✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda nake hada koyarwa da fitowa a shirin ‘Dadin Kowa’ – Madam Gloria

Esther Smart wadda aka fi sani da Madam Gloria tana daya daga cikin manyan jarumai a shirin ‘Dadin Kowa Sabon Salo’ da ake nunawa a…

Esther Smart wadda aka fi sani da Madam Gloria tana daya daga cikin manyan jarumai a shirin ‘Dadin Kowa Sabon Salo’ da ake nunawa a tashar talabijin ta Arewa24. Duk da kasancewarta Bayarabiya ta tana taka muhimmiyar rawa a shirin. A hirarta da Aminiya, jarumar ta bayyana dalilin da ya sa ta fara harkar fim da yadda take hada koyarwa da fitowa a shirin fim na ‘Dadin Kowa’ duk da cewa ita ba Bahaushiya ba ce:

 

Wace ce Madam Gloria?

Cikakkaken sunana Esther Smart, ni Bayarabiya ce ’yar asalin Jihar Osun, amma an haife ni a Kaduna. Ina kuma da shekara biyar mahaifana suka dawo Kano da zama, a Kano na yi karatu har na kai matsayin da nake koyarwa a makarantar Treasure Life International Academy da ke Kano. Ina da aure da ’ya’ya uku.

 

Me ya ja hankalinki  kika fara harkar fim?

Wannan tafiya tawa ta harkar fim ta fara ne tun ina makarantar sakandare, domin a lokacin ni mamba ce a kungiyar dirama, inda ma har na zama shugaban kungiyar, to tun a wancan lokacin nakan yi wasan dabe, haka bayan na kammala makarantar sakandare ma nakan yi wasan dirama na coci, haka  wani lokaci da aka samu aikin cewa cocinmu zai shirya wani fim, a nan aka kira ni aka ce in zo in fito a fim din.

Daga baya sai na shiga Kungiyar Jarumai ta Najeriya (AGN), saboda daraktan da ya ba da umarni a fim din da cocinmu ya dauki nauyi dan kungiyar AGN ne, na yi fina-finai guda biyu ma kafin in fara fitowa a shirin fim na ‘Dadin Kowa’.

 

A fim din kina fitowa a muguwar mata ko mai zafin rai, shin da ma haka halinki yake a zahiri?

A gaskiya ba haka halina yake ba, domin yawanci idan na hadu da mutane a zahiri bayan alaka ta hada mu sai ka ji suna cewa ashe da ma haka nake, domin ina nan shiru-shiru, amma a fim kullum cikin zafi.

 

Yaya aka yi kika samu sunan Madam Gloria?

Wannan suna ne na fim kawai, suna ne da aka ba ni a shirin talabijin na Arewa24, inda nake da ’ya Stepahanie a fim din.

 

Me ya sa kika zabi fitowa a fina-finan Arewa24 maimakon na masana’antar Kannywood?

A gaskiya na ji cewa tashar talabijin ta Arewa24 za ta fara shirya fina-finai ne, sai na rika bin diddigin batun, inda ranar da aka zo tantance wadanda za su fito a shirin wato auditioning, sai na zo wurin da ake tantancewar, inda aka ba ni labarin fim (script), na karanta kuma na gwada abin da na karanta din. A wannan lokaci ba ni kadai aka kira tantancewar ba, amma daga karshe Allah Ya ba ni nasara aka zabe ni a matsayin daya daga cikin jaruman shirin Dadin Kowa na tashar Arewa24.

Kuma abin da ya sa har yanzu nake ci gaba da fitowa a shirin shi ne idan aka duba ana yin fim ne a kan abubuwan da suka shafi al’umma, ba wai kawai a kan nishadantarwa ba. Bayan na shiga harkar sosai sai na kara samun gamsuwa shiri ne a kan abubuwan da suka shafi jama’a kai-tsaye, ba wai kawai nishadi ba. Shiri ne da ke wayar da kan jama’a a kan illar kabilanci da kuma sauran miyagun ayyuka.

 

Yaya kike ji da yake kina fitowa a shirin da Hausa ne amma ke ba Bahaushiya ba ce?

Babu wata matsala, duk da cewa ni ba Bahaushiya ba ce, amma ji nake kamar a gida nake, domin ana nuna mini soyayya, ina jin cewa fitowar da nake a shirin ma kamar wata hanya ce ta hada kan kabilun kasar nan. Hakan ya nuna cewa idan za mu hada kanmu, mu fahimci bambance-bambancen da ke tsakaninmu to kasar nan za ta samu bunkasa da habaka. Idan aka lura a cikin shirin za a ga cewa ina caccakar masu nuna kabilanci.

 

A yanzu idan aka kira ki don ki yi fim a Kannywood za ki amince?

Eh zan amince duk da cewa ya danganta da irin rol din da aka bukaci in yi, zan amince ko da a Nollywood ne ba kawai Kannywood ba, domin ina da yakinin duk matsalolin da ake samu a kasar nan tsakanin kabilu da addinai dalilin rashin fahimta ne. Kuma na tabbatar idan muka fahimci bambancin da ke tsakaninmu ta hanyar fina-finai zai taimaka a magance matsalar rikice-rikice da fadace-fadace a nan da can a kasar nan.

 

Yaya kike hada koyarwa da fitowa a shirin ‘Dadin Kowa?

Ina tsara komai nawa daki-daki, kamar a Arewa24 duk lokacin da ake bukata ta sukan fada mini mako guda kafin ranar. Sai in dauki script dina in karanta, daga nan idan akwai bukatar wani ya taimaka mini a wurin aiki sai in sa shi, idan kuma babu bukatar hakan shi ke nan, idan kuma lokacin da ake bukata ta bai shafi aikina a makaranta ba, sai in je makaranta daga nan in wuce wurin daukar shirin.

Haka nakan tabbatar da komai ya daidaita a gida kafin in fita aiki, nakan sanar da iyalina cewa a wannan makon zan fita aikin shirin fim, don haka kowa zai shirya wa hakan, kuma ina gode musu domin suna taimaka mini, iyalina da sauran jama’ata a wurin aiki sun taimaka mini sun sanya komai yana zuwa mini da sauki.

 

Ko za ki bar ’yarki ta shiga harkar fim idan ta bukaci hakan?

Zan bar ta idan har tana da sha’awar haka, za ta zama jaruma ta kuma rika hada fitowa a fim da wasu ayyukan, tunda ni ma hakan nake yi, komai ya danganta da sha’awa ce idan tana son fim ba zan hana ta fitowa a ciki ba.

 

Ko kina da wata shawara ga jama’a?

Daga farko ina so mutane su rika mutunta addinan juna, kada mu rika zagin addinan juna. Idan ka mutunta addinin wani, to shi ma zai mutunta naka. Sannan dangane da mutane da ake safararsu zuwa kasashen waje ina kiransu da su nemi aikin yi, domin idan suka samu aikin yi babu wanda zai yaudare su ya ce zai kai su kasashen waje don su samu aiki.