✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Ranar Makewayi ta gudana a Jihar Oyo

Ranar 19 ga Nuwamban kowace shekara rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe a matsayin Ranar Makewayi ta Duniya, wacce ta zo daidai da…

Ranar 19 ga Nuwamban kowace shekara rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe a matsayin Ranar Makewayi ta Duniya, wacce ta zo daidai da ranar Talata da ta gabata. Wakilinmu a Jihar Oyo ya duba yadda mutane suke yin ba-haya a kan hanyoyin birnin Ibadan wanda shi ne birni mafi girma a Afirka ta Yamma ba tare da lura da irin cututtukan da suke haifarwa ga rayuwarsu ba.

Bincike ya nuna cewa, kashi 90 cikin 100 na gidajen da aka gina a cikin birnin Ibadan an gina su ne ba tare da makewayi ba. Wannan bincike ya tsaya ne kawai a cikin birni ban da gidajen masu hali da ake ginawa a wajen gari. Tun a wancan lokaci mahukunta suka dauki matakan tilasta gina makewayi a kowane gida wanda hakan ya sa aka bullo da salon kebe wani wuri da ake gina dakali daga cikin gida mai karamin rami da ake ajiye bokiti a karkashinsa a bayan katangar gida wanda ake amfani da shi a wasu gidaje. Akwai ma’aikatan kwashe irin wannan kazanta wadanda suke zuwa cikin dare bayan sun lullube fuskokinsu suna kwashe kazantar daga cikin bokitai a kullum. Wannan sabon salo da mahukuntan suka bullo da shi bai yi wani tasiri ba, domin mutane sun ci gaba da tsugunnawa da rana tsaka a kan hanyoyi da bola suna yin ba-haya a bayyane.

Hatta a kan manyan hanyoyi an ci gaba da gudanar da wannan mummunar al’ada. A wasu lokuta ma wadansu mutane sukan yi ba-haya a gidajensu su kunshe a takarda ko leda su rika jefarwa a kan hanya.

Gwamnatocin baya sun kafa tsauraran  dokoki domin hukunta masu gina gidaje a cikin birni ba tare da makewayi ba. Kuma jami’an duba-gari sun yi ta kama mutane da laifin tsuguno a kan hanya amma har yanzu an kasa samo mafita.

Wakilinmu ya zagaya wasu sassan birnin Ibadan a sanyin safiyar ranar Talata da ta gabata wacce ta yi daidai da ‘Ranar Makewayi ta Duniya’ inda ya gane wa idonsa yadda mutane ke fitowa suna tsugunno a kan hanya.

Tope Abiola, mai shagon sayar da abinci a Unguwar Oke-Padre cewa, ta yi, “Ka ga shagon da nake sayar da abinci a kusa da wurin ne kuma ake zuwa ana yin bayi. Babu yadda zan iya domin ba zan iya hanawa ba. Gwamnati ce ke da alhakin hana yin wannan abin haushi da ke haifar da cuta ga mutane.” Shi kuwa Taiye Babalola cewa, ya yi, “Ya kamata mu da kanmu da muke gudanar da harkokin kasuwanci a wurare irin wadannan da suke da kusanci da kogi mu dauki matakin hanawa kafin mu jira gwamnati ta yi mana, domin irin wannan al’amari babu kyau ko kusa kuma abin kunya ne.”

Binciken ya nuna cewa, akwai karancin gidajen wanka da bayi a birnin Ibadan wanda hakan ya taimaka wajen ci gaba da samun masu yin bayi a kan hanya.

Wakilinmu ya tuntubi Babban Jami’in Sadarwa a Ma’aikatar Tsabtace Muhalli ta Jihar Oyo Mista Abiodun Atilola, wanda ya ce “Kwamishinan wannan ma’aikata ne ya jagoranci jami’ansa domin yekuwar girmama ‘Ranar Makewayi ta Duniya’ a Ibadan kuma tun kafin wannan lokaci muka dauki matakin tabbatar da tsabtace muhalli a dukkan kananan hukumomi 33 na Jihar Oyo. Wannan yekuwa ce ta jan kunnen jama’a su rika tsabtace muhalli a ciki da wajen gidajensu domin kare kansu daga kamuwa da cututtuka. Mun aika da jami’an duba gari zuwa sassa daban-daban musamman zuwa bola da magudanun ruwa don kama duk wanda ya taka dokar yin bayi a kan hanya,” inji shi.

Da yake karin haske a kan ‘Ranar Makewayi ta Duniya’ Kwamishinan Ma’aikatar Tsabtace Muhalli ta Jihar Oyo Mista Kehinde Ayoola, ya ce gwamnati ta kammala shirin samar da makewayi tare da samar da wadataccen ruwa a ko’ina cikin a jihar. Kwamishinan ya fadi hakan ne a zantawa da ’yan jarida a Ibadan. Ya ce, wannan muhimmin aiki ne na hadin gwiwa a tsakanin ma’aikatarsa da Ma’aikatar Samar da Ruwa ta Jihar inda za su yi fafutikar yaki da ba-haya a kan hanya.