina godiya ga Allah.

Kasancewarka dan kasuwa, yaya kake hada harkokin biyu?

Babban sirri shi ne, ilimi da juriya. Ilimi zai taimaka maka wajen tsara lamuranka yadda ya dace, sannan juriya za ta taimaka maka wajen hakuri har hakarka ta cimma ruwa. Ai ban da wadannan harkokin biyu, na kasance ina karatun jami’a, ka ga ke nan lokacin na hada harkoki manya guda uku ke nan. Amma duk da haka ban yi sanyi a gwiwa ba, na ci gaba da kokari, har na kammala karatuna, na yi hidimar kasa, sannan yanzu ina da niyyar komawa makaranta domin in yi digiri na biyu. Idan ba don juriya ba da kuma iya tsara lamura da abin ba zai yiwu ba. Kuma wani sirrin, wanda ke gaba da wadanda na ambata shi ne dogara ga Allah. Duk abin da mutum zai yi, yana da kyau idan ya yi azama, sai kuma ya dogara ga Allah. Amma gaskiya ina ba kowane muhimmanci, kuma wani bai shiga cikin wani, ballantana ya kawo min cikas. Da kuma uwa-uba; addu’ar iyaye da ’yan uwa da abokan arziki.

Wace shawara za ka ba mawaka ’yan uwanka?

Shawarata ga mawaka ’yan uwana ita ce, mu so juna da rikon amana, musamman a wakar siyasa, kada ka rika waka kana cewa wadansu barayi ne kai kuma a ba ka kudin mawaka ka cinye. Ya kamata kuma mu daina wakokin cin mutuncin juna, sannan mu rika girmama juna tare da bin na gaba. Duk wanda bai bi wani ba, shi ma ba za a bi shi ba. Su kuma manyan mawaka su daina rainawa da danne na kasa da su, domin ita duniya juyi-juyi ce. Idan yau kai ne, watakila gobe ba kai ba ne. Kuma Hausawa suna cewa zamani riga.

A bangaren gwamnati kuwa, muna bukatar a tallafa mana ta wajen bunkasa kasuwancin wakokinmu zuwa babban mataki kamar yadda Obasanjo ya yi wa mawakan Kudancin kasar nan a lokacin da yake mulki. Yau ga shi suna gogayya da sa’o’insu na duniya.