✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rasuwar Ali Namani Kotoko Sarkin Noman Najeriya ta girgiza jama’a

A ranar 13 ga Yulin nan ne Allah Ya amshi ran Sarkin Noman Najeriya Alhaji Ali Namani Kotoko Wasagu a asibitin Saraki Special da ke…

A ranar 13 ga Yulin nan ne Allah Ya amshi ran Sarkin Noman Najeriya Alhaji Ali Namani Kotoko Wasagu a asibitin Saraki Special da ke garin Sakkwato. Rasuwar marigayin ta girgiza dubban mutane a Jihar Kebbi, musamman manyan attajirai da manoma da jami’an gwamnati da sauran jama’a.
Da yawa daga cikin ’yan kasuwa a manyan kasuwannin Wasagu da Bena da Ribah da Zuru sun rufe shagunansu jim kadan da samun labarin rasuwarsa, yayin da ma’aikatan gwamnati suka tashi daga aiki kafin lokacin tashi, domin nuna bakin cikinsu a kan wannan babban rashi da Jihar Kebbi da kuma Najeriya suka yi.
Farfesa Abdullahi Abdu Zuru, Shugaban Jami’ar Jihar Kebbi da ke garin Aliero (sabon Shugaban Jami’ar Usman dan Fodiyo da ke Sakkwato) ne ya jagoranci manyan ma’aikatan gwamnatin jihar zuwa gidan marigayi da ke garin Wasagu a karamar Hukumar Danko-Wasagu dominn ta’aziyya ga iyalan mamacin.
Marigayi Alhaji Ali Namani Kotoko mai shekara 102 ya rasu ya bar matan aure 4 da ’ya’ya 20, maza 7 da mata 13 da jikoki 110.
daya daga cikin manyan aminan marigayi Sarkin Noman, Alhaji Gareci Sallaman Wasagu, ya shaida wa wakilinmu a garin Wasagu cewa marigayi Alhaji Ali Namani Kotoko ya fito ne daga garin Shimfida da ke karamar Hukumar Jibiya da ke Jihar Katsina, kuma ya zo kasar Wasagu ne a matsayin mai wasan Nakiya da Garma. Ya ce ya fara zama ne a wani gari da ake kira Garewa domin duk Katsinawa ne a cikin garin daga baya ne ya dawo cikin garin Wasagu ya zauna.
“A lokacin da ya zo Wasagu yana tare da yaransa masu yi masa kidi yana wasa da garma kusan yaransa 24 a lokacin masu yi masa kida, bayan wannan kuma yana sana’ar alewa yana sayarwa, idan za a yi gasar noma a duk fadin Jihar Sakkwato sai an gayyato shi, haka na nuna amfanin gona.
Ya ce akwai wata rana da marigayi Sardaunan Sakkwato Alhaji Ahmadu Bello (Allah Ya jikansa) ya gayyace shi gonarsa ta Bakura wajen gasar noma. To shi Ali Namani Kotoko ne ya zo na daya, inda Sardauna ya ba shi kyautar kofi, ya ce masa idan ya dawo Ingila kafin a yi mana nunin amfanin gona za su gana sai aka kashe Sardauna.
“Bayan an kashe Sardauna sai ya kusanci Sarkin Wasagu marigayi Alhaji Musa, to zamansa kusa da Sarki ne sai siyasar Alhaji Shehu Shagari ta bullo sai ya tsunduma cikin siyasa daga nan har aka ba shi shugaban Jam’iyyar NPN na karamar Hukumar Zuru a lokacin ana tsohuwar Jihar Sakkwato.
Bayan an ba shi shugaban Jam’iyyar NPN, sai wata rana aka zo wasan noma na jiha, yana daya daga cikin wadanda suka samu nasara a wannan rana kuma aka ba shi Sarkin Noman Jihar Sakkwato.”
Ya ce: “Ana nan kuma wata rana sai aka shirya mana nunin amfanin gona a Kaduna, sai aka gayyace shi, daga nan da aka ga irin nasarorin da ya samu da gudunmawar da ya ba da wajen bunkasa aikin gona, a nan aka nada shi Sarkin Noman Najeriya, inda har Allah Ya yi masa cikawa yake rike da wannan sarauta.
Bayan an ba shi Sarkin Noman Najeriya daga nan sai ya bar wasan Nakiya da Garma ya kama aikin gona gadan-gadan ba kakkautawa.”
Alhaji Gareci Sallaman Wasagu ya ci gaba da cewa ya san Ali Namani da wata waibuwa, inda ya ce idan ana noma gonar Ali Namani ko mutum nawa ne ba a tsayawa a ci abinci sai dai a kawo fura tsakiyar gona a aje a samu wasu mutane su rike ludayi suna juya ta za ka ga tana ragewa kadan-kadan, to ta nan kowa zai ji ya koshi . Kuma a lokacin da yake wasa da garma idan ana ba shi kidi, idan ya dauko kashin doki a nan take zai maida shi goro ya rarraba wa masu noma.
“Kafin ya fara noma gadan-gadan a duk kasar Arewa kamar Zariya da Kano da Gombe da jiharsa ta Katsina da Ilori da Tsafe ba inda ba a gayyatarsa wajen wasan noma, saboda Allah Ya yi masa baiwa a kan wasan noma.
Babban dansa, Shehu Aliyu Namani Kotoko, ya shaida wa wakilinmu cewa ya ce batun aikin noma yanzu a gidansu sai dai su kara fadin gona bisa ga ta babansu, amma rasuwarsa ba za ta sa su janye daha noma ba. Ya ce kafin mahaifinsu ya rasu mazansu da matansu kowa yana da gona kuma yana nomawa har da matan da suka yi aure. Ya ce fadin gonar babansu kilomita 4 ne haka tsawon duka gonakin biyu haka suke, amma ban da gonar zogale da gonar rogo da gonar rake da kuma inda yake kiwon shanu. Alhaji Shehu Aliyu Namani ya ci gaba da cewa mahaifinsa yana noma buhu dubu na masara da buhu dubu na dawa, shi ko wake tasa maganarsa, kuma duk shekara yana ba da zakka fiye da buhu 800 tsakanim masara da dawa da wake. Amma babanmu ba ya yin noma gero saboda kasar ba ta yin gero.
Game da cewa akwai gari a cikin gonar marigayi Ali Namani Kotoko, sai ya ce “yanzu haka da za mu je da kai gonar da ka gani da idonka kuma ba don komai ba, suka zauna sai saboda noma, kuma a da gonar ta mahaifinmu duk abin da kake so ka saya akwai shi, har da mata masu zaman kansu, kuma a kullum safiya  mutun sama da 100 suke aiki a gonar.
An ce marigayi Alin Kotoko, saboda karfinsa, idan yana wasa da garma yana jefa ta sama yana cabewa sai abin ya ba mutum mamaki, kuma sai mai karfi ke irin wannan wasa.
Game da ko akwai wanda ya gaje shi wajen yin wasa da garma, Shehu Alin Kotoko ya ce, “Eh akwai wani karaminmu ne don ko yanzu  ya dauki kashin jaki yana iya maida shi goro ya ba ka shi ka ci, ba tare da wata matsala ba.”
Ya bukaci sauran ’yan uwansa su hada kai su ba marada kunya, mu yi kamar mahaifinmu bai rasu ba, domin sana’ar noma sun iya ta cikinta suka tashi, “mu kuma taimaki jama’a kamar yadda muka ga mahaifinmu yana taimakon jama’a, kada mu yi wasa sarautar noma ta bar gidanmu da kuma Jihar Kebbi.