Daily Trust Aminiya - Yadda shirin janye sojoji a yankunan da ake rikici ke jawo f
Subscribe

Sojojin Najeriya, yayin wani fareti

Yadda shirin janye sojoji a yankunan da ake rikici ke jawo fargaba

Shirin Gwamnatin Tarayya na fara janye sojoji a yankunan kasar nan da aka samu zaman lafiya a rubu’in farko na bana da maye gurbinsu da ’yan sanda ya fara daga hankalin jama’a tare da jawo fargaba a yankunan da dama.

Babban Hafsan Sojin Ruwa, Riya Admiral Ibok Ekwe-Ibas ne ya sanar da shirin janye sojojin lokacin da yake zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa a karshen makon jiya, bayan taronsu da Shugaban Kasa.

Ya ce za a yi haka ne domin a ba ’yan sanda dama su gudanar da aikinsu na tabbatar da tsaron cikin gida. Ya ce janye sojojin wanda za a yi a hankali zai taimaka wajen juya akalarsu zuwa fuskantar wasu kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

Da aka tambaye shi ko hakan ba zai iya jefa yankunan cikin koma- baya a harkokin tsaro ba? Ya ce, “Abin da nake nufi shi ne, za a janye sojojin ne bayan an bincika kuma an tabbatar da abin da ke kasa. Ba wai za a janye su ba ne a yankunan da suke fuskantar kalubale. Sannan kasancewar kasar nan na kokarin karo sababbin makamai ga sojoji. Muna sa ran zuwan rubu’i na biyu na bana, dukkan makaman sun iso.Da haka ne ’yan sanda za su samu damar yin aikinsu na tsaron cikin gida a yankunan da aka tabbatar da samun zaman lafiya. Ba zai yiwu ba a janye sojojin a inda ake bukatarsu,” inji shi.

texem
More Stories