✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Sakkwato ta zama sansanin tawagogin rakuma

Sannu a hankali, Sakkwato ta zama sansanin tawagogin rakuma. A duk shekara, musamman lokacin kaka, Fulani makiyaya daga Jamhuriyar Nijar sukan yo hijira tawaga-tawaga, bisa…

Wata Bafulatana da kayanta a lokacin da suke koma wa NijarSannu a hankali, Sakkwato ta zama sansanin tawagogin rakuma. A duk shekara, musamman lokacin kaka, Fulani makiyaya daga Jamhuriyar Nijar sukan yo hijira tawaga-tawaga, bisa rakuma su shigo Najeriya kuma su yada zango a Sakkwato, kafin su wuce zuwa wasu jihohin. Ba su za su koma gida ba sai da damina, lokacin da ruwan sama ya fara sauka.
Irin wadannan Fulani makiyaya, sukan yo hijira ne, inda suke shirya kansu cikin tawagogi, kowace tawaga sukan nada mata shugaba a matsayin madugu; wanda suke kira da lakanin ‘Garso.’ Kowace tawaga, za ka same ta dauke da mutane masu alaka da juna, kodai ’yan uwan juna ne na jini, ko na makwabtaka da sauransu.
Haka kuma, kamar yadda ake kiran madugun kowace tawaga da lakanin, ita kuma tawagar ana yi mata lakabi da ‘Chakkol.’ A kowace Chakkol, za ka samu adadin iyalai bakwai zuwa goma, wadanda ke dauke da mata da maza, manya da yara. Kai da ganin yadda ayarin ke tafiya, ka san cewa hijira ce suke yi, ko kuma a kira ta da ci-rani. Za ka same su dauke da kayayyakin bukata, kamar korai, tukwane da sauran kayan bukata na gida.
Baya ga Chakkol, akwai kuma wata shigen tawagar da ake wa lakani da ‘Biggeeji,’ wacce ke dauke da takaitattun mutane da ba su tare da iyali ko yara. Mutanen da ke cikin irin wannan tawaga, ba su wuce uku zuwa biyar ba.
Makiyayan nan, za ka same su bisa rakuma, wasu a kan shanu, wasu kuwa a kan jakuna da sauransu. Ko yaya suke gudanar da wannan tafiya tasu kuma da ina da ina suke zuwa a cikin Najeriya? Wakiliyarmu ta gana da wasu daga cikin irin wadannan ’yan ci-rani a Sakkwato, inda suka bayyana dalla-dalla yadda suke tafiyar da al’amuransu.
Suka ce idan sun shigo Najeriya daga Nijar, sukan je Jihar Kwara da Neja kuma sukan taho ne daga garuruwan Madawa da Dosso da Tahoa da ke Jamhuriyar Nijar. Kamar yadda makiyayan suka ce sun fi zuwa jihohin Kwara da Neja ne musamman saboda a can ne suke sama wa dabbobinsu abinci mai kyau. A lokacin damina kuwa, sukan koma gida Nijar ne saboda abincin dabbobi ya fi kyau a irin wannan yanayi a can kasarsu.
“A duk lokacin da aka ce maka damina ta kama, muka koma gida Nijar, dabbobinmu kan ci abinci mai kyau ka ga sun yi bul-bul. Idan ka kwatanta su da dabbobin da aka kiwata a Najeriya a lokacin damina, za ka ga namu sun fi kyau da lafiya. Wannan shi ne ma babban dalilin da ya sanya muke komawa gida a irin lokacin damina.” Inji daya daga cikin makiyayan.
Dauda, ya kasance daya daga cikin madugan da ke jagorantar tawagogin Fulani makiyaya. Ya shaida wa Aminiya cewa, yana jin dadin zuwa ci-rani Najeriya. “A duk lokacin da na shigo Najeriya, nakan ji dadin zama sosai, musamman saboda dabbobina na samun wadataccen abinci kuma mai kyau.” Inji shi.
Kamar yadda ya ce, a bana ayarinsa Jihar Neja suka je ci-rani. Ya kara da cewa, tafiyar ta dauke su tsawon kwanaki goma sha biyar. “Daga Nijar zuwa Jihar Neja a Najeriya, mun yada zango har sau ashirin. A duk lokacin Sallah, mukan tsaya mu yi, idan kuma dare ya yi, mukan samu wuri mai kyau mu tsaya, mu kwanta, da safe kuma mu tashi mu ci gaba da tafiya.”
Wani al’amari mai ban sha’awa da ke faruwa tsakanin makiyayan nan ’yan ci rani da kuma manoma shi ne, yadda suke taimakon juna. Kamar yadda Aminiya ta kalato, manoma kan saukar da makiyayan a gonakinsu, su ci karmami da sauran sharar gona. Su kuma sukan amfana da kashin dabbobin a matsayin taki. Manoman kan kuma taimaka wa makiyayan da dafaffen wake, musamman ma ga ayarin da ba su tare da iyalinsu. Amma wadanda ke da iyali kuwa, manoman kan ba su gero, wanda matansu kan sarrafa domin amfanin tawagar gaba daya.
A sanadiyyar irin wannan tafiye-tafiye na ci-rani, akan samu sanayya tsakakin Fulanin Nijar da na Najeriya, inda har auratayya kan shiga tsakani. Sai dai irin wannan aure, akan yi shi ne bisa sharadi da yarjejeniya. Idan Bafulatanin Nijar ya ga yarinya yana so a Najeriya, dole sai da sharadin zai rika tafiye-tafiyen ci-rani, idan ba haka ba, ba za a ba shi auren ba. A takaice, sun fi son su ba matafiyi, fiye da mazaunin wuri guda.
Alhaji Alhassan, Bafulatanin Najeriya ne da ke zaune a Falaliya da ke karamar Hukumar Goronyo, Jihar Sakkwato. Ya ce alaka tsakaninsu da Fulanin Nijar tana da karfi sosai. Ya ce sukan kai wa juna ziyara a kai-a kai.
“Mukan yi zumunci da juna sosai, har ma muna amfanar juna da dukiyarmu. Akwai wata al’ada da muke yi, inda mukan ara wa juna sanuwa. Mutum kan ara wa wani da suke zumunci da juna sanuwa, idan ta haihu sai ya dauki diyar, ya mayar masa da sanuwarsa. Shi ma wata rana sai ya yi haka, kamar dai yadda ake yin adashi.”
Ya kuma kara da cewa: “Mukan yi auratayya da junanmu domin addininmu daya, mu Musulmi ne, ba ma nuna wa juna wariya. Muna zaune da juna cikin lumana da kwanciyar hankali.”
Ya kuma bayyana irin yadda suke fuskantar kalubale, a yayin da suke kiwata dabbobinsu a daji. “Wasu lokutan, idan muna kiwo a daji, mukan fuskanci matsalar muggan dabbobin daji, kamar zaki ko damisa da kan halaka mana dabbobi.” Inji.
Da yake bayyana yadda suke samun kariya daga hadarin namun daji, Alhaji Alhassan ya ce, aikin madugu ne ya tsara hikima ko dubarar yadda za su tsare ko kare dabbobinsu da ’yan tawagarsu daga hadarin namun daji.
Haka kuma, wata matasalar da suke fuskanta ita ce, wasu lokutan sukan samu sabani ko rashin jituwa tsakaninsu da manoma. Kodayake ya ce abin na faruwa ne daga wasu daga cikin su Fulanin. Kamar yadda ya ce, akwai Fulanin da ke tafiya ba tare da iyalinsu ba, irinsu ba su dauke da yara ko tawaga mai yawa. Irinsu ne ke yi wa manoma barna a gonaki, sai su gudu da sauri. Idan haka ta faru, sai a dora wa Fulani masu iyali laifin, a bar su da biyan diyyar barnar da ba su suka aikata ba.
Ya kara da cewa: “Mukan kuma fuskanci matsalar annobar cutar dabbobi. Wani lokacin mukan sauka garin da ke da matsalar wata cutar, wacce kan kama dabbobinmu. Idan haka ta faru, mukan yi kokarin tashi daga wurin, mu tseratar da dabbobinmu ba tare da sun kamu da cutar ba. Amma a yayin da suka kamu kuwa, mukan tuntubi kungiyar Miyetti Allah, domin su yi mana jagorar samo malamin dabbobi.”
“Wata matsalar kuma da muke fuskanta, shi ne na barayin shanu. Wani lokacin za ka gansu da motar A-kori-kura, su mamaye mu, su lode shanunmu su tsere. Amma yau da kullum mukan samu dubarar kare kanmu daga irin wadannan barayi. Saboda dadewa cikin harkar, yanzu muna tanadar wa kanmu makaman da muke kare kanmu da dukiyarmu daga barayin.”