Da Dumi Dumi

Yadda Sheikh Dahiru Bauchi ya jagoranci Sallar Idi

Shaikh Dahiru Usman Bauchi a Lokacin da yayi hawan Idin sallah karama a daura da gidan sa a jihar Bauchi

Dubban Musulmi ne a garin Bauchi suka halarci Sallar Idin karamar Sallah karkashin Jagorancin Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Tun adaren ranar Juma’a sharararren malamin ya bayyana cewa ya samu bayanai da suka tabbatar masa da cewa an ga wata a wurare da dama a Nijeriya.

Tun da misalin karfe bakwai na safiya wasu al’ummar Musulimi suka yi dafifi a gidan Shehin Malamin da ke Kofar Gombe don jiran lokacin Sallar da aka fara da karfe tara na safiya.

Sheikh Dahiru Bauchi yace,  labari yazo mana sahihi anga watan Shawwal  shi ya sa muka tashi da idi babu azumi tun da watan Ramadana yakare.

“Da ma hukuncin da aka ba mu shi ne wata yana tabbata in aka samu mutane adilai guda biyu sun ce sun ga wata kuma an tabbatar da adalancinsu, ko ko jama’a masu yawa”, inji malamin.

ADVERTISEMENT

“Jama’a masu yawa inda take farawa daga an samu mutum biyar baligai masu hankali, to shi ke nan an samu jama’a mustafidah – su kuma ba a binciken adalcinsu.

“A nan cikin garin Bauchi mutum takwas sun gani. A Liman Katagum mutum 10 sun gani – faya kam ma yaron gidanmu ne.

“Mun samu labari a Geidam, Yobe ke nan, mutane da yawa sun ga wata; mun samu labarin wasu sun kai labarin sun ga wata gidan Shehu Gibirima wajen halifansa…

“Jama’ar Zariya sun aiko mana sun ce sun ga wata, labari ya same mu an ga wata a Yawuri da Zariya.

“Tun da yake Jama’a da yawa sun gani a garuruwa daban-daban, ba maganan  mutum biyar ba ne, na jma’a ne da yawa,  kuma Allah ya wajabta mana Azumi ya ce yan kwanaki ne yan kadan, an ce a Zariya kauyuka uku ne suka kawo labarin an ga wata haka kuma anguwanni uku ne sukaga wata a Zariya.

Sheikh ya ce “kowane yini na Ramadan wanda Allah ya wajabta mana, akalla martabarsa wata biyu. In ka ci abinci da gangan a Ramadana dole ka yi azumin wata biyu a jere sannan ka biya yinin da ka bata.

Malamin ya kuma yi adduoin neman zama lafiya da kwanciyar hankali da kuma kawo karshen wannan annoba na cutar kurona data addabi Nijeriya.

Da yake gabatar da Huduba bayan Sallahn Idi Sayyadi Ibrahim Sheikh Dahiru ya hori alummar musulmi game da muhimmancin fitar da zakkan fiddakai sannan ya rokesu dasu rika bin koyarwan addinin Musulunci cikin tafarkin rayuwarsu

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya