✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Sarkin Katsina ya gudanar da bikin cika shekara 10 a sarauta

A ranar Talatar da ta gabata ce Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya yi taron addu’o’in don murnar cikarsa shekara 10 bisa…

A ranar Talatar da ta gabata ce Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya yi taron addu’o’in don murnar cikarsa shekara 10 bisa karagar sarauta.

Taron addu’o’in wanda aka yi a fadar Mai martabar ya saba wa tunanin wadansu ko al’adar da aka saba a duk lokacin da wani Sarki ya cika wasu shekaru bisa mulki inda ake yin bukukuwa iri-iri don taya shi murna. Shi dai Sarkin  taron yin addu’o’i da godiya ga Allah Wanda Ya ba shi wannan sarauta ya yi. 

An gayyato malamai daga sassa daban-daban na masarautar tare da hakimansa domin gudanar da wannan addu’a wadda aka yi ga shi kansa Sarki da magabatansa da kuma addu’o’i neman zaman lafiya a kasa baki daya.

kauran Katsina Hakimin Rimi Alhaji Nuhu Abdulkadir wanda kuma shi ne jagoran masu zaben Sarki ya ce, “Tun lokacin da ka hau wannan kujerar sarauta, kullum abin da muke gani shi ne alheri tare da yabo daga jama’a. Har yanzu babu wanda ya yi kuka a kanka. Muna yi maka fatan ci gaba da samun wadannan nasarori.”

 An haifi Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumin Kabir Usman a ranar 9 ga Janairun 1952 a gidan sarautar marigayi Sarkin Katsina Sa Usman Nagogo dan Sarkin Katsina Muhammadu Dikko wanda ya zamo Sarki na farko daga sashin Sullubawa a 1906. Sarki Abdulmumin ya yi makarantar firamare ta Kayalwa da ke cikin garin Katsina daga 1959 zuwa 1964, daga nan ya wuce makarantar Kwalejin Gwamnati a yanzu daga 1965-1969. Ya yi Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a 1972 zuwa 1974. Kuma ya samu digiri a fannin sanin halayyar dan Adam (Sociology) a Jami’ar Usman dan Fodiyo daga 1978-1981, sannan ya yi wa kasa  hidima a hukumar Rima ta Sakkwato. Alhaji AbdulmuminuKabir Usman ya zama Sarkin Katsina a ranar 13 ga Maris din shekarar 2008 bayan rasuwar mahaifinsa Sarki Kabir Usman Nagogo. Shi ne Sarki na 50 tun daga sarautar Habe da Durbawa zuwa ga Fulani. Sannan shi ne Sarki na 12 a Sarakuna Fulani tun daga kan Dallazawa, kuma shi ne Sarki na 4 a masarautar Fulani ta Sullubawa wadda ta faro daga kan Sarki Dikko a 1906.

Bayan an gama addu’o’in, Sarki Abdulmumin ya jagoranci jama’a zuwa bude sabon masallaci da makarantar Islamiya wadanda ya gina mai suna, ‘Hubbaren DUKA’ (Dikko, Usman, Kabir, Abdulmumin) a filin da ke kusa da gidan Ganye, wato inda ake rufe Sarakunan Sullubawa tun daga Sarki Dikko tare da wadansu daga cikin matan sarakunan. Sarkin ya shiga wannan makabarta domin yi wa iyayensa Sarki Dikko da Sarki Kabir da kakansa Sarki Usman addu’o’in samun rahama. 

Daga nan ya kara duba itaciyar dabinon da ya shuka da hannunsa wadda ke nuni da cewa shi ma idan lokacinsa ya yi a nan za a rufe shi kamar yadda Sarki Dikko da Usman da kuma mahaifinsa Sarki Kabir suka yi.