✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Yadda Sarki da tsohon shugaban yanki da iyalansu suka rasa rayukansu

Wakilinmu ya tuntubi Daraktan kula da jama’a na karamar hukumar Illaila, Alhaji Adulhamid Shu’aibu, wanda ya yi magana a madadin karamar hukumar , inda ya…

Wakilinmu ya tuntubi Daraktan kula da jama’a na karamar hukumar Illaila, Alhaji Adulhamid Shu’aibu, wanda ya yi magana a madadin karamar hukumar , inda ya ce.‘Margayi tsohon kantomanmu mun yi aiki da shi tsawon wata 13, a dan wannan zaman da muka yi da shi mun fahimci mutum ne mai kyawawan hali da son jama’a da mutunta na gaba da shi, ga fadin gaskiya a lamurransa. Kwana 30 da sauke su ne ya tafi aikin hajji, sai ta Allah ta kasance a wurinsa. Lokacin da ya dauka yana jagorantarmu gaskiya ya kawo mana cigaba da sauyi mai alfanu, musamman a tsare-tsaren aikin hajji, wanda a duk shekara sai an samu matsala, ban da wannan shekarar, aikin gwamnati ya gyaru a zamaninsa da duk sauran abubuwan da ake bukatar kulawarsa.’ In ji shi.

Alhaji Abdulhamid ya kara da cewa, ‘Mataimakin magatakarda da ke rijistar Alhazan wannan karamar hukuma, ya ce mun rasa Alhazzai 81, wato mata 55 maza 26. A kauyen Araba an rasa mutum 10, Amarawa 7, Gidan Hamma 5, a nan garin Illela ne ake da sauran kason. Kusan mun fi kowa asarar rayuka a duk Nijeriya, saboda lokacin da abin ya faru suna cikin tsakiyar wurin.
Daga jihar Taraba kuma, marigayi Sarkin Zing Alhaji Ibrahim Abbas Sambo, daya daga cikin sarakunan gargajiya da ake girmamawa a jihar saboda dattakonsa da kuma son zaman lafiya tare da fadin gaskiya komai dacinta, yana daya daga cikin wadanda suka rasu tare da matansa biyu a lokacin turmutsitsin.
Marigayin wanda daya ne daga cikin sarakuna shida masu daraja ta daya (Farar sanda) a jihar, shi ne gwamnatin jihar Taraba ta nada a matsayin Amirul Hajj na bana.
dan shekara sittin da biyu,Sarkin Zing ya kasance kamar ya san cewa zai mutu a kasa mai tsaki, domin a lokacin da yake yi wa alhazan jihar wadanda zai masu jagoranci, ya shawarci jama’a su kasance masu yafe wa juna tare da kasancewa masu gaskiya da rikon amana domin ba wanda ya san ranar da zai koma ga mahalilcinsa. Ya shaida wa maninyatan cewa, kila wadansu daga cikinsu ba za su dawo gida ba.
Masarautar Zing ta hada mabiya addinai daban-daban, wadanda ke bin addinin Musulinci da Kirista da kuma masu bin addinin gargajiya, da aka fi sani da masu Dodo. Dukkansu hankalinsu ya tashi.
Sakataren Hukumar Alhazai ta jihar Taraba, Alhaji Umar Leme, ya bayyana wa Aminiya ta waya daga Saudiyya cewa sun gano gawar sarkin kuma har ma an yi jana’izarsa a Makkah a ranar Jumma’ar da ta gabata. Amma su matan Sarkin su biyu tare da Hakimin garin Garba –chede Alhaji kasimu Kaigama da wadansu alhazan jihar su 8 har zuwa lokacin ba a gansu ba. Wadansu alhazan jihar Taraba sun bayyana wa Wakilinmu cewa matan Sarkin su biyu sun rasu, domin tare suke da shi maigidansu a lokacin da wannan hadari ya auku. Kuma suna kyautata zaton cewa sauran mahajjatan da ba a gansu bas u ma sun mutu.
Ana ta zuwa fadar marigayin domin ta’aziyya, cikin wadanda suka fara isa fadar sun hada da Mataimakin gwamnan jihar Alhaji Haruna Manu da Shugaban Majalisar dokokin jihar Mista Abel Peter Diah wanda ya jagoranci sauran ‘yan majalisar jihar.
Shugaban Majalisar Sarakuna na jihar, wanda kuma shi ne Aku-Uka na Wukari, Mista Shekarau Agyu ya ce Majalisar Sarakuna ta jihar ta yi asarar babban jigo, wanda ya bayar da gudunmawa mai yawa a kan harkokin masarautu a jihar.