✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rikicin zauna gari banza ya ci rayukan matasa

A makon jiya ne al’ummar Arewa mazauna yankin Apapa Bandir a daura da unguwar Ajegunle suka wayi gari da rashin matasa hudu tare da jikkatar…

A makon jiya ne al’ummar Arewa mazauna yankin Apapa Bandir a daura da unguwar Ajegunle suka wayi gari da rashin matasa hudu tare da jikkatar wasu tara sakamakon wani rikici.

Gungun wasu zauna gari banza a wata unguwa da ke makwabtaka da su ne suka haddasa rikicin, a cewarsu.

A kokarinta na gano abin da ya faru, Aminiya ta ziyarci unguwar ta kuma zanta da Sarkin Hausawan yankin wanda kuma dansa na cikin matasan da aka kashe.

Kazalika Aminiya ta zanta da wata uwa da ta rasa dan da take riko, baya ga dan cikinta da ya sami mummunar rauni a rikicin.

Yadda rikicin ya samo asali

Sarkin Hausawan Ajegunle Malam Muhammadu Rabiu Sidi ya shaida wa Aminiya cewa rikicin ya samo asali ne tsakanin ‘yan zauna gari banza a unguwar Aalayabiagba da ‘yan sanda masu sintiri a yankin.

“Duk sadda ‘yan sandan suka zo yin sintiri sai ‘yan iskan wadanda ‘yan kasa ne masu gadarar su ke da waje, su yi ta yi wa ‘yan sanda bore suna jifan su suna ce masu ‘Ole-ole’ wato barayi-barayi.

“To a ranar da abin zai faru haka suka yi ta yi wa ‘yan sandan suna jifan su da kwalabe.

“A ranar Talatar makon jiya, sai ‘yan sandan suka yi kansu, sai yaranmu suka shiga tsakani suka bai wa ‘yan sandan hakuri.

“Da ‘yan sandan suka tafi sai wadannan ‘yan iska suka shigo unguwarmu suna cewa don me yaranmu za su sanya baki?

“To sai yaran unguwar ta mu suka kora su, suka hana su shigowa su tayar da hankali. Da suka ga haka sai suka ga haka sai suka je suka debo bindigogi masu harsashin ‘yayan boris, suka riko adduna suka shigo unguwarmu suna neman tayar da hargitsi.

“Ko da matasanmu suka ga haka sai suka tare su domin su kare unguwar inda suka kora su baya.

“Ganin haka sai suka fara harbe-harbe da sara, amma duk da haka matasan suka yi galaba suka mai da su baya”, inji Sarkin Hausawan Ajegunle.

Sarkin Hausawan Ajegule, Malam Muhammadu Rabiu Sidi

‘Sojoji ne suka kashe matasan’

Sarkin Hausawan ya ce akwai wasu sojoji da ke aikin ba da tsaro a daura da yankin. Ko da suka jiyo karar bindiga sai suka karaso wajen.

“A daidai lokacin da yaran namu ke dawowa bayan sun kora wadancan sai sojojin suka gan su cikin zuga. Sun dauka su ke yin harbin sai suka bude musu wuta.

“Lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu nan take a cikin yaranmu wadanda suke Hausawa ne da kuma wani matashin dan kabilar Ijaw daga Bayelsa da shi ma cikin matasanmu ya shiga ya kare unguwarsa.

“Akwai kuma karin wani matashin da ya rasu bayan an kwantar da shi asibiti, sannan akwai wadanda suka jikkata da dama, wasunsu harbin ‘yan iskan ne ya same su, na ‘yayan boris, wasu kuma sara ne da adduna”, inji shi.

Ba rikicin kabilanci ba ne

Malam Muhammadu Rabiu Sidi ya kara da cewa ba fada ne na kabilanci ba, kamar yadda wasu ke yayatawa.

Ya ce sunayen matasan da aka rasa su ne Habila, da Mansur, da kuma Rabiu sai kuma dan kabilar Ijow mai suna Peter Goddey.

Sojoji sun bayyana alhininsu

“An kira mu mun je Babban Ofishin Rundunar ‘Yan Sandan Legas inda suka bukaci mu yi masu bayanin abun da ya faru.
“Su kuma sojoji sun nuna tausayi da alhininsu domin ba a san ransu wannan abu ya faru ba, domin sun je wajen ne su kwantar da tarzoma.
“Yanzu haka mun yi jana’izar wadannan yara”, kamar yadda ya shaida wa Aminiya.

Mun bar wa Allah komai’

Sarkin ya ce  maganar bi wa yaran hakkinsu, idan sun yi hakan ba dawowa za su yi ba, “…don haka ba wanda ya fi cancanta mu bar wa lamarin sai Allah.

“Duk wadanda suke maganganun sai a bi wa yaran hakkinsu babu wanda ya fi ni dangantaka da yaran a cikinsu,  domin ni ma na rasa yaro guda a lamarin.

“Mu fatanmu a dauki matakin kare aukuwar lamarin a nan gaba.

“Wadannan ‘yan zauna gari banza da ke unguwar Aalayabiagba, a yi mana maganin matsalolin da suke addabar jama’a da su.

“Ji suke tamkar su ma wata hukuma ce ko gwamnati mai zaman kanta da babu wanda ya isa ya tsawata musu”, inji shi.

Uwargida Tina Resemse wadda aka kashe dan da take riko aka kuma jikkata dan cikinta a rikicin.

‘Mun rungumi kaddara’

Alhaji Labaran Sidi shi ne Galadiman Ajeromi Ifelodun ya shaida wa Aminiya cewa sun dauki wannan abu da ya faru a unguwar a matsayin kaddara daga Allah.

Sai dai babbar matsalar ita ce na yaran Yarbawa zauna gari banza na yankin Aalayabiagba, wadanda duk sadda wani dan abu ya faru suke dauko bindigoggi suna harbe-harbe, sace-sace da ji wa mutane rauni.

“Kuma wannan abu na faruwa ba sau daya ba, ba sau biyu ba. Babu wani da ya isa ya tsawatar masu. Don haka yana da kyau gwamnati ta shiga tsakani, domin tabbatar da zaman lafiya a yankinmu”, inji shi.

‘Dana ya jikkata, na kuma rasa dan riko’

Aminiya ta zanta  da Uwargida Tina Resemse wadda ta aka kashe dan da take riko aka kuma jikkata dan cikinta a rikicin.

Tina ‘yar asalin jihar Bayelsa mai zama a unguwar Ajegule, ta ce a lokacin da lamarin ya faru ta aiki yaran ne.

“…har na kwanta na fara barci a daren Talatar sai sai yaran suka je za su sayo burodi da kwai su ci. A hanya ne harsashin ya same su.

“Dan karamin harsashin ya fara tabawa sunansa Confidence mai shekaru 13.

“Ko da babban Goddey mai shekaru 18 ya yunkura zai tallafi dan uwansa sai shi ma aka harbe shi, nan take kuma ya mutu.

“Yanzu haka karamin yana asibiti, Sarkin Hausawa ne ke biyan kudin maganinsa”, inji ta.

Uwargida Tina ta kara da cewa suna bukatar daukin gwamnati wajen kulawa da wadanda suka jikkata tare da tallafa wa iyalen wadanda aka rasa.

Sarkin Hausawan Ajegule Muhammadu Rabiu a yayin  jana’izar wasu matasan da aka kashe a yamutsin.

Karamar hukuma da masu fada a ji

Malam Musa Yahaya Nayis shi ne Hadimin Shugaban Karamar Hukumar Ajeromi Ifelodun kan Al’amuran Cigaban Yankin.

Ya shaida wa Aminiya cewa abun da ya faru na da matukar tayar da hankali, ganin yadda suka rasa matasa hudu sannan da yawa suka jikkata.

Ya ce Mahukunta a karamar hukumar sun yi zama na musamman da shugabanin al’ummar yankin da Rundunar Sojin Ruwa kasancewar wajen kusa yake da barikin sojin ruwa.

Zuwa lokacin hada wannan rahoton, Musa Yahaya ya kara da cewa magabatan yankin na yin duk abin da ya dace domin magance matsalar.

Wakilin Aminiya ya yi yunkurin jin ta bangaren matasan unguwar Aalayabiagba, wadanda ake zargi da tayar da rikicin sai dai a lokacin da ya isa unguwar sun kaurace mata, inda wata majiya ta shaida masa cewa suna buya ne domin gudun ‘yan sanda su kama su.

Haka zalika wakilin Aminiya ya tuntubi Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas DSP Bala Elkana ta wayar salulu, amma bai amsa kiran ba, bai amsa sakon karta kwana da wakilinmu ya aike masa ba game da lamarin.