✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rikicin cikin gida ka iya sa APC ta rasa Gwamna da sanatoci a Zamfara

Bayan da Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’aziz Yari ya shelanta cewa Kwamishinan Kudi na Jihar Alhaji Mukhtar Shehu Idris ne yake so ya gaje shi…

Bayan da Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’aziz Yari ya shelanta cewa Kwamishinan Kudi na Jihar Alhaji Mukhtar Shehu Idris ne yake so ya gaje shi a matsayin Gwamna sai rikicin siyasa ya kunno kai a jihar.

Akwai mutum takwas da suke neman tsaya wa Jam’iyyar APC takarar Gwamnan Jihar Zamfara baya ga Alhaji Mukhtar Shehu Idris.

’Yan takarar wadanda suka dunkule wuri daya suka kira kansu da Rukunin Mutum, sun turje wa zabin Gwamnan inda suka ja daga tare da nuna rashin amincewarsu da matakin da Gwamna Abdul’aziz Yari ya dauka suna nuni da cewa ba a shirya yin adalci a tsakaninsu ba.

’Yan takarar su ne Sanata Kabiru Marafa da Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Wakkala Muhammad da Alhaji Sagir Hamidu da Alhaji Dauda Lawal Dare da Alhaji Abu Magaji.

Sauran sun hada da tsohon Gwamnan Jihar, Alhaji Mahmud Aliyu Shinkafi da dan Majalisar Wakilai daga mazabar Birnin Magaji da Kauran Namoda, Alhaji Sani Jaji da kuma Ministan Tsaro Birgediya Janar Mansur Dan Ali.

Duk da cewa Gwamna Abdul’aziz Yari ya nuna ga wanda yake so ya gaje shi, ya kuma ce kowa yana iya sayen fom ya tsaya takara don ba a hana kowa takara ba, amma dai su suna nuna goyon bayan su ga Alhaji Mukhtar Shehu Idris ne ya zama Gwamna, kuma ya ce wakilan jam’iyya ne za su yi zaben na fid da gwani ba ’ya’yan jam’iyya ba.

Su kuma ’yan takarar 8 suka ja daga cewa sai dai a yi zaben ’Yar Tinke, inda za a ba kowane dan jam’iyyar damar zaben wanda zai tsaya wa APC takarar Gwamna a jihar, Wannan ya sanya aka rika sanya ranakun zaben fid da gwanin ana dagewa sakamakon rashin samun daidaito a tsakanin bangaren gwamnati da ’yan takarar 8.

Daga bisani an sanya ranar Larabar 3 ga Oktoba domin yin zaben fid da gwanin, amma bayan an fara zaben da ’yan awanni sai wasu matsaloli suka kunno kai wadanda suka hada rashin isassun katin jefa kuri’a da kuma rigingimu a sassa da dama na jihar.

Rigingimun da suka yi sanadiyyar rasa rayuka da lalata dukiya baya ga wadanda suka samu raunuka.

Saboda wadannan matsaloli ne sai kwamitin da uwar jam’iyyar ta tura jihar domin gudanar da zaben fid da gwanin wanda Dokta Abubakar A Fari yake jagoranta ya ba da sanarwar soke zaben. Matakin da Gwamna Yari ya yi watsi da shi, inda ya ce zaben zai ci gaba kuma sai an kammala shi.

Kwana biyar bayan soke zaben Jam’iyyar APC reshen jihar ta ba da sanarwar cewa Alhaji Mukhtar Shehu Idris ne ya lashe zaben fid da gwanin na jihar, kuma ta bayyana Gwamna Yari ne ya lashe zaben fid da gwani na Sanatan Zamfara ta Yamma.

Shugaban Jam’iyyarAPC ta Jihar Zamfara, Alhaji Lawali M. Liman ya bayyana dukan ’yan takarar da gwamnati ke mara wa baya don takarar sanatoci da ’yan Majalisar Taryya da ta jihar a matsayin wadanda suka lashe zaben fid da gwanin jamiyyar.

To amma sai kwamitin shirya zaben da aka tura jihar ya yi watsi da sakamakon zaben ya ce ba a yi zabe a jihar ba kuma zai rubuta rahoto su ba hedkwatar jamiyyar ta kasa kan haka.

Daya daga cikin masu son tsayawa takarar Gwamnan Jihar, Sanata Kabiru Marafa ya nuna amincewa da soke zaben na ranar 3 ga Oktoba.

Kuma bayan nan ne an sake turo wani sabon kwamitin shirya zaben a jihar a karkashin Manjo Janar Abubakar Mustapha Gana (mai ritaya) don sake gudanar da zaben fid da gwanin. Kuma kwamitin ya sa da ranar Lahadin da ta gabata domin gudanar da zaben, sai dai kuma hakan bai yiwu ba, saboda rigingimun da aka samu kan rajistar masu jefa kuri’a.

Da farko an kawo rajista mai dauke da jerin sunayen mutum dubu dari biyar da ’yan kai. Sai kuma aka kawo wata mai dauke da sunayen mutum dubu dari biyu da arba’in da bakawai. Hakan ya saya ’yan takarar suka yi ta takaddama har aka kai ga ba hammata iska a kan rajistar za a yi amfani da ita a wurin zaben.

An yi ta muhawara har zuwa asubahin ranar Lahadin da za a yi zaben, aka zarce har zuwa yammacin Lahadin amma zaben bai yiwu ba.

A gefe guda kuma Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ba da wa’adin zuwa karfe 12 na dare a ranar Litinin a kammala zabubbukan fid da gwanin na jam’iyyun.

Kwatsam a shekaranjiya Laraba, sai Hukumar Zabe ta Kasa ta bayyana cewa babu ’yan takarar kowane mukami a Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, sakamakon yadda aka kasa samun daidaito a gudanar da zaben fid da gwani a jihar zuwa ranar karshe ta 7 ga Oktoban bana.

Hukumar INEC ta bayyana haka ne a wata wasika da ta aike ga Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, Kwamared Adams Ohiomhole. Wasikar mai taken: “Gaza gudanar da zaben fid da gwani a Jihar Zamafara a kan lokaci, tana dauke da sanya hannun Mukaddashin Sakatare Hukumar Okechukwu Ndeche ta kafa hujja da jadawalin harkokin zaben badi da hukumar ta fitar a ranar 9 ga Janairun bana.

Hukumar ta ce, “Bisa tanadin Sashi na 87 da 31 na Dokar Zabe ta 2010 (wadda aka gyara), hukumar ba ta sa ran jam’iyyarku za ta mika sunan kowane dan takara daga Jihar Zamfara.”

Sai dai a martanin da Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa ya mayar, Oshiomhole ya ce Hukumar INEC ta yi azarbabi da ta ce jam’iyyarsa ba ta tsayar da ’yan takara ba don zaben na badi a Jihar Zamfara.

Oshiomhole a wata wasika da ya aike wa Shugaban Hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya ce kamata ya yi hukumar ta tuntubi shugabannin Jam’iyyar APC gaskiyar halin da ake ciki a Jihar Zamfara kafin ta yanke wannan shawara da ta saba wa doka.

Oshiomhole ya ce jadawalin harkokin zabe na 2019 da Hukumar INEC ta saki a ranar 9 ga Janairun bana ya nuna cewa: “Dukan jam’iyyun siyasa ana sa ran su mika jerin ’yan takararsu a ko kafin ranar 18 ga Oktoban bana bayan warware dukan takaddamar cikin gida da koke-koken da suka biyo bayan zaben fid da gwani.”

“A matsayinmu na jam’iyya muna kan warware wadannan matsaloli na cikin gida ne kafin mu mika sunayen ’yan takararmu gare ku. Mun kadu da ba ku jira mu ba mu mika muku sunayen ’yan takararmu ba a Jihar Zamfara (ganin cewa wa’adin da aka diba bai cika ba) kafin ku bayyana ra’ayinku a wasikar da kuka turo mana,” inji shi.

Oshiomhole ya ce Jam’iyyar PDP ma ba ta gudanar da zaben fid da gwani ba a Jihar Kano, “Amma ba a rubuta mata irin wannan wasika ba kana bin da ya faru a Jihar Kano.”

Yadda takaddamar take

Binciken Aminiya ya gano cewa, an shaida wa Oshiomhole cewa an cimma matsaya a tsakanin dukan ’yan takarar da Hukumar INEC da’yan takarar takwas a wata zama da aka yi a otel din City King da ke Gusau.

Wata majiya a Hukumar INEC ta shaida wa wakilinmu cewa, Gwamna Yari ya mika adadinkuri’ar  da ya ce ’ya’yan APC sun kada a lokacin zaben ’Yar Tinke, “Amma sai Kwamishinan INEC a Jihar Zamfara ya ki sanya hannu a kan takardun bisa cewa ba a kammala zaben ’Yar Tinken ba kafin hedkwatar APC ta Kasa ta dakatar tare da rusa shugabannin jam’iyyar na jihar.”

Majiyar ta ce hatta da’awar da Oshiomhole ya yi cewa an cimma matsaya babu madogara, domin ba za ka warware takaddama ba, a lokacin da abokan takaddama ba su nan, babu ko daya daga cikin ’yan takara 8 da ya amince da matsayar.”

An ce takardun da Gwamna Yari ya gabatar sun kunshi sunayen akasarin mutanen bangarensa ne.

Lauyoyi dai sun ce idan INEC ta ki janye wannan shawara da ta yanke kan matsayina na Zamfara, Jam’iyyar APC tana iya zuwa kotu ta bukaci a kara mata lokaci ta yi zaben fid da gwanin. Sai dai wani lauyan ya ce hujjojin da Oshomhole ya gabatar sun isa su sa INEC ta dogara da su wajen warware matsalar.

Wasu majiyoyi sun ce Gwamna Yari yana shirin kalubalantar matakin da uwar jamiyyar ta dauka kan zaben fid da gwani na Zamfara a gaban kotu.