✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rikicin Boko Haram ya kassara Kasuwar Kifi ta Baga

Kasuwar Kifi ta Tashar Baga da ke birnin Maiduguri a Jihar Borno wata cibiya ce ta hada-hadar kifi da ta fi kowace girma a Afirka…

Kasuwar Kifi ta Tashar Baga da ke birnin Maiduguri a Jihar Borno wata cibiya ce ta hada-hadar kifi da ta fi kowace girma a Afirka ta Yamma. Sai dai kasuwancin kifin da aka san kasuwar da ita ya hadu da cikas tun barkewar rikicin Boko Haram sama da shekara 10 da suka gabata inda kasuwar ta kassare. Hakan ya jefa dubban masu harkar kifi da kasuwancinsa a cikin halin kaka-ni-ka-yi.

’Yan Boko Haram sun fara tarwatsa harkar kamu da kasuwancin kifi ne sakamakon tarwatsa kauyukan da suke yankin Tafkin Chadi, irin su Dabar Masara da Cikon Gudu da sauransu da dama wadanda mazaunansu ba su da wata sana’a illa kamun kifi da gasa shi da sayar da shi.

A ziyarar da wakilin Aminiya ya kai Kasuwar Kifi ta Tashar Baga da ke birnin Maiduguri, ya ga yadda kasuwar ta kasance wayam babu harkar kirki. Ya iske kifi kalilan ne a kan teburan masu kasawa suna sayarwa, sabanin baya da za a ga motoci shake da kwalayen kifi ko’ina, ana ta harkar saye da sayarwa don kai shi sassan kasar nan da wasu kasashe makwabta.

Malam Dauda Lawan wani dillalin kifi a kasuwar ya shaida wa Aminiya cewa a halin yanzu, za a iya cewa kusan babu komai a harkar kifi domin a da sukan samu akalla motoci 100 zuwa 150 na kifi a duk mako, amma a yanzu da kyar ake samun mota biyu a kasuwar da ke ci sau uku a mako, wato ranakun Laraba da Alhamis da kuma Juma’a.

Ya ce masu kawo musu kifi daga bakin Chadi suna fuskantar kalubale sosai daga jami’an tsaro da kuma fargabar fadawa hannun ’yan Boko Haram. Ya ce wannan ne dalilin da ya sa yanzu babu kifin, domin babu wanda zai saka makudan kudinsa a inda zai yi asara kuma ya sa rayuwarsa a hadari.

Dauda Lawan ya yi kira ga Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya taimaka a bude hanyar Baga, domin a rika samun kifi daga bakin Tafkin Chadi.

Shi kuwa Ashiru Dogon Malam wanda ke safarar kifi da namun daji daga bakin Chadi zuwa Najeriya da Jamhuriyyar Nijar ya bayyana yadda masu harka irin tasa suke tsintar kawunansu a cikin matsala a hannun jami’an tsaro da suke kama kayansu. Ya ce suna yin asara mai yawa don haka suna fata shugabannin Kungiyar Masu Kifi, sun ci gaba da sanya baki ana yi musu sassauci. “A gaskiya muna fuskantar barazana mai yawa a wannan sana’a tamu. Wani lokacin za ka sayi kaya misali daga Geidam ko wani wuri, amma idan ka zo shigowa Maiduguri kun yi ta fama da jami’an tsaro, wata rana ma idan ba Allah Ya taimaki mutum ba, ya rasa kayan gaba daya. Don haka ina kira ga jami’an tsaro su sassauta kan hana shigowa da kifi, saboda akwai daruruwan matasa da suke dogara da wannan harka ta kifi wajen samun abinci,” inji shi.

Ali Usman wanda aka taba kone musu kifi bayan sun kawo daga yankin Tafkin Chadi, ya ce, suna kama kifi ne a yankin ruwa na Jamhuriyyar Nijar, sannan su kawo nan Najeriya. Ya ce kafin bullar Boko Haram suna zaune ne a mahaifarsa kauyen Dabar Masara, kuma tunda ya tashi ba ya da wata sana’a in ban da kamun kifin. “Boko Haram ne suka zo suka kore mu suka kone garinmu, dole muka zama ’yan gudun hijira a kasar Nijar, inda muka ci gaba da sana’ar kamun kifi muna kawowa Tashar Baga, amma kama kayanmu da jami’an tsaro ke yi suna konawa yana karya mu. Ko a baya-bayan nan sun kona mana kifi mota biyu, hakan ya sa dan abin da muke juyawa ya kare, yanzu haka na koma sayar da buhunan leda ne,” inji shi.

Ya roki gwamnati ta sassauta kan hana kawo kifi Kasuwar Baga, domin kasuwar tana samar wa sama da mutum miliyan daya abinci daga sassan kasar nan, baya ga samar da kudin shiga ga gwamnati.

Sakataren Kungiyar Masu Sayar da Kifi a Tashar Baga, Alhaji Mu’azu Isa ya shaida wa Aminiya cewa duk da sojoji sun hana kawo kifi bisa zargin wai ana kawo kifin ’yan Boko Haram ne, ana sayarwa suna samun kudi, ya ce, a gaskiya su a matsayinsu na kungiya shawarar da muka ba su ita ne, kada a hana kawo kifi gaba daya, ko a hana mutane zuwa bakin Chadi don su kamo kifi, a hada kai da kungiyarsu domin duk masu kawo kifi sun sansu, kuma har masu kamowar. Ya ce, a kyale duk wanda ya ga zai iya, in ya so a nemi su taimaka wa jami’an tsaro wajen karkade ’yan ta’addan a bakin Tafkin Chadi.

Da wakilinmu ya tambaye shi kan zargin cewa jami’an tsaro musamman sojoji sun karbe harkar kasuwancin kifin daga bakin Tafkin Chadi zuwa Kasuwar ta Baga, sai Alhaji Mu’azu Isa ya ce, “A gaskiya yanzu sun daina kawo kifi kai-tsaye, a da suna kawo kifi da kansu, kuma jami’an tsaron su taimaka mana wajen bude hanya a rika shigowa da kifi. Domin a da lokacin akwai kifi, mutane daga ko’ina a fadin kasar nan da kasashen waje suna zuwa cin kasuwar kifi a nan Tashar Baga.”

Shi ma Malam Fannami cewa ya yi sojoji ba sa kawo kifi a yanzu, amma a da sun rika kawowa. “Mu a matsayinmu na masu harkar sayar da kifi a nan Tashar Baga babu abin da za mu ce, sai mu kara gode wa Allah, tunda ga shi har yanzu muna dan taba harkar dillancin kifi, duk da ba dadi. Kullum muna kira ga gwamnati ta taimaka mana a bude hanyoyin Monguno da garin Baga domin a rika samun kifi. A da idan ka zo nan turmutsitsin mutane kadai ya ishe ka, saboda yadda harkar take tafiya, daga k’ ina jama’a na zuwa domin sayen kifi,” inji shi.

Sai ya yi kira ga hukumomin tsaro su kara kaimi, don ganin jami’an tsaron da ke Tafkin Chadi sun karkade ’yan Boko Haram da suke hana jama’a sana’arsu ta kamun kifi, wanda hakan ne zai sa kasuwar kifin ta farfado ta koma yadda take a baya.

Wani mai kawo kifi daga yankin Tafkin Chadi mai suna Ali Garba ya bayyana wa Aminiya cewa a baya yakan kawo kifi daga Chadi, kuma a wani lokaci yakan hado da sojoji, domin suna taimaka musu wajen kawo kifin cikin sauki. “Amma a yanzu gaskiya na daina kawo kifin, tunda aka hana bin hanyar Gamboru, wadda dama ita ce hanyar da ake samu a shigo da kifi daga kauyukan da ke bakin Tafkin Chadi da suke karkashin Jihar Borno. Amma maimakon ka tashi daga Dabar Masara, ka taho kai-tsaye zuwa Doron Baga, lamarin ya canja sai ka shigo ta cikin Chadi kafin ka iso Gamboru, hakan ya sa duk mun hakura da kasuwancin, don ita ma hanyar Gamboru babu ita a yanzu,” inji shi.

Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar Tsaro ta Lafiya Dole, Kanar Ado Isa ya shaida mata cewa sun sha yin magana a kan wannan lamari, don haka babu abin da zai sake cewa a kai.