Aminiya

Yadda Obasanjo ya gana da shugabannin Kungiyar Fulani ta Gan Allah a Abeokuta

A ranar Asabar da ta gabata ce tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo ya yi taro da shugabannin Kungiyar ci Fulani Makiyaya ta Gan Allah Fulbe da arakunan Fulanin  jihohin Kudu maso Yamma da na jihohin Kwara da Kogi inda suka shafe sama da awa biyar suna ganawar sirri domin lalubo mafita a rigingimun Fulani makiyaya da manoma da kuma tabarbarewar tsaro da ake alakantawa da Fulani makiyaya.

Shugaban Kungiyar Fulani ta Gan Allah Fulbe ta Kasa, Alhaji Sale Bayeri ne ya jagorancin Fulanin a lokacin taron, kuma ya shaida wa Aminiya cewa, Cif Olusegun Obasanjo ne ya nemi su da kansa domin su tattauna matsalolin da ke addabarsu don lalubo bakin zaren. Ya ce tsohon Shugaban Kasar ya nemi ganawa da shi ne a karo na farko bayan ya ga wani rubutu da ya yi a wata jarida, “Da ya ga rubutun da na yi a jarida sai ya neme ni ta hanyar wani babban manajansa. Da na zo muka tattauna da shi na fayyace masa halin da mu Fulani makiyaya muka samu kanmu a ciki, nan shi ma ya nuna damuwarsa kwarai sai ya bukaci mu zo mu zauna mu tattauna domin lalubo bakin zaren. Ya kuma amince da in zo da shugabannin Fulani na wannan kungiya tamu na jihohin Kudu maso Yamma da jihohin Kwara da Kogi da sarakunan Fulanin yankin inda kowace jiha daga jihohin 8 suka samu wakilcin mutum 3. Mun sanya jihohin Kwara da Kogi ne lura da kamanceceniyarsu da jihohin Yarbawa a al’adance domin matakan da aka dauka na warware matsalolin a jihohin Yarbawa za su yi aiki a jihohin Kwara da Kogi,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Ya ce, sun kwashe sama da sa’a biyar suna tattaunawa da Obasanjo, sun kuma tattauna muhinmman batutuwa sannan za su yi aiki da shawarwarin da ya ba su kuma za su dawo bayan kwana 90 domin a tattauna kan ci gaban da aka samu. “Bayan gabatar da taron Cif Obasanjo ya sallami ’yan jarida ya ce su fita su ba mu waje mu yi taronmu da shi, don a cewarsa taro ne na ’yan uwan juna, kuma ya ce ranar wanka ba a boyon cibi don haka mu fayyace masa duk halin da ake ciki, kuma mun yi na’am gare shi domin shi dattijo ne uban kasa da ba a yankin Yarbawa kadai ba a ko’ina ana sauraron maganarsa,” inji shi.

A nasa bangaren Cif Obasanjo ya sha alwashin ci gaba da tattaunawa da Fulani makiyaya domin kawo karshen rikicin da ake alakanta su da shi. Taron ya samu halartar Sakataren Kungiyar Yarbawa ta Afenifere, Yinka Odunmakin wanda ya shaida wa Aminiya cewa, kungiyar a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da Kungiyar Fulani ta Gan Allah Fulbe domin sun yi amanna da salonsu, “In ka lura a makon jiya ma tsohon Shugaban Kasa Janar Abdulsalami ya gayyace mu irin wannan taro amma mun janye ne saboda shugabanin kungiyar Fulani makiyaya da muka gani a wajen domin ba mu aminta da salonsu ba,” inji shi.

ADVERTISEMENT