✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rashin fitowa zabe ke shafar sakamako zabe

A gobe ne ’yan Najeriya za su fita rumfunan zabe don zaben Shugaban Kasa da wakilan Majalisar Dokoki ta Kasa da za su jagoranci kasar…

A gobe ne ’yan Najeriya za su fita rumfunan zabe don zaben Shugaban Kasa da wakilan Majalisar Dokoki ta Kasa da za su jagoranci kasar nan a shekara  hudu masu zuwa.

Binciken Amniya kan bayananan zabubbukan da suka gabata a shafin yanar gizo na Hukumar INEC ya gano cewa wadanda suka kada kuri’a ba su  wuce kashi 55.2 cikin 100 na wadanda ya kamata su kada kuri’a ba.

Binciken ya gano cewa kashi 52.3 cikin 100 ne kawai suka yi zabe a 1999.

Sannan aka samu karin masu zabe a shekarar 2003 da kashi 69.1 cikin 100, sai adadin ya koma baya a zaben shekarar 2017 da kashi 57.4. A zaben shekarar 2011 kuma an samu kashi 53.7 cikin 100, sai  zaben 2015 da aka samu kashi 43.6 cikin 100 suka kada kuri’a.

Tsakanin zaben 1999 zuwa na shekarar 2019, masu zabe a Najeriya sun karu daga mutum miliyan 57 da dubu 938, da 945 zuwa miliyan 84 da dubu 4 da 84.

A zaben shekarar 1999, yankin Kudu maso Kudu ne ke da ingantattun kuri’ar da aka kada da miliyan 4 da dubu 227 da 330, sai Arewa maso Yamma da kuri’a  miliyan 3 da dubu 884 da 836, sai Arewa ta Tsakiya mai kuri’a 3 da dubu 615 da 793, sai Arewa ta Gabas mai kuri’a miliyan 3 da dubu 552 da 353, sai Kudu maso Gabas, miliyan 2 da dubu 307 da 772 sai kuma Kudu maso Yamma da kuri’a miliyan 1 da dubu 902 da 196.

A zabe na karshe da aka gudanar a shekarar 2015. Yankin Arewa maso Yamma ke kan gaba da kuri’a miliyan 8 da dubu 505 da 577, sai Kudu maso Kudu da kuri’a miliyan 4 da dubu 667 da 879, sai Kudu maso Yamma da kuri’a miliyan 4 da dubu 362 da 456, sai Arewa ta Tsakiya da kuri’a miliyan 4 da dubu 149 da 143, sai Arewa maso Gabas da kuri’a miliyan 3 da dubu 672 da 348, sai Kudu maso Gabas da kuri’a miliyan 2 da dubu 719 da 167.

A tarihi ’yan Najeriya ba su cika fitowa zabe ba, inda a  zaben 1999, duk da cewa akwai masu rajista miliyan 57 da dubu 938 da 945, kuri’a miliyan 30 da dubu 280 da 52 kawai aka kada, wato kashi 52.3.

Haka abin ya kasance a zaben 2003, inda aka kada kuri’a miliyan 42 da dubu 18 da 735 daga cikin masu rajista miliyan 60 da dubu 823 da 22.

A shekarar 2007, an kada kuri’a miliyan 35 da dubu 419 da 262 daga cikin kuri’a miliyan 61 da dubu 566 da 648 da ke cikin rajista, wato kashi 57.4 ke nan.

A 2011 an kada kuri’a miliyan  39 da dubu 469 da 484 daga cikin miliyan 73 da dubu 528 da 40 da ke cikin rajista.

A zaben 2015 kuma, abin ya fi komawa baya, inda kashi 43.6 ne kawai suka kada kuri’a, inda mutum miliyan 29 da dubu 432 da 83 kacal suka kada kuri’a, daga cikin miliyan 67 da dubu 422 da 5 da ke cikin rajista.

Ko za a samu sauyi a zaben bana?

A zaben bana, Hukumar INEC ta yi rajistar masu kada kuri’a  miliyan 84 da dubu 4 da 84. Kuma akwai akalla ’yan takara dubu 20, da suke neman kujeru daban-daban, wanda shi ne mafi yawa a tarihin zabe a  kasar nan.

A ciki akwai masu neman Shugaban Kasa 73, masu neman sanata 1,800, sai masu neman Majalisar Wakilai 2,600. Sannan akwai ’yan takara 14,000 masu neman kujeran majalisun jihohi 991.

Shugaban Kasa dai guda daya kawai zai samu nasara, sannan Majalisar Dattawa na da sanatoci 109, sai ta wakilai guda 360.  Majalisun jihohi kuma akwai gurabe 991.

Sannan kuma binciken Aminiya ya gano cewa ’yan takara 81 ne suka taba neman takarar Shugaban Kasa a Najeriya tun zaben 1999 zuwa zaben 2015.