✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rikicin fitar da ’yan takara ke neman awon gaba da Oshiomhole

Bisa ga dukan alamu  rikicin fitar da ’yan takara da ya ki ci ya ki cinyewa yana neman yin awon gaba da  Shugaban Jam’iyyar APC…

Bisa ga dukan alamu  rikicin fitar da ’yan takara da ya ki ci ya ki cinyewa yana neman yin awon gaba da  Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, inda hakan ya jawo sanya zare a  tsakaninsa da wadansu daga cikin gwamnonin jam’iyyar kuma dangantaka a tsakaninsu ke ci gaba da tabarbarewa a ’yan kwanakin nan.

A ranar Litinin da ta gabata  wata kungiya mai suna  Federation of Buhari Support Group (FBSG), a karkashin shugabancin Alhaji Ibrahim Sikiru sun yi zanga-zanga a hedkwatar Jam’iyyar APC da ke Abuja inda suka zargi gwamnonin da suka hada da Shugaban Majalisar Gwamnoni ta Kasa Gwamna Abdul’aziz Yari na Jihar Zamfara da Rotimi Akeredolu na Jihar  Ondo da Kayode Fayemi na Ekiti da Nasir El-Rufa’i  na Jihar Kaduna da Ibikunle Amosun na Ogun da Jubrilla Bindow na Adamawa da Rochas Okorocha na Imo da Mohammed Abubakar na Jihar Bauchi da sauransu cewa suna bita-da-kulli ga Kwamared Oshiomhole.

Alhaji Ibrahim Sikiru ya kara da cewa halaye da dabi’un gwamnonin na iya jawo koma-baya ga Jam’iyyar APC ko ma su hana Shugaba Muhammadu Buhari samun nasara a zabe mai zuwa.

Kwamared Oshiomhole ya dare kan kujerar shugabancin jam’iyyar ce a watan Yuni bana, bayan ya samu goyon bayan tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma jagoran Jam’iyyar APC, Sanata Bola Ahmed Tinubu Jagaban Borgu.

Idan ba a manta ba, mafi yawa daga cikin gwamnonin Jam’iyyar APC ba su so Kwamared Oshiomhole ya karbi shugabancin jam’iyyar daga hannun Cif John Odigie-Oyegun ba, ganin cewa tsohon shugaban ya bar su suna cin karensu babu babbaka a jihohinsu da kuma wajen daukar matakai kan alkiblar jam’iyyar a kasa baki daya.

Gwamnoni da dama sun ji a jikinsu a watannin da suka gabata saboda sa-in-sar da suka yi da wadansu daga jiga-jigan jam’iyyar a jihohinsu a lokacin zabubbukan wakilan jam’iyya da aka yi a watan Mayun bana da kuma zabubbukan fid-da-gwani na wadanda za su tsaya takarar gwamnonin da ’yan majalisa a tarayya da jihohi.

Har yanzu dai ana kai ruwa-rana a wasu jihohin saboda an gaza warware matsalolin da suka taso.

Rikicin Kwamared Oshiomhole da gwamnonin ya kara tabarbarewa ne a lokacin da ya nace cewa tilas a yi amfani da tsarin zaben ’yar Tinke wajen zabubukan fid-da-gwani; tsarin da ya tanadi cewa duk wani dan jam’iyya da ke da kati yana da damar ya shiga layi wajen zaben wanda zai tsaya wa Jam’iyyar APC takara.

Su kuma gwamnoni ganin cewa tuni sun samu damar mallakar wakilan jam’iyya a jihohinsu, sai suka ki amincewa da wannan tsari da Kwamared Oshiomhole ya ce yana so a yi amfani da shi.

A bayan zaben ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC Owelle Roachas Okorocha ya bayyana cewa lallai Shugaba Buhari ya sa baki kuma akwai alamun za a daidaita.

Sai dai masu fashin baki suna ganin Okorocha ya yi wannan bayani ne domin ya cimma burinsa na dora surukinsa Uche Nwosu a matsayin dan takarar Gwamna a Jihar Imo, shi kuma ya tsaya takarar Sanata daga yankinsu, sai uwargidansa ta yi takarar Majalisar Wakilai.

Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’azizi Yari ya zargi Kwamared Oshiomhole da daukar kansa tamkar wani gunki da tilas kowa ya bauta masa, ya ce lallai sai sun yi duk abin da ya dace domin tumbuke shi daga kan kujerarsa ta shugabancin Jam’iyyar APC.

Gwamna Yari ya harzuka ne domin bai samu nasarar dora Kwamishinan Kudi na Jihar Zamfara, Alhaji Mukhtar Idris a matsayin magajinsa ba.

Gwamna Yari ya hassala ne saboda Kwamared Oshiomhole ya nace cewa dole ne a gudanar da zaben fid-da-gwani ta hanyar zabe kai-tsaye a Jihar Zamfara; matakin da ya bai wa wadansu ’yan adawar cikin gida na Jam’iyyar APC a jihar irin su Sanata Kabiru Marafa da Mataimakin Gwamna Ibrahim Wakala da Ministan Tsaro Masur Dan-Ali da sauransu hada kai domin hana dan takarar Yari samun nasara zama Gwamnan Jihar Zamfara.

Har yanzu ana kai ruwa-rana a tsakanin Jam’iyyar APC da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) kan batun tsayar da ’yan takarar jam’iyyar a Jihar Zamfara, domin Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce Jam’iyyar APC a Zamfara ba za ta tsayar da ’yan takara a zabubbukan da za a gudanar a badi ba.

Shi ma Gwamna Ibekunle Amosun na Jihar Ogun ya yi rantsuwa cewa sai ya ga bayan Oshiohmhole saboda wanda yake so ya gaje shi, dan Majalisar Wakilai Adekunle Akinlade ya sha kasa.

A ranar Lahadin makon jiya Gwamna Amosun da Minista a Ma’aikatar Ilimi Sanata Iyabo Anisulowo wacce daga Jihar Ogun take, sun yi tatttaki zuwa Fadar Shugaban Kasa ta Aso Rock inda suka gana da Shugaba Muhammadu Buhari kan wannan batu.

Sai dai bisa ga dukan alamu hakar Amosun ba ta cimma ruwa ba, domin ko a ranar Alhamis, Sakataren Labarai na Jam’iyyar APC ta Kasa, Malam Lanre Issa-Onilu ya zargi Gwamna Amosun da yin riga malam masallaci wajen gudanar da zaben fid-da-gwani ba tare da ya jira jam’iyyar ta gudanar da zaben ba; ya mai ce hakan ba daidai ba ne. Tuni dai jam’iyyar ta bayar da sunan Cif Dapo Abiodun a matsayin dan takararta na Gwamna a Jihar Ogun, matakin da Gwamna Amosun ya ce an kisa shi ne a Legas a tsakanin Bola Tinubu da tsohon Gwamnan Ogun Segun Osoba.

Gwamna Nasir El-Rufa’i kuwa da kyar ya sha a Jihar Kaduna a rikicinsa da Sanata Shehu Sani. Duk da cewa Gwamna El-Rufa’i ba ya fuskantar barazana a kan kujerarsa ta Gwamna, amma ya harzuka matuka lokacin da Kwamared Oshiomhole ya bai wa Sanata Shehu Sani damar sake takara ba tare da hamayya ba.

Gwamna El-Rufa’i yana goya wa Babban Mashawarcinsa kan harkokin siyasa ne, Malam Uba Sani don ya karbe kujerar Sanata daga hannun Shehu Sani, wanda ba sa ga maciji.

Duk da cewa ya cimma burinsa a karshe, kuma Shehu Sani ya bar Jam’iyyar APC ya koma Jam’iyyar PRP, bincike ya nuna cewa Gwamna El-Rufa’i bai hakura ba kuma suna nan suna kokarin sai sun kawar da Kwamared Oshiomhole daga shugabancin jam’iyyar APC.

Shi kuwa Gwamna Muhammadu Jibrilla Bindow na Jihar Adamawa yana matukar fishi da Kwamared Oshiomhole domin wahalar da ya sha a hannun irin su tsohon Shugaban Hukumar EFCC, Malam Nuhu Ribadu da kuma kanen Uwargidan Shugaban Kasa A’isha Buhari wato Mahmud Halilu Modi kafin ya tsira da kujerarsa a zaben fid-da-gwanin.

Ita ma A’isha Buhari har bore ta yi a shafinta na Twitter a yanar gizo, inda ta zargi Oshiomhole da rashin iya gudanar da mulki ta yadda APC ta fada rudani a jihohi da yawa na kasar nan.

A Jihar Oyo ma Ministan Sadarwa Adebayo Shittu ya hasala matuka saboda Kwamared Oshiomhole ya hana shi tsayawa takarar Gwamna.

Lamarin dai babu dadi a jihohi da dama kuma masana siyasa suna ganin kamar Kwamared Oshiomhole ne ya tara wa kansa gajiya domin kusan yana fada da kowa.

Mafi yawan gwamnonin APC suna ganin Oshiomhole ne ummul-haba’isin matsalolin da suke fuskanta don haka suka sha alwashin ganin bayansa.

Kafin ranar Talatar da ta gabata lokacin da aka yi wani bore a hedkwatar APC, Kwamared Oshiomhole ya fitar da wani bayani a ranar Lahadin da ta gabata ta bakin Kakakinsa Simon Ebegbulem.

Ebebulam ya mayar da martani ne ga Alhaji Mumakai Unagha wanda ya so ya yi takarar Shugaban Kasa a karkashin jam’iyyar amma Kwamared Oshiomhole da sauran jiga-jigan jam’iyyar suka taka masa birki.

Alhaji Unagha ya yi hasashen cewa zai yi matukar wuya Jam’iyyar APC ta ci zabubbukan 2019 a karkashin abin da ya kira mulkin kama-karya da Kwamared Oshiomhole yake yi.

Kafin wannan hasashe da ya yi, shugabannin Jam’iyyar APC na jihohi 36 har da Abuja sun yi wani taro a Abuja inda suka nemi su yi tir da irin tsarin mulkin Kwamared Oshiomhole.

Masana al’amuran siyasa suna ganin cewa shugabannin jihohi wadanda yawancin su ba wai suna cin gashin kansu ba ne gwamnoninsu ne suka turo Abuja domin su yi bore.

Ganin cewa wutar da ake zargin Oshiomhole ya cinno wa kansa ta yi yawa ne, ya sa Kwamared Oshiomhole ya yi amai ya lashe a shekaranjiya Laraba, inda ya tilasta wa Kakakinsa ya bayyana wa manema labarai cewa ana kokarin sasantawa.

A baya dai Oshiomhole ya bayyana wa manema labarai a Abuja cewa wadansu tsirari ne daga cikin gwamnoni suke adawa da shi domin ya ki ba su damar yin abubuwan da suke so.

Shugaba Buhari ya gana da gwamnonin tare da wadansu jiga-jigan Jam’iyyar APC, inda ya tabbatar musu da cewa zai yi duk abin da ya dace domin kawo zaman lafiya a jam’iyyar.

A yanzu dai ba a san yadda za ta kaya ba, domin ana ganin bayanin da Shugaba Buhari ya yi bai gamsar da wadansu ba.

Idan za a iya tunawa rikicin cikin-gida a APC ya jawo sanatoci da dama da ’yan majalisa ficewa daga jam’iyar, abin da ake ganin ka iya kawo mata tarnaki a zabubbuka masu zuwa.