Daily Trust Aminiya - Yadda shawarma ta yi sanadiyyar mutuwa a Legas
Subscribe

Shawarma

Yadda shawarma ta yi sanadiyyar mutuwa a Legas

Wani mutum da ba a san ko wane ne ba ya cika wandonsa da iska bayan ya dirka wa wani mai suna Kayode Oloruntoba harsashi a ciki a wani wurin sayar da abinci da ke Alagbado a Jihar Legas.

Sai dai duk yunkurin da wasu da ke zaune a wurin suka yi na ceto wanda aka harban bayan faruwar lamarin ya ci tura inda nan take ya ce ga garinku nan.

Rahotanni sun ce takaddamar ta samo asali ne lokacin da Kayode mai shekara 35 ya je wata mashaya a Alagbado domin sayen Shawarma tare da abokinsa mai suna Okikiola.

Mai sayar da shawarmar na cikin sallamar sa ne takaddama ta kaure tsakanin abokinsa Okikiola da wani da ya zo yin sayayya a wajen.

Sa-in-sar ta fara ne a kan wanda za a fara sallama kafin ta rikide ta zama tashin hankali, wanda bayan mutumin ya harzuka, kawai sai ya koma ya shiga motarsa ya bar wajen.

Bayan mintoci ya sake dawowa ya zaro bindiga ya dirka wa Kayode albarushi a ciki ya kuma cika wandonsa da iska.

Wani ganau mai suna Chinedu ya ce wanda ake zargin ya yi harbin ne a bisa kuskure.

“Hakika wanda ya so harba shi ne Okikiola (wanda suka yi takaddamar da shi).

“Sai dai a cikin rashin sa’a ya harbi wanda ba shi ya yi niyya ba. Nan da nan ya kuma ya tsere”, inji Chinedu.

texem
More Stories